Limamin Masallaci Ya Tsoma Kansa a Matsala kan Tallata Shugaba Tinubu

Limamin Masallaci Ya Tsoma Kansa a Matsala kan Tallata Shugaba Tinubu

  • An cire Imam Dahiru Abubakar daga limanci bayan zargin yaƙin neman zaɓen Tinubu a lokacin wa’azi bayan salloli
  • Kwamitin masallacin ya bayyana cewa ya sha gargaɗin limamin kan mayar da masallaci dandalin siyasa
  • Ana zargin limamin ya kuma nemi a sauya sunan masallacin zuwa “Masjid Imam Bola Ahmed Tinubu”, amma kwamitin ya ƙi amincewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - An cire Imam Dahiru Abubakar, limamin wani masallaci da ke unguwar Madina a cikin garin Bauchi, daga mukaminsa bisa zargin yaƙin neman zaɓen sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

An ce limamin ya kasance yana nuna goyon bayansa ga sake zaɓen Tinubu a fakaice yayin wa’azin da yake yi wa jama’a bayan kammala sallolin farilla.

An cire limami a Bauchi kan Tinubu
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce an dakatar da shi bayan ya sake yin hakan bayan sallar Asuba a ranar Lahadi, 18 ga watan Oktoban 2026.

Kara karanta wannan

"Babu zagi": Yari ya fadi abin da za su tallata Shugaba Tinubu da shi

Wata majiya ta bayyana cewa limamin kan gaya wa masu sallah cewa Tinubu ba shi ne ya haddasa matsalar rashin tsaro ba, kuma ya cancanci a sake zaɓensa.

Majiyar ta ce:

“An kafa kwamiti bayan ya sake yin irin wannan abu a ƙarshen makon da ya gabata, daga bisani kuma aka cire shi daga mukaminsa.”

Abin da Limamin ya ce kan wa’azinsa

Imam Dahiru Abubakar ya ce ya kasance yana wa’azi ga jama’a cewa Shugaba Tinubu ba shi ne musabbabin matsalolin da ƙasar ke fuskanta ba, yana mai danganta matsalolin tattalin arziki da rashin tsaro da abin da ya kira abubuwan da ke faruwa a ƙarshen zamani.

“Na kasance ina wa’azi ga jama’a da su daina zargin Shugaba Tinubu kan matsalar rashin tsaro da ƙalubalen tattalin arziki. Na ƙarfafa musu gwiwa su shirya zaɓensa tare da ba shi wani wa’adi a shekarar 2027 domin ya ci gaba da mulkinsa."
“Wa’azina ya fi mayar da hankali kan ƙarfafa tsoron Allah da kuma daina ɗora wa shugabanni laifin matsalar rashin tsaro, musamman Shugaba Tinubu, domin taimakon Allah ne kawai zai iya kawo ƙarshen waɗannan matsaloli ta hanyar addu’a. Amma wannan bai yi wa kwamitin masallacin daɗi ba.” In ji shi.

Kara karanta wannan

Tinubu na da abin da zai fada wa yan Najeriya su zaɓe shi a 2027? Baba Ahmed ya yi magana

Limamin ya ƙara da cewa wa’azinsa ya fi karkata ga tsoron Allah da yadda ya kamata mutane su gudanar da ayyukansu na yau da kullum.

Ya ce ya kasance yana kawo misalan matsalolin rashin tsaro da ake fuskanta a wasu ƙasashen Afirka, ciki har da Sudan, Chadi da Mali, yana tambayar ko Shugaba Tinubu ne ya haddasa matsalolin tsaro a waɗannan ƙasashe.

Dalilin da kwamitin masallacin ya bayar

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, shugaban kwamitin masallacin, Imam Abubakar Jibrin, ya ce matsalarsu da limamin ba ta tsaya ga yaƙin neman zaɓen Tinubu kawai ba, har da yadda yake tara mutane da dama a gaban masallacin, wani lokaci kuma ya shiga cikinsa da nufin tattauna harkokin siyasa.

Jibrin ya ce kwamitin ya zauna da limamin tare da gargaɗinsa kan mayar da masallaci dandalin siyasa. Ya bayyana cewa sun yi hakan ne bisa koyarwar Alƙur’ani cewa masallatai na ibadar Allah ne kaɗai.

“Mun ƙi amincewa da amfani da masallacin wajen tarukan siyasa. Mun yi masa gargaɗi ba sau ɗaya ko sau biyu ba, amma sau da dama, duk da haka bai bi shawarar da muka ba shi ba."

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya fito ya yi maganar dalilin da ya sa Atiku ba zai iya kifar da Tinubu ba

“Ko da yake mun yarda cewa siyasa ita ce hanyar samar da shugabanni a ƙasa, akwai hanyoyin da aka tsara domin gudanar da ita, waɗanda suka haɗa da jam’iyyun siyasa. Ya kamata a gudanar da harkokin siyasa a ofisoshin jam’iyyu, ba a cikin masallaci ba.” In ji shi.

Zargin neman sauya sunan masallacin

Shugaban kwamitin ya kuma ce, baya ga yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa, limamin ya dage kan a sauya sunan masallacin daga Masjid Abdullahi Bin Zubbair zuwa Masjid Imam Bola Ahmed Tinubu.

Sai dai Jibrin ya ce dukkan mambobin kwamitin sun ƙi amincewa da wannan buƙata, saboda masallacin mallakin al’umma ne.

An cire limami a Bauchi
Taswirar jihar Bauchi, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Tinubu ya taya Kwankwaso murna

A wani labarin kuma, kun ji cewa Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Sanatan Kano ta Tsakiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

Shugaba Bola Tinubu ya taya dan takarar mataimakin shugaban kasar na NDC murnar cika shekara 70 da haihuwa a duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng