Wata Sabuwa: An Fallasa Shirin Tafka Magudi a Babban Zaben 2027

Wata Sabuwa: An Fallasa Shirin Tafka Magudi a Babban Zaben 2027

  • Seriake Dickson ya yi zargin cewa wasu na shirin sauya sakamakon zaɓen 2027 tare da amfani da jami’an tsaro na bogi wajen tsoratar da masu zaɓe
  • Sanatan ya buƙaci INEC da jami’an tsaro su gudanar da ayyukansu bisa doka, cikin adalci da ƙwarewa, tare da guje wa tsoratar da jama’a
  • Dickson ya zargi APC da dogaro da taron jama’ar da aka biya kuɗi da kuma masu riƙe da muƙaman siyasa wajen nuna goyon baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bayelsa - Jagoran jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) na ƙasa, Seriake Dickson, ya yi zargi kan shirin magudi a zaben 2027.

Sanata Dickson ya yi zargin cewa wasu mutanen da bai bayyana sunayensu ba na shirin yin maguɗin sakamakon zaɓen 2027 tare da amfani da jami’an tsaro na bogi wajen tsoratar da masu zaɓe.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Dalung ya hango matsalar da za ta iya zama hatsari ga ADC a zaben 2027

Sanata Dickson ya yi zargi kan zaben 2027
Sanata Seriake Dickson na jawabi a wajen taron NDC Hoto: @IamHSDickson
Source: Facebook

Dickson, wanda ke wakiltar mazabar Bayelsa ta Yamma a Majalisar Dattawa, ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Alhamis, 12 ga watan Nuwamban 2026.

A cikin saƙon, tsohon gwamnan jihar Bayelsa ya bayyana abin da ya tattauna da shugabannin matasa da mata na NDC daga mazabu daban-daban a ƙaramar hukumar Ekeremor.

Dickson ya yi gargadi kan maguɗin zaɓe

Sanatan ya ce ya sanar da shugabannin jam’iyyar game da zargin shirin yin maguɗin zaɓe, inda ya buƙace su da su kasance cikin shiri domin kare sahihancin tsarin zaɓe.

“Na kuma bukace su da su kasance cikin shiri tare da kare sahihancin tsarin zaɓe.
“Ina sane da zargin shirye-shiryen sauya sakamakon zaɓe da kuma tura jami’an tsaro na bogi domin tsoratar da masu zaɓe.” In ji shi.

Dickson ya ƙara da cewa ya ƙarfafa wa ’yan ƙasa gwiwar yin tsayin daka wajen ƙin amincewa da duk wani nau’in maguɗin zaɓe ko tsoratarwa, ta hanyoyin da doka ta amince da su.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kwantar da hankulan 'yan Najeriya, ya fadi shirinsa kan kawo karshen rashin tsaro

Sai dai tsohon gwamnan bai ambaci sunan wata jam’iyyar siyasa ko wani mutum da yake zargi da shirin aikata waɗannan abubuwa ba.

An yi kira ga hukumar INEC

Ya jaddada cewa babu wani shugaban ƙasa ko shugaban hukumar tsaro da zai ba wa wani umarnin kashewa, raunatawa ko harbin mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba a cikin al’ummominsu ranar zaɓe.

Ya kuma buƙaci jami’an tsaro da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) su gudanar da ayyukansu bisa doka, ba tare da nuna bambanci ba, kuma cikin ƙwarewa.

Dickson ya ce ’yan ƙasa na da haƙƙin ƙalubalantar duk wani mataki da ya saɓa wa doka, tare da kai rahoton tsoratarwa ko yunƙurin maguɗin zaɓe ga hukumomin da abin ya shafa.

Dickson ya yi zargin ana shirin magudin zabe
Sanata Seriake Dickson na jawabi ga matasan da suka ziyarce shi Hoto: Henry Seriake Dickson
Source: Facebook

Dalilin Dickson na kin shiga APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa Sanata Seriake Dickson, jagoran ƙasa na Nigeria Democratic Congress (NDC), ya fito ya bayyana dalilinsa na kin shiga jam'iyyar APC mai mulki.

Sanata Seriake Dickson ya ce ya ƙi shiga APC ne saboda bai yarda Najeriya ta koma ƙasar da jam’iyya ɗaya ke mulki ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng