Masu Bukata na Musamman Sun Kafa Sharadi ga Gwamna Abba kan Samun Tazarce a 2027
- Ƙungiyoyin masu bukatu na musamman a Kano sun nemi a tanadar musu kujeru uku a Majalisar Dokokin jihar
- Sun kuma nemi muƙaman kansila da mai ba da shawara kan harkokin nakasassu a kowace ƙaramar hukuma, wanda zai kai muƙamai 88
- Ƙungiyar ta yi alƙawarin tallafa wa neman wa’adi na biyu na Gwamna Abba Kabir Yusuf, tare da wayar da kan masu zaɓe da iyalansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Mutanen da ke da buƙatu na musamman (PWDs) a jihar Kano sun buƙaci a tanadar musu kujeru uku a Majalisar Dokokin jihar mai mambobi 40, tare da ba su muƙaman siyasa 88 a ƙananan hukumomi 44.
Sun bayyana waɗannan buƙatu ne a matsayin hanyar tabbatar da shigar da su cikin harkokin mulki, tare da bayyana goyon bayansu ga gwamnan jihar a zaɓe mai zuwa.

Kara karanta wannan
Peter Obi ya shirya share hawayen 'yan Arewa, ya gano hanyar magance matsalar yankin

Source: Facebook
An gabatar da buƙatun ne cikin daftarin yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da haɗin gwiwar ƙungiyoyin nakasassu da shugabanninsu suka miƙa yayin wani taro a Kano ranar Asabar, 14 ga watan Nuwamban 2026, cewar rahoton jaridar Daily Trust.
Buƙatar kujeru 3 a Majalisar Dokoki
A cikin yarjejeniyar, ƙungiyar ta nemi a tanadar wa masu buƙatu na musamman kujera ɗaya a kowace shiyyar sanata uku da ke jihar Kano.
Ƙungiyar ta ƙunshi ƙungiyoyi shida na nakasassu, waɗanda suka haɗa da masu matsalar ji, nakasar jiki da gani, masu zabaya, masu raunin laka da kuma masu cutar kuturta.
Haka kuma, akwai masu riƙe da sarautun gargajiya, tsofaffin waɗanda suka taɓa riƙe muƙaman gwamnati da wasu ƙungiyoyin da ke fafutukar kare haƙƙin nakasassu.
Sun nemi muƙamai 88 a ƙananan hukumomi
Ƙungiyar ta kuma buƙaci Gwamna Abba Kabir Yusuf ya naɗa kansila ɗaya da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin nakasassu a kowace ƙaramar hukuma. Wannan buƙata za ta samar da muƙamai 88 a ƙananan hukumomi 44 na jihar.
Bugu da ƙari, sun nemi gwamnan ya kafa Hukumar Nakasassu ta Jihar Kano ta hanyar dokar majalisa cikin watanni shida na farkon wa’adinsa na biyu, idan ya sake lashe zaɓe.
Shirin hukumar ya tanadi cewa a naɗa babban sakatarenta daga cikin masu buƙatu na musamman, sannan ta kasance da mambobi 14 a kwamitin gudanarwarta.
An bayyana waɗannan buƙatu a cikin wata takarda mai taken Commitment to Disability-Inclusive Governance in Kano State (2027–2031), mai kwanan watan 14 ga Nuwamba, 2026.
Ƙungiyar ta kuma nemi muƙamai biyar a matakin gwamnatin jiha, da suka haɗa da mai ba da shawara na musamman, babban mataimaki na musamman, mataimaki na musamman, mataimaki na kai da kuma mai bayar da rahotanni na musamman kan harkokin nakasassu.
Ƙungiyar ta yi magana kan wakilci a gwamnati
Da yake jawabi a taron, shugaban ƙasa na Society for People with Disabilities Forum, Comrade Sherif Sulaiman Ibrahim, ya ce buƙatun sun nuna yadda nakasassu ke son taka rawa sosai wajen tafiyar da gwamnati.
Ibrahim, wanda kuma shi ne daraktan kamfen ɗin mutanen da ke da nakasa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya ce samun wakilci a majalisun dokoki na da matuƙar muhimmanci.
Ya bayyana cewa rashin samun wakilan nakasassu a Majalisar Dokokin jiha da Majalisar Tarayya na cikin abubuwan da suka taimaka wajen ƙara tsananta matsalolin da al’ummar ke fuskanta.
Ya ce tuni ya tattauna da Gwamna Yusuf kan kafa hukumar nakasassu, kuma yana da yakinin gwamnan zai kafa ta kafin zaɓen 2027.
Ibrahim ya ƙara da cewa gwamnan ya tabbatar masa da aniyarsa ta kafa hukumar, duk da cewa yarjejeniyar da ƙungiyar ta gabatar ta tanadi kafa ta cikin watanni shida na farkon wa’adi na biyu.
Sun yi gargaɗi ga ’yan siyasa
Daraktan kamfen ɗin ya yi kira ga jam’iyyun siyasa da ’yan takara, ba tare da la’akari da jam’iyyarsu ba, da su nuna jajircewa wajen inganta rayuwar nakasassu.
Ya gargaɗi cewa al’ummar ba za ta goyi bayan ’yan takarar da suka ƙi magance matsalolinsu ba.
A kalamansa, ya ce:
“Ba za mu nemi mutanen da ke da nakasa su goyi bayan duk wani ɗan takara da ba ya goyon bayan nakasassu ba.”
Ya kuma buƙaci ƙungiyoyin nakasassu daban-daban su haɗa kai, yana mai cewa haɗin kansu zai ƙara musu ƙarfin tattaunawa da shugabannin siyasa.
Ƙungiyar ta bayyana ƙarfin masu zaɓenta
Ibrahim ya ce nakasassu a Kano na da damar tattara ƙuri’u tsakanin miliyan ɗaya zuwa biyu. Sai dai a cikin yarjejeniyar da suka gabatar, ƙungiyar ta bayyana cewa tana da mambobi sama da 600,000 da suka yi rajistar zaɓe a faɗin ƙananan hukumomi 44 na jihar.
A ƙarƙashin yarjejeniyar, ƙungiyar ta yi alƙawarin tattara mambobinta da iyalansu domin tallafa wa neman wa’adi na biyu na Gwamna Abba Kabir Yusuf.
Ta kuma yi alƙawarin zama jakadun kamfen ɗin gwamnan kan harkokin nakasassu, da shiga ayyukan wayar da kan masu zaɓe da tabbatar da gudanar da zaɓe cikin lumana.
Yarjejeniyar ta kuma tanadi kafa kwamitin aiwatarwa mai mambobi bakwai, waɗanda za su ƙunshi wakilan nakasassu huɗu da mutum uku daga tawagar kamfen ɗin gwamnan.

Source: Original
Matar Gwamna Abba ta nemi saki
A wani labarin kuma, kun ji cewa Zainab Musa Kwankwaso, matar Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf ta biyu, ta shigar da ƙarar neman a kashe aurensu a Kotun Shari’a da ke Gudu, Abuja.
Takardar sammaci mai lambar CV/97/26 ta umarci gwamnan da ya bayyana a gaban kotun a ranar 17 ga Nuwamba, 2026.
Asali: Legit.ng


