Sheikh Pantami Ya Yi Magana kan Hadarin da Shugaban APC Ya Yi
- Kungiyar Pantamiyya Movement ta yi ta’aziyya ga iyalan mutanen da hatsarin mota ya rutsa da su a hanyar Deba zuwa Talasse a jihar Gombe
- Hatsarin ya rutsa da shugaban APC na jihar, Mohammed Dantata Ndus, da daraktan yakin neman zaben jam’iyyar na 2027, Sa’adu Hassan
- Kungiyar ta kuma yi addu’ar Allah ya jikansa da mai babur da ya rasu, tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Gombe – Kungiyar Pantamiyya Movement ta yi ta’aziyya ga iyalan wadanda hatsarin mota ya shafa a hanyar Deba zuwa Talasse a jihar Gombe, inda ta yi addu’ar Allah ya ba wadanda suka jikkata lafiya cikin gaggawa.
Hatsarin ya rutsa da shugaban jam’iyyar APC na jihar Gombe, Hon. Mohammed Dantata Ndus, da daraktan kwamitin yakin neman zaben gwamnan jihar na jam’iyyar a 2027, Malam Sa’adu Hassan.

Source: Facebook
A cikin wata sanarwa da Sheikh Isa Ali Pantami ya fitar a Facebook ranar Talata, 17 ga Nuwamba, 2026, ya ce ya samu labarin hatsarin cikin matukar alhini da jimami.
Pantami jajantawa 'yan APC
Kungiyar Pantamiyya, karkashin jagorancin dan takarar gwamnan jihar Gombe na jam’iyyar PDP, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ta mika sakon ta’aziyyarta ga iyalai, abokai da makusantan duk wadanda hatsarin ya shafa.
Ta kuma mika ta’aziyya ta musamman ga iyalan mai babur da ya rasa ransa a hatsarin, tana mai cewa tana tare da su a wannan lokaci na bakin ciki.
A sanarwar da ta fitar, kungiyar ta yi addu’ar Allah ya ba iyalan mamacin hakurin jure wannan rashi, ya kuma jikansa da rahama.
An kai wadanda suka jikkata asibiti
Pantamiyya Movement ta bayyana cewa Mohammed Dantata Ndus, Sa’adu Hassan da sauran wadanda suka jikkata na samun kulawar likitoci a Asibitin Koyarwa na Tarayya da ke Gombe da kuma Babban Asibitin Deba.
Kungiyar ta yi addu’ar Allah ya ba su lafiya cikin gaggawa, ya kuma dawo da su cikin koshin lafiya.
Haka kuma, kungiyar ta yi addu’ar Allah ya kare matafiya a kan hanyoyi, tare da hana sake aukuwar irin wannan mummunan lamari.

Source: Original
Sanarwar da Farfesa Suleiman Mohammed ya sanya wa hannu a madadin kungiyar ta nuna cewa ta’aziyyar ta shafi dukkan wadanda hatsarin ya rutsa da su, ba tare da la’akari da matsayinsu na siyasa ba.
ADC ta zargi APC da tarzoma
A wani labarin, mun rahoto cewa jam’iyyar ADC ta yi zargin cewa wasu mutane na shirin amfani da rigunan jam’iyyar wajen haddasa tarzoma gabanin ziyarar Shugaba Bola Tinubu a jihar Kebbi.
Jam’iyyar ta ce ta gano wani shiri na raba rigunan da ke dauke da tambarin ADC ga wasu mutane da ta kira bata-gari, domin su haddasa rikici tare da nuna kamar mambobinta ne suka aikata hakan.
Mataimakin sakataren yada labaran jam’iyyar, Atiku Abubakar, ne ya bayyana zargin a wani taron manema labarai, inda ya ce manufar shirin ita ce a daura wa ADC alhakin duk wata tarzoma da za ta iya faruwa.
Asali: Legit.ng

