Matashi Ya Dauki Bindigogi da Niyyar Kashe Trump a Amurka

Matashi Ya Dauki Bindigogi da Niyyar Kashe Trump a Amurka

  • Jami’an tsaron Amurka sun kama wani mutum dauke da bindigogi kusa da fadar White House bisa zargin yin barazanar kashe Shugaba Donald Trump
  • Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka ta ce wanda ake zargin yana cikin motar da aka sace, inda aka gano bindigar AK da wasu bindigogi biyu da harsasai
  • Rahoton ya ce mutumin ya shaidawa jami’an tsaro cewa wasu muryoyi a kansa ne suka umarce shi da zuwa Washington domin kashe Trump

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Jami’an tsaron Amurka sun kama wani mutum kusa da fadar White House bisa zargin mallakar makamai ba bisa ka’ida ba da kuma barazanar kashe Shugaba Donald Trump.

Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka ta bayyana cewa jami’an tsaron sun lura da mutumin mai suna Ronny Yordrix Guanipa Chrinos yana nuna halin shakku a cikin wata mota da ke kusa da fadar shugaban kasar ranar Alhamis.

Kara karanta wannan

An gargaɗi matasan Najeriya kan sayen ƙuri'u da mutanen da ya kamata su zaɓa a 2027

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

A cewar sanarwar ma’aikatar da CNN ta wallafa, mutumin ya fito daga Venezuela, kuma ya shiga Amurka ba bisa ka’ida ba a shekarar 2024.

Abin da wanda ake zargin ya fada

Sanarwar ta ce lokacin da jami’an tsaron suka tunkari mutumin, ya bayyana cewa yana jin wasu muryoyi da ke umartarsa da zuwa Washington, DC domin kashe Shugaba Donald Trump.

Bayan haka, jami’an sun gano cewa motar da yake ciki an bayyana ta a matsayin motar sata, sannan wanda ake zargin ya amsa cewa yana da makamai a cikinta.

Binciken da jami’an suka gudanar ya gano bindiga kirar rifle, bindigogi guda biyu da kuma harsasai da dama a cikin motar.

An gurfanar da wanda ake zargi

An kama Chrinos bisa zarge-zargen mallakar makamai ba bisa ka’ida ba, amfani da abin hawa ba tare da izini ba da kuma karɓar kayayyakin sata.

A halin yanzu, Anadolu ta rahoto cewa yana hannun Hukumar Kula da Gidajen Yari ta Amurka, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

Kara karanta wannan

Zabe ya wuce, Trump na shirin kaddamar da manyan hare hare Iran

Shugaban Hukumar Tsaron Sirri ta Amurka, Sean Curran, ya ce jami’an sun yi amfani da horo da gogewarsu wajen shawo kan lamarin ba tare da barin rikicin ya tsananta ba.

White House da ke Amura
Fadar White House da shugaban Amurka ke zama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya bayyana cewa lamarin na nuna irin barazanar tsaro da jami’an ke fuskanta, musamman daga mutanen da ke zuwa kusa da fadar White House dauke da makamai.

A watan Mayun 2026, jami’an tsaro sun harbe wani mutum mai suna Nasire Best har lahira bayan ya bude wuta kusa da wani shingen binciken jami’an tsaro a fadar White House.

Maganar kai hare-hare Iran

A wani labarin, kun ji cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya gana da jami’an tsaron kasarsa domin tattauna yiwuwar sake fara hare-haren soji kan Iran.

Rahotanni sun nuna cewa rundunar sojin Amurka ta fara kammala shirye-shiryen yiwuwar sake kai manyan hare-hare kan birnin Tehran na Iran.

A gefe guda, Iran ta miƙa wa Amurka sabon shirin tattaunawa kan makamashin nukiliyarta ta hannun Qatar, yayin da Rasha ke kokarin karfafa kokarin diflomasiyya tsakanin kasashen..

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng