Maganar Cire Liman kan Goyon Bayan Tinubu Ta Bar Baya da Kura, an Samu Bayanai
- Mazauna unguwar Madina a Bauchi sun musanta ikirarin Dahiru Abubakar na korarsa daga limanci saboda goyon bayan Tinubu
- Wasu mazauna sun ce Dahiru ba limamin masallacin na din-din-din ba ne, sai dai yana jagorantar sallah ne kawai idan limamin masallacin ba ya nan
- Sai dai Jejiwe Danmalam ya dage cewa an cire shi saboda goyon bayansa ga Tinubu, musamman kan tsaro, da shawarar sauya sunan masallacin zuwa sunan shugaban ƙasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Bauchi - Mazauna unguwar Madina da ke cikin birnin Bauchi sun musanta maganar korar ikirarin Dahiru Abubakar Danmalam daga limanci.
Danmalam ya yi ikirarin cewa an cire shi daga limancin wani masallaci saboda goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Source: Twitter
Wasu mazauna unguwar sun ce Abubakar ba shi ne limamin masallacin na din-din-din ba, inda suka bayyana cewa yana jagorantar sallah ne kawai idan limamin da aka sani ba ya nan, cewar Leadership.
Danmalam ya ce an cire shi daga limanci
Sai dai Abubakar ya dage cewa an cire shi daga wani ƙaramin masallacin unguwa da yake jagorantar sallah da kuma wa’azi lokaci zuwa lokaci, yana zargin cewa kamfen ɗin da yake yi wa Bola Tinubu ne ya haddasa matakin.
Wani mazaunin unguwar mai suna Ibrahim Muhammad, wanda ya ce ya san lamarin, ya bayyana Abubakar a matsayin mutum mai jawo ce-ce-ku-ce, wanda ya yi zargin yana hulɗa da ’yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban.
Muhammad ya ce:
“Kowa ya san Jejiwe Danmalam a matsayin ɗan barkwanci kuma mutum mai jawo ce-ce-ku-ce. Yana aiki da kusan kowace jam’iyyar siyasa.”
Ya yi zargin cewa watanni kaɗan da suka gabata, Abubakar ya zargi Tinubu da jam’iyyar APC da haddasa matsin tattalin arziki a ƙasar, kafin daga bisani ya bayyana goyon bayansa ga shugaban ƙasa.
Muhammad ya yi hasashen cewa sauye-sauyen matsayinsa na siyasa na iya kasancewa da alaƙa da rikicin na yanzu, wanda yake ganin wataƙila an ƙirƙire shi ne domin jawo hankalin jama’a.
Ya kuma dage cewa Abubakar ba shi ne limamin masallacin na din-din-din ba, yana mai cewa tuni masallacin yake da sanannen jagoran addini.
Muhammad ya shawarci ’yan jarida da sauran jama’a su tabbatar da sahihancin bayanai kafin yaɗa su, musamman a lokacin da harkokin siyasa suke ƙara ƙarfi gabanin zaɓen 2027.
Ya ce:
“A wannan lokacin siyasa, kowa zai nemi hanyar jawo hankalin jama’a. Saboda haka, yana da muhimmanci ’yan jarida su tabbatar da sahihancin bayanai kafin yaɗa su.”
Ya ƙara da cewa bai kamata a jawo addini cikin saɓanin siyasa ko amfani da shi wajen neman moriyar kai ba.

Source: Original
Mutane sun fadi ra'ayinsu kan Danmalam
Wani abokin hulɗar Abubakar da ke zaune a unguwar shi ma ya musanta cewa shi ne limamin masallacin na din-din-din.
Ya ce:
“Ba shi ne limamin masallacin na din-din-din ba. Yana jagorantar sallah ne kawai idan ainihin limamin ba ya nan. Wannan shi ne kawai.”
Haka kuma, wani mazaunin unguwar mai suna Adamu Garba ya musanta cewa Abubakar ne limamin masallacin, cewar Punch.
Garba, wanda ya ce yana zaune a titin kusa da makarantar Barden Gabas, inda ake cewa masallacin yake, ya bayyana cewa sun ji labarin takaddamar.
Kamfe: Yele Sowore ya nemi alfarmar Tinubu
Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar AAC ta Omoyele Sowore ta tura bukata ta musamman ga Shugaba Bola Tinubu ya ba ta izinin ƙaddamar da kwamitin kamfen.
Jam’iyyar ta kuma nemi a samar da abinci, abubuwan sha da sauran kayan tallafi ga mahalarta taron da aka tsara gudanarwa.
AAC ta ce amincewa da buƙatarta za ta nuna adalci, daidaito da kuma bai wa dukkan jam’iyyun siyasa damar amfani da cibiyoyin gwamnati.
Asali: Legit.ng


