Gwamna Ya Bukaci Yan Najeriya Su Karbi Kudin APC amma Su Zabi Wadanda Ya Dace a 2027

Gwamna Ya Bukaci Yan Najeriya Su Karbi Kudin APC amma Su Zabi Wadanda Ya Dace a 2027

  • Dan takarar shugaban kasa na APM, Gwamna Seyi Makinde, ya bukaci ‘yan Najeriya su karbi duk kudin da APC ta ba su a lokacin zaben 2027
  • Ya ce masu kada kuri’a su yi amfani da kudin, amma kada su hakan ya hana su zaben shugabanni nagari da za su kawo sauyi
  • Makinde ya bukaci masu rashin jin dadin halin da kasar ke ciki, musamman matsalar tsaro da yunwa, su mara wa jam’iyyarsa baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Bauchi - Dan takarar shugaban kasa na APM kuma gwamnan jihar Oyo, Injiniya Seyi Makinde, ya bukaci ‘yan Najeriya da su karbi duk wani kudi da jam’iyyar APC mai mulki za ta ba su a lokacin babban zaben 2027.

Sai dai Gwamna Makinde ya bukaci mutane da su kada kuri'unsu ga shugabannin da suke ganin za su iya kawo sauyi tare da ceto kasar nan daga halin da take ciki.

Kara karanta wannan

Bakar wahalar da ‘yan ADC suka sha wahala kafin Atiku ya shirya kamfen a Sokoto

A rahoton Leadershipz Makinde ya ce bai kamata ‘yan Najeriya su ki karbar kudin da aka ba su a lokacin kamfe ba musamnan wadanda suka fito daga APC, yana mai jaddada cewa kudin na al’umma ne.

Ya yi wannan kira ne a ranar Asabar a Bauchi, yayin kaddamar da yakin neman zabensa na shugaban kasa, inda ya bukaci masu kada kuri’a da kada su bari kyautar kudi ta zama sanadin zaben wanda ba su so.

Gwamna Makinde ya ce:

"Idan suka zo da kudi a lokacin zabe, ku karba, idan kudin naku ne, ku karba ku kashe. Amma ku kiyaye lamirinku, sannan ku yanke shawara mai kyau idan lokacin zabe ya yi. Na san zukatanku na tare da mu da kuma ni.”

Makinde ya ja hankalin masu korafi

Dan takarar na APM ya kuma bukaci ‘yan Najeriya da ba su gamsu da halin da kasar ke ciki ba, musamman karuwar rashin tsaro, yunwa da gazawar gwamnati wajen magance manyan matsalolin kasa, da su goyi bayan jam’iyyar APM.

Ya ce:

“Idan ba ku ji dadin halin da kasarmu take ciki a yau ba, musamman karuwar rashin tsaro, yunwa da gazawar gwamnati wajen magance kalubalen da ‘yan Najeriya ke fuskanta, to jam’iyya daya ce gare mu. Wannan jam’iyya ita ce jam’iyyar da ke mutunta Najeriya.”

Kara karanta wannan

“Ko zai shafi Tinubu a 2027?” Yadda al’ummar Legas suka tarbi Kwankwaso ya ja hankali

Makinde ya bukaci ‘yan Najeriya da su shiga tafiyar siyasar APM, inda ya bayyana magoya bayan jam’iyyar da sunan “Resetters”.

Ya ce jam’iyyar ta kuduri aniyar mutunta al’ummomi, karfafa tsarin tsaron kasar da kuma samar da yanayin siyasa da zamantakewa da zai ba karin ‘yan Najeriya damar taka muhimmiyar rawa a harkokin mulki.

Kun ji cewa ɗan takarar shugaban kasa na APM kuma gwamnan Oyo, Seyi Makinde zai kayar da Tinubu a jihohi 12 da ware a matsayin wadanda zaben 2027 zai yi zafi.

Kwamitin yakin neman zaben shugaban na APM ne ya yi wannan ikirarin yayin da yake maida martani kan matakin da Shugaba Bola Tinubu ya dauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262