Yadda Tinubu Ya Tarairayi Naira Ta Dawo Hayyacinta, Ya Kare Manufofinsa

Yadda Tinubu Ya Tarairayi Naira Ta Dawo Hayyacinta, Ya Kare Manufofinsa

  • Shugaba Bola Tinubu ya kare darajar Naira, yana mai cewa kuɗin Najeriya da ya kusan kai N1,300 kan dala
  • Tinubu ya bayyana haka ne yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC da aka gudanar a Akwa Ibom ranar Juma'a
  • Shugaban ƙasar ya ce haɗa farashin musayar kuɗaɗen waje wuri guda da gwamnatinsa ta yi a 2023 ya taimaka wajen hana Naira durƙushewa gaba ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya kare yadda Naira ta kasance a ƙarƙashin gwamnatinsa inda ya fadi fa'idojin da aka samu kan haka.

Kara karanta wannan

Aiki ya samu kwamishinoni a jihohi, Gwamnatin Tinubu ta ba su abin yi kan zaɓe

Tinubu ya bayyana cewa da ba don sauye-sauyen da ya kawo a harkar musayar kuɗaɗen waje ba, da kuɗin ƙasar ya rasa darajarsa gaba ɗaya.

Tinubu ya kare manufofin tattalin arzikinsa
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Twitter

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Juma'a yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar APC a jihar Akwa Ibom, cewar Punch.

Tinubu ya kare sukar gwamnatinsa da ake yi

Shugaban ƙasar ya yi watsi da sukar da ake yi wa gwamnatinsa kan faɗuwar darajar Naira idan aka kwatanta da dalar Amurka.

Ya bayyana cewa duk da yadda Naira ke canjawa a kan kusan N1,300 kan dala ɗaya, har yanzu kuɗin yana da darajar da za a iya amfani da shi.

A kalamansa:

"Da ba mu ɗauki matakin da na ɗauka a ranar da na karɓi mulki ba, da yanzu sai muna amfani da amalanke wajen ɗaukar Nairarmu saboda da ba za ta da wata daraja ba.
"Kuna magana kan N1,300 kan dala ɗaya. Kai, kai, har yanzu tana da darajar da za a iya sakawa a aljihu. Da mun bar yadda ake tafiyar da ita a baya, da sai ana amfani da amalanke zuwa kasuwar tumatir."

Kara karanta wannan

Sanata Yari ya yi wa yankin Tinubu gori kan kuri'u, ya bugi kirki kan Arewa

Tinubu ya fadi gyaran da ya yi a fannin tattalin arziki
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya yana jawabi a taro. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Getty Images

Yadda Tinubu ya sauya tsarin musayar kuɗi

A watan Yunin 2023, jim kaɗan bayan hawansa mulki, Tinubu ya sanar da haɗa tsarin musayar kuɗaɗen waje daban-daban na Najeriya wuri guda.

Matakin na daga cikin sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatinsa domin rage tazarar da ke tsakanin farashin dalar Amurka a kasuwar gwamnati da kasuwar bayan fage.

Bayan aiwatar da manufar, Naira ta yi matuƙar faɗuwa daga kusan N750 kan dala ɗaya zuwa kusan N1,900 kafin daga bisani ta farfaɗo zuwa kusan N1,300, kamar yadda Tinubu ya bayyana.

Tinubu ya kawo sabon shirin tallafi

An ji cewa hukumar SMEDAN ta ƙaddamar da shirin da ke da burin samar da hamshakan ’yan kasuwa 100 ta hanyar horo da tallafin kuɗi.

Shirin zai haɗa da gasar gabatar da dabarun kasuwanci da kyautar Naira miliyan 100, domin tallafa wa ƙananan ’yan kasuwa.

An ce za a raba tallafin a taron GROW Nigerian na shekarar 2026 da muke ciki da kuma wani taro da za a gudanar a Arewacin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.