An Gargadi Matasan Najeriya kan Sayen Kuri'u da Mutanen da Ya Kamata Su Zaba a 2027
- Masu ruwa da tsaki sun bukaci matasa su zabi ’yan takarar da za su yi shugabanci bisa gaskiya da rikon amana a zaben 2027
- Sun yi gargadin cewa sayar da kuri’a tamkar jinginar da makomar Najeriya ne, suna masu kira ga matasa su shiga siyasa
- Hukumar INEC ta ce tana kokarin inganta ayyukanta tare da karfafa wayar da kan masu kada kuri’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Masu ruwa da tsaki sun bukaci matasan Najeriya su fito su ba da gudummuwa a babban zaben 2027 ta hanyar kada kuri’a ga ’yan takarar da suka cancanta, tare da kin amincewa da sayen kuri’u.
Sun yi gargadin cewa matasan da ke sayar da kuri’unsu suna jingina makomar kasar ne, inda suka jaddada muhimmancin zabar shugabanni bisa halayensu, kwarewarsu da tarihin ayyukansu.

Kara karanta wannan
Kare ya haddasa babbar matsala da ake zargin ta jawo kashe wani bawan Allah a Kano

Source: Facebook
Leadership ta ruwaito cewa Smsun yi wannan kira ne a taron tattaunawa na biyu tsakanin masu ruwa da tsaki kan wayar da kan masu kada kuri’a da shigar matasa cikin harkokin zabe.
Taron ya hada shugabannin matasa, kungiyoyin fararen hula, masu ruwa da tsaki a harkokin zabe, kungiyoyin mata, shugabannin addinai, ’yan jarida, kwararru da wakilan al’umma domin tattauna hanyoyin karfafa shigar matasa siyasa.
Jan hankalin da aka yi wa matasa
Da yake jawabi a taron, Babban Jami’in Shirye-shirye na Kungiyar Kimpact Development Initiative (KDI), Kelvin Agabge, ya ce an shirya taron ne domin hada masu ruwa da tsaki a harkokin zabe don gano kalubalen da ake fuskanta.
Agabge ya bayyana rashin sha’awar kada kuri’a da raguwar shiga harkokin siyasa, musamman a tsakanin matasa, a matsayin manyan matsalolin da ke bukatar daukar matakin gaggawa.
Ya ce:
“Muna son ganin an magance wannan matsala, tare da samun karin matasa da za su shiga harkokin zabe.
Ya bayyana zabe a matsayin damar da ’yan Najeriya za su gyara kura-kuran siyasar baya ta hanyar zabar shugabanni bisa halaye nagari, kwarewa, iya aiki da tarihin ayyukansu, maimakon la’akari da kabila, addini, kudi ko jam’iyyar siyasa.
Ya yi kira da a ci gaba da gudanar da gangamin wayar da kan masu kada kuri’a a makarantu, unguwanni, tashoshin mota, kasuwanni da shafukan sada zumunta, ta amfani da harsuna da hanyoyin sadarwa da matasa za su fahimta cikin sauki.
INEC ta yi bayani kan matsalolinta
A nata bangaren, Mataimakiyar Daraktan Wayar da Kan Masu Kada Kuri’a a INEC, Mrs Paula Iwenyiora, ta amince cewa akwai damuwa kan amincewar jama’a da hukumar.
Ta ce shugaban INEC ya kara yawan ganawa da masu ruwa da tsaki, ya gudanar da rangadin aiki a wurare daban-daban, tare da kokarin karfafa ayyukan hukumar.

Source: Facebook
A cewarta, INEC na kuma kokarin kawar da munanan dabi’u a cikin tsarin aikinta, tare da inganta walwalar ma’aikata domin rage yiwuwar wasu ’yan siyasa su rinjaye su ko kuma su yi musu katsalandan.
Ta bukaci matasa kada su mika makomarsu ta siyasa ga wasu ta hanyar kin shiga zabe, inda ta jaddada muhimmancin shiga jam’iyyun siyasa, bayyana ra’ayoyinsu da kuma neman a ba su wakilcin da ya dace.

Kara karanta wannan
Atiku ya soki DSS, ya fadi makircin da aka shirya domin hana shi gangamin kamfe a Sokoto
Dalilin kirkiro sababbin rumfunan zabe
Kun ji cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yi ƙarin bayani kan rahotannin ƙirƙiro sababbin rumfunan zaɓe 453 a faɗin Najeriya.
Mataimakin daraktan yaɗa labarai na INEC, Wilfred Osilama Ifogah, ya bayyana cewa an kirkiro sababbin rumfunan zabe ne sakamakon hukuncin kotu da ya haifar da ƙirƙiro karin mazaɓu a jihohin Kogi, Benue da Delta.
Asali: Legit.ng
