Shugaban Hukumar Hisbah Ya Yi Murabus daga Mukaminsa, an Ji Dalili

Shugaban Hukumar Hisbah Ya Yi Murabus daga Mukaminsa, an Ji Dalili

  • Barr. Aminu Balarabe Isah ya ajiye muƙaminsa na babban kwamishinan mai kula da sashen Hisbah a Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi
  • Aminu Balarabe Isah ya jaddada cewa murabus ɗin nasa na son ransa ne, kuma ba ya da alaƙa da wata matsala tsakaninsa da Gwamna Bala Mohammed ko wani jami’in gwamnatinsa
  • Tsohon kwamishinan ya gode wa gwamnan bisa damar da ya ba shi ta yi wa jihar Bauchi hidima, yana mai bayyana naɗin nasa a matsayin babban abin alfahari.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Bauchi - Babban Kwamishinan da ke kula da sashen Hisbah a Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi, Barr. Aminu Balarabe Isah, ya yi murabus daga muƙaminsa.

Aminu Balarabe Isah ya sanar da matakin nasa ne ta wata wasiƙa mai kwanan wata 26 ga Oktoba, 2026, wadda ya aika wa Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana kan kisan gilla da aka yi wa Sheikh Masussuka a Katsina

Shugaban Hisbah na Bauchi ya yi murabus
Tsohon shugaban Hisbah na jihar Bauchi, Aminu Balarabe Isah Hoto: Barrister Aminu Balarabe Isah
Source: Facebook

Ya aika wa Gwamna Bala wasika

A cikin wasiƙar, ya bayyana cewa ya yanke shawarar barin muƙamin ne bisa dalilansa na kansa, ba tare da wani matsin lamba ko takaddama da gwamnatin jihar ba, cewar rahoton jaridar Leadership.

“Na rubuto wannan wasiƙa ne domin sanar da kai a hukumance shawarar da na yanke ta yin murabus daga muƙamina na Kwamishinan da ke kula da Hisbah a Hukumar Shari’a ta Jihar Bauchi.”

Ya musanta samun saɓani da gwamnati

Tsohon kwamishinan ya jaddada cewa ya yanke shawarar yin murabus ɗin ne bayan zurfafa tunani kan lamarin.

Ya ce matakin nasa na son ransa ne, kuma ba shi da alaƙa da wata rashin jituwa ko matsala da Gwamna Bala Mohammed ko wani jami’in gwamnatinsa.

A cewarsa, yana barin muƙamin ne cikin mutunta tsarin gwamnati da kuma mutanen da ya samu damar yin aiki tare da su a lokacin da yake riƙe da muƙamin.

Kara karanta wannan

Sakon Gwamna Radda ga mutanen Katsina kan kisan Sheikh Masussuka

Aminu Balarabe Isah ya bayyana cewa bai yanke shawarar ne saboda wata takaddama da gwamnati ba, yana mai jaddada cewa murabus ɗin nasa na kansa ne kawai.

Ya gode wa Gwamna Bala Mohammed

Aminu Balarabe Isah ya kuma nuna godiyarsa ga Gwamna Bala Mohammed bisa damar da ya ba shi ta yi wa gwamnatinsa da al'ummar jihar Bauchi hidima.

Ya bayyana naɗin da aka yi masa a matsayin babban abin alfahari, yana mai cewa yana matuƙar godiya bisa amincewar da aka nuna masa wajen ɗora masa alhakin jagorantar sashen Hisbah.

"Babban abin alfahari ne a gare ni na bayar da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya, kyawawan ɗabi'u da ci gaban Jihar Bauchi ta hannun sashen Hisbah.” In ji shi.

Ya ƙara da cewa yana matuƙar godiya ga gwamnan bisa amincewar da ya nuna masa ta hanyar ba shi wannan muƙami mai muhimmanci da kuma nauyi.

Aminu Balarabe Isah ya yi murabus
Aminu Balarabe Isah a wajen taron Hisbah Hoto: Barrister Aminu Balarabe Isah
Source: Facebook

Shugaban Hisbah ya ajiye aikinsa

A wani labarin kuma, kun ji cewa babban kwamandan hukumar Hisbah ta jihar Katsina, Dr Aminu Usman, wanda aka fi sani da Abu Ammar, ya yi murabus daga mukaminsa.

Dr Aminu Usman ya sanar da murabus din ne a wata wasika mai dauke da kwanan watan 5 ga Oktoba, 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng