Abdulaziz Yari Ya Fadi Yadda za Su Tunkari Talakawa Su Tallata Tinubu
- Sanata Abdulaziz Yari ya bayyana shirye-shiryen da suke domin tunkarar zaben shugaban kasa na 2027 karkashin jam'iyyar APC
- Ya bayyana haka ne a wata hira bayan bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu zai kaddamar da kamfen din shi a jihar Kaduna
- Sanata Yari ya sanar da cewa jam'iyyar APC da Bola Tinubu ba su tsoron Atiku Abubakar da Peter Obi a zaben da suka tunkara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Sanata Abdulaziz Yari ya yi magana kan shirin da suke suke domin tunkarar talakawa da shugabanni a zaben shugaban kasa na 2027.
Ya bayyana cewa alamu sun nuna cewa shugaban kasa Bola Tinubu ne zai yi nasara saboda yadda yake da mutane a Kudu da Arewa.

Source: Facebook
A matsyinsa na Darakta Janar na kamfen din Tinubu, Yari ya yi magana ne a wata hira da ya yi da DW Hausa kuma ta wallafa a Facebook.
Shirin tunkarar jama'a
Abdulaziz Yari ya bayyana cewa sun fara shiri tun mako hudu da suka gabata, inda ya ce za su bukaci 'yan Najeriya su ba su hadin kai.
A game da kamfen, ya ce suna bin matakai matakai ne. Ya ce akwai lokacin da za su bi kan talakawa bayan sun bi kan shugabanninsu.
Ya ce za su bi kan shugabannin talakawa da su talakawan kansu domin bayyana manufofinsu don su zabe su a 2027.
Game da Atiku Abubakar da Peter Obi, Sanata Yari ya ce ba su tsoronsu kwata-kwata, inda ya ce kuma lissafi ya nuna cewa Bola Tinubu zai yi nasara saboda yana da goyon baya a Kudu da Arewa.
Ya ce babu wanda ya yi karfi a siyasa a Arewa kamar Muhammadu Buhari, amma bai yi nasara ba sai da ya hada kai da Kudu, inda ya ce Atiku da Obi ba su da irin wannan hadin kai, amma Tinubu yana da shi.
Maganar tallafin man fetur
Da aka tambaye shi dalilin dawo da tallafin man fetur, Sanata Ya bayyana cewa ba yadda za a yi a ciwo bashi a biya tallafin man fetur ba.
'Ba za a ciwo ba shi a biya tallafi ba, har abada. A ci ba shi a Najeriya don a biya tallafin man fetur. A tara wa 'ya'yanka ba shi."
A karkashin haka ya ce matakan da aka dauka sun kawo sauki sosai, inda ya bayar da misali kan yadda farashin kayan abinci ya yi kasa sosai.

Source: Getty Images
Magana kan rashin tsaro
Sanata Yari ya bayyana cewa ba yau aka fara rashin tsaro a Najeriya, inda ya ce a shekarun baya bama-bamai suna tashi a Abuja amma yanzu ba a yi.
Ya ce suna kokari domin magance matsalar tsaro, inda ya ce APC ta kawo Janar na soja (Buhari) domin magance matsalar tsaro amma Allah bai yi ba.
APC za ta fara kamfen a Kaduna
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC za ta kaddamar da yakin neman zaben ta na shekarar 2027 a jihar Kaduna.
Wata sanarwa da kwamitin yakin neman zaben shugaba Bola Tinubu ya fitar ta nuna cewa bayan Kaduna, za su wuce Rivers.
Hakan na zuwa ne yayin da 'yan siyasa daga jam'iyyu daban-daban ke kara shiri domin tunkarar jama'a su bayyana manufofinsu.
Asali: Legit.ng


