An Bayyana Tulin Ayyukan Alherin Tinubu a Arewa da Ya Cancanci Tazarce a 2027

An Bayyana Tulin Ayyukan Alherin Tinubu a Arewa da Ya Cancanci Tazarce a 2027

  • Tsohon ɗan takarar majalisar dokokin Zamfara, Hon. Naziru Aliyu Kaura, ya bayyana nasarorin da Shugaba Bola Tinubu ya samu tun bayan hawansa mulki
  • Ya ce gwamnatin Tinubu ta aiwatar da ayyukan tituna, tallafa wa ɗalibai da manoma tare da ƙoƙarin farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya
  • Kaura ya buƙaci matasa su fito kwansu da kwarkwatarsu domin nuna goyon baya ga Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaura, Zamfara - Tsohon dan takarar majalisar jihar Zamfara Hon. Naziru Aliyu Kaura ya yi magana kan nasarorin Bola Tinubu.

Hon. Kaura ya bayyana irin abubuwan ci gaba da Tinubu ya kawo a yankin Arewacin Najeriya.

Hon. Nazir ya yabawa salon mulkin Tinubu
Hon. Nazir Aliyu Kaura da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: Nazir Aliyu, Asiwaju Bola Ahmad Tinubu.
Source: Facebook

Dan siyasar ya bayyana haka ne yayin zantawa da wakilin Legit Hausa a ranar Juma'a 6 ga watan Nuwambar 2026 da muke ciki.

Kara karanta wannan

"Nan ba da daɗewa ba yan Najeriya za su fara murna da tsare tsaren Shugaba Tinubu"

Matashi ya kare salon mulkin Tinubu

Matashin ya ce Tinubu ya yi ayyukan hanyoyi, taimakawa dalibai da farfaɗo da tattalin arzikin Najeriya.

Har ila yau, ya ce Tinubu ya ba da gudunmawa wurin tabbatar da samun ingantaccen lafiya a yankin.

Ya bayyana yawan kilomita na hanyoyi da ya zagaye kusan dukkan jihohin Arewa musamman a Arewa maso Yamma.

Har ila yau, matashin ya yi magana kan tsadar rayuwa inda ya ce wannan matsala ba iya Najeriya ko gwamnatin Tinubu kadai ba ce, kasashen duniya da dama na fama da irinta.

Ya ce:

"A bangaren ilimi, Tinubu ya ware N17bn kan harkar, ya raba motoci a jihohi na sufuri da ya kai N3.5bn da yawanci jihohi suka amfana.
"Sannan ya ware N1.6bn ga manoma domin tabbatar da inganta harkokin noma, fannin dalibai kuma ya ba su lamuni saboda yadda yaranmu kowa ya san ba su karatu sosai.
"Maganar tsadar rayuwa kuma zai zo ƙarshe idan Allah ya so musamman idan Bola Tinubu ya yi nasara a zaɓen 2027."

Kara karanta wannan

Matsalar da Tinubu ya fara cin karo da ita bayan dawowa Najeriya daga Umrah

An yaba ayyukan alherin Tinubu a Arewa
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Bayo Onanuga.
Source: Facebook

Hon. Kaura ya yi kira ga matasa da su fiti kwansu da kwarkwata domin nunawa Bola Tinubu gata a zaɓen 2027.

Ya tabbatar da cewa sake zaben Bola Tinubu zai kara taimakawa yankin da kuma samun abubuwan ci gaba fiye da wanda aka samu a shekarunsa na farko daga 2023 zuwa 2027.

Fahimtar wasu kan mulkin Tinubu

Duk da wannan ikirari na matashin, akwai wadanda ke ganin babu abin da Tinubu ya tsinana a mulkinsa sai dai kara tabarbarewar tsaro, tsadar rayuka da kuma kara karbo basuka.

Wasu gani suke yi idan har aka ba Tinubu dama a karo na biyu, komai na iya lalacewa a kasar da har zai iya durkusar da ita.

Ta'addanci: Dan APC ya kare gwamnatin Tinubu

A wani labarin, mun kawo muku cewa ana ci gaba da caccakar masu yada maganar murabus din ministan tsaro, Christopher Musa a mukaminsa.

Wani masoyin Bola Tinubu, Khamis Musa Darazo ya bukaci 'yan siyasa da masu ruwa da tsaki su daina siyasantar da batun tsaro Darazo ya yabawa.

Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa mai ritaya, saboda jajircewa wajen yaki da ta'addanci wanda ya addabi musamman Arewacin Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.