Shugaba Tinubu Ya Yi Hira da Fitacciyar 'Yar Amurka, za a Saki Bidiyon Tattaunawar
- Shugaban kasa Bola Tinubu ya yi wata hira ta musamman da fitacciyar masaniyar siyasa kuma mai sharhi kan kafafen yada labarai ta Amurka, Diana London
- Ana sa ran za a fitar da hirar nan ba da jimawa ba, kamar yadda wani hadimin shugaban APC na kasa ya bayyana a wata sanarwa
- Diana London ta wallafa hotunanta a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda aka gan ta tare da Tinubu da shugaban ma’aikatan fadar, Femi Gbajabiamila
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya yi wata hira ta musamman da fitacciyar ‘yar jarida kuma mai sharhi kan kafafen yada labarai ta Amurka, Diana London.
Ana sa ran za a fitar da hirar nan ba da jimawa ba, kamar yadda Imran Muhammad, babban mataimaki na musamman kan kafafen yada labarai ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana.

Source: Facebook
Imran Muhammad ne ya sanar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Talata bayan ganawar London da shugaba Tinubu.
Diana London ta gana da Tinubu
A sakon da ya wallafa, Muhammad ya ce Tinubu ya yi hira ta musamman da Diana London, wadda ya bayyana a matsayin fitacciyar mai sharhi kan harkokin siyasa da kafafen yada labarai a Amurka.
Ita ma London ta wallafa hotunanta a fadar shugaban kasa da ke Abuja, inda aka gan ta tare da Tinubu da shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila.
A rahoton da Punc ta wallafa, ta ce London ta bayyana cewa hadin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka na samar da sakamako mai kyau.
London ta yabi Najeriya da Amurka
A wani sakon daban, London ta ce hadin gwiwar tsaro tsakanin Amurka da Najeriya na taimakawa wajen samun zaman lafiya ta hanyar karfin tsaro.
Ta ce nasarar hadin gwiwar na da alaka da kyakkyawar alakar da ke tsakanin Shugaban Amurka Donald Trump da takwaransa na Najeriya, Bola Tinubu, da kuma kokarin da kasashen ke yi wajen kawar da ’yan ta’adda.
London ta kara da cewa hadin gwiwar na iya bude karin damammakin cinikayya da bunkasa tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.

Source: Facebook
Ta bayyana Najeriya a matsayin babbar kawar Amurka a nahiyar Afirka, tana mai cewa akwai damammakin tattalin arziki da cinikayya masu yawa da za a iya samu ta hanyar kyakkyawar alakar kasashen.
Tinubu zai ba da rancen gini
A wani labarin, mun rahoto cewa Shugaba Bola Tinubu ya sanar da wani shirin gwamnatin tarayya da zai bai wa ’yan Najeriya masu cancanta damar samun bashin sayen gida har Naira miliyan 100.
Shugaban ya ce za a bayar da bashin ne ta hanyar asusun MREIF, wanda ke da jarin Naira tiriliyan 1, kan samar da ribar kashi 9.75 cikin 100, tare da damar biyan kudin cikin shekara 20.
Tinubu ya bayyana cewa mai neman bashin zai fara da biyan kashi 10 cikin 100 na kudin gidan. Ya kuma ce sama da ’yan Najeriya 2,300 a jihohi 27 sun riga sun amfana da bashin gidaje na Naira biliyan 160.
Asali: Legit.ng

