Bakin Atiku na Neman Jefa Shi a Matsala, Hukumar DSS Ta ba Shi Zabi 2

Bakin Atiku na Neman Jefa Shi a Matsala, Hukumar DSS Ta ba Shi Zabi 2

  • Hukumar DSS ta ce binciken cikin gida da ta gudanar bai tabbatar da zargin Atiku Abubakar na shirin tayar da zanga-zanga a Sokoto ba
  • Atiku ya zargi jami’an DSS da tara mutane domin haddasa hargitsi da ba gwamnatin APC ta Sokoto damar sanya dokar hana fita
  • DSS ta buƙaci Atiku ya janye zargin a bainar jama’a, ya fayyace matsayarsa ko kuma ya gabatar da hujjoji domin ci gaba da bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta ce binciken da ta gudanar kan zargin, Atiku Abubakar, cewa ta shirya zanga-zanga a Jihar Sokoto domin kawo cikas ga kamfen ɗin ADC, bai gano wata hujja da ke tabbatar da zargin ba.

Saboda haka, hukumar ta buƙaci Atiku ya janye zargin a bainar jama’a ko ya fayyace matsayinsa, ko kuma ya gabatar da sahihiyar hujja da za ta taimaka wajen ci gaba da bincike.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa ya yi murabus daga mukaminsa kan wasu zarge zarge

DSS ta kalubalanci kan zargin kai hari a Sokoto
Atiku Abubakar na gabatar da jawabi a wajen taro Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktan hulɗa da jama’a da dabarun sadarwa ta hukumar, Favour Dozie, ta fitar ranar Talata, 17 ga watan Nuwamban 2026 a shafin X.

Yadda Atiku ya yi zargi kan DSS

A ranar 3 ga Nuwamba, Atiku ya zargi shugabannin DSS da ɗaukar mutane domin shirya zanga-zanga a Sokoto, da nufin haddasa rikici da kuma ba gwamnatin jihar da APC ke jagoranta hujjar sanya dokar hana fita.

Dan takarar shugaban kasar ya yi zargin cewa hakan zai hana ADC gudanar da harkokin yaƙin neman zaɓenta a jihar.

Atiku ya kuma yi ikirarin cewa an tara wasu daga cikin masu zanga-zangar a wani ofishi da ke bayan bankin Zenith a kan titin Koko Road.

Ya ce an ajiye manyan motoci a wurin, sannan aka tura su zuwa wasu muhimman wurare, ciki har da wani zagaye-zagaye.

DSS ta ce ta gudanar da bincike

Kara karanta wannan

Siyasa ta yi zafi: Kwankwasiyya ta yi martani mai zafi ga gwamnatin Abba

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mataimakiyar daraktan hulɗa da jama’a da dabarun sadarwa ta hukumar, Favour Dozie, ta fitar ranar Talata, 17 ga watan Nuwamban 2026 a shafin X.

A cikin sanarwar, hukumsr DSS ta ce ta fara binciken cikin gida ne bisa umarnin Darakta-Janar ɗinta.

Hukumar ta ce ta faɗaɗa binciken ta hanyar tattaunawa da shugabanni da mambobin ADC, da sauran masu ruwa da tsaki a Jihar Sokoto.

Sanarwar ta ce:

“Sakamakon binciken farko bai tabbatar da zargin ba, domin ba a samu wata hujja da za ta tabbatar da hakan ba.”

Taimakon da aka yi wa ɗan takarar ADC

Hukumar ta ce ta samu wasiƙun godiya daga shugaban ADC na jihar da ɗan takarar gwamnan jam’iyyar a Sokoto, Mannir Daniya, sakamakon matakin da jami’anta suka ɗauka lokacin da aka kai masa hari.

DSS ta ce jami’anta da aka tura domin kare Daniya sun fitar da shi zuwa wani wuri mai aminci a ranar 31 ga Oktoba, 2026, lokacin da aka kai masa hari a jihar.

A cewar hukumar, an kai wa jami’anta biyu hari a yayin lamarin, kuma har yanzu suna karɓar magani a asibiti.

Kara karanta wannan

Babu ladabi: 'Yan TikTok sun yi rashin kunya ga Sheikh Daurawa a Kano

Ta ƙara da cewa Daniya da kansa ya tuntubi daraktan hukumar na jihar domin nuna godiya, tare da neman a ƙara masa jami’an tsaro.

DSS ta buƙaci Atiku ya fayyace zarginsa

Hukumar ta ce matakin da ta ɗauka na kare ’yan siyasa ba tare da la’akari da jam’iyyarsu ba ya saɓa da zargin Atiku.

Ta kuma bayyana damuwarta cewa irin wannan zargi na iya rage wa jami’an tsaro ƙwarin gwiwa, musamman waɗanda ke jefa rayukansu cikin haɗari yayin gudanar da ayyukansu.

Sanarwar ta kara da cewa:

“Duk da cewa hukumar ta amince da wasiƙun godiya daga shugaban ADC da ɗan takarar gwamnan jam’iyyar a Jihar Sokoto, har yanzu tana buƙatar mai girma Atiku ya fayyace batun a bainar jama’a, kasancewar zargin an yi shi a bainar jama’a, ko kuma ya gabatar da sahihiyar hujja idan yana da ita domin a ci gaba da bincike.”

Hukumar ta kuma bayyana cewa tana maraba da duk wani bincike na gaskiya da zai gudana cikin 'yanci domin gano sahihancin zargin.

DSS ta kalubalanci Atiku
Atiku Abubakar na jawabi a wajen yakin neman zabe Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Jigon PDP ya soki Atiku

A wani labarin kuma, kun ji cewa wani jigon jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya soki yawan yunƙurin tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, na neman shugabancin Najeriya.

Sowunmi ya yi ikirarin cewa ’yan Najeriya sun sha ƙin amincewa da burin Atiku na zama shugaban ƙasa a lokutan zaɓe daban-daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng