Abin da Ya Fi Burge Atiku a yayin Kamfen Zaɓen 2027 Idan Aka Taɓa Tinubu
- Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya ce yana ɗaukar kiran ‘Tinubu Must Go’ da jama’a ke yi a gangaminsa a matsayin kira na neman sauyi
- Atiku ya gode wa al’ummar Potiskum da jihar Yobe bisa tarbar da suka yi masa da tawagarsa yayin rangadin yaƙin neman zaɓensa
- Dan siyasar ya yi alkawarin ɗaukar matakan gaggawa domin rage tsadar rayuwa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Potiskum, Yobe - Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar, ya bayyana yadda yake ji a duk lokacin da magoya bayansa ke yi wa Shugaba Bola Tinubu ihun ‘Tinubu Must Go’ a wajen gangamin siyasa.
Atiku ya bayyana hakan ne yayin da yake gode wa al’ummar Potiskum da sauran mutanen jihar Yobe bisa irin tarbar da suka yi masa da tawagarsa a ranar Litinin, 16 ga watan Nuwamban 2026.

Kara karanta wannan
Shugaban APC ya ware gwamnonin Arewa 7, ya ba su shawara kan goyon bayan Tinubu a 2027

Source: Twitter
A cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaransa na dabarun sadarwa, Phrank Shaibu, ya fitar, Atiku ya ce tarbar da aka yi masa tun daga Azare a jihar Bauchi har zuwa Potiskum ta nuna yadda mutane ke fatan samun sauƙin rayuwa, cewar Daily Trust.
Atiku ya yi magana kan ziyartar Yobe
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana cewa yawan mutanen da suka fito domin tarbarsa, murmushinsu da kiraye-kirayen da suke yi sun kasance abubuwan da ba zai manta da su ba.
Ya kuma gode wa gwamnan jihar Yobe bisa tabbatar da cewa jam'iyyar ADC ta gudanar da gangamin yaƙin neman zaɓenta cikin yanayi na adalci da bai wa kowa dama.
Atiku ya ce dimokuraɗiyya tana bunƙasa ne idan dukkan jam’iyyun siyasa suka samu damar ganawa da al’umma da bayyana manufofinsu ba tare da takura musu ba.
Amfani da AI: Atiku ya soki gwamnatin Tinubu
A wani ɓangare na sanarwar, Atiku ya yi zargin cewa fadar shugaban ƙasa na buƙatar amfani da fasahar AI wajen ƙirƙirar hotunan cunkoson jama'a a gangamin siyasa.
Ya ce abin da ya faru a Potiskum ya bambanta, domin mutanen da suka fito tarbarsa na zahiri ne, ba hotunan da aka ƙirƙira ko aka gyara ta amfani da fasaha ba.
A kalamansa, Atiku ya yi ba'a cewa da alama fasahar AI ta gwamnatin Tinubu ta manta cewa mutane suna buƙatar kujerun zama, kuma ba sa shawagi a sama yayin sauraron jawabin 'yan siyasa.

Source: Twitter
Abin da Atiku ya ce game da Tinubu Must Go
Atiku ya bayyana cewa kamfen ɗin ADC mai taken 'Affordable Life' ba wai taken siyasa kawai ba ne, domin yana da alaƙa da ƙoƙarin samar da sauƙin rayuwa ga 'yan Najeriya.
Ya ce duk lokacin da ya ji jama'a suna ihun 'Tinubu Must Go' a gangaminsa, yana ɗaukar kalaman a matsayin kira na neman sauyin shugabanci da kuma tunatarwa kan nauyin da zai hau kansa idan aka ba shi amanar mulki.
Atiku ya yi alkawarin cewa idan Shugaba Tinubu ya bar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2027, zai tabbatar da ingantaccen shugabanci da kuma rage tsadar rayuwa.
Ya kuma ce zai fara ɗaukar matakan gaggawa domin sauƙaƙa wa 'yan Najeriya rayuwa idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a zaɓen ranar 16 ga watan Janairun 2027, cewar Vanguard.
Ana ganin Atiku zai yi nasara kan Tinubu
Mun ba ku labarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, na kara kokarin neman goyon bayan al’ummar Arewa gabanin zaben shugaban kasa na 2027.
Tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung, ya yi ikirarin cewa wasu magoya bayan marigayi Muhammadu Buhari na karkata zuwa Atiku.
Rashin gamsuwar wasu ’yan Najeriya kan tsadar rayuwa, rashin tsaro da matsalolin tattalin arziki na daga cikin abubuwan da ka iya shafar zaben 2027.
Asali: Legit.ng

