INEC Ta Fadi Dalilin Kirkiro Sababbin Rumfunan Zabe a Najeriya

INEC Ta Fadi Dalilin Kirkiro Sababbin Rumfunan Zabe a Najeriya

  • Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta yi ƙarin bayani kan rahotannin ƙirƙiro sabbin rumfunan zaɓe 453 a faɗin Najeriya
  • Hukumar ta ce sauye-sauyen sun biyo bayan hukuncin kotu da ya haifar da ƙirƙiro sababbin mazaɓu a jihohin Kogi, Benue da Delta
  • INEC ta ce ba ta gudanar da aikin a ɓoye ba, amma za ta yi cikakken bayani ga masu ruwa da tsaki bayan kammala nazarin dukkan matakan cikin gida

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja – Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana dalilin sauye-sauyen da ake zargin ta yi wa rumfunan zaɓe a wasu jihohin Najeriya gabanin babban zaɓen 2027.

Rahotanni sun yi zargin cewa hukumar ta ƙirƙiro ƙarin rumfunan zaɓe 453 ba tare da sanar da jama'a ko tuntubar muhimman masu ruwa da tsaki a harkokin zaɓe ba.

Kara karanta wannan

An jika wa Netanyahu aiki a Isra'ila bayan kayar da Trump a zaben Amurka

Shugaban INEC a Najeriya
Shugaban hukumar INEC na bayani. Hoto: INEC Nigeria
Source: Twitter

A hira da Daily Trust, mataimakin daraktan yaɗa labarai na INEC, Wilfred Osilama Ifogah, ya bayyana cewa sauye-sauyen sun samo asali ne daga hukuncin kotu da ya haifar da ƙirƙiro sabbin mazaɓu a jihohin Kogi, Benue da Delta.

Hukumar INEC ta yi bayani

Ifogah ya ce ƙirƙiro sababbin mazaɓu sakamakon hukuncin kotu zai shafi tsarin unguwanni da rukunin zaɓe da ke cikin wuraren da abin ya shafa.

Ya bayyana cewa hukumar na buƙatar tabbatar da cewa ta yi cikakken nazari kan dukkan abubuwan da suka shafi aikin kafin bayyana cikakken bayani ga jama'a.

Mataimakin daraktan ya musanta cewa INEC ta gudanar da aikin ne a ɓoye, inda ya nuna cewa mai yiwuwa wani ma'aikacin hukumar ne ya fitar da bayanan kafin lokacin da aka shirya sanar da su a hukumance.

Sai dai bayanin nasa bai tabbatar da adadin ƙarin rukunin zaɓe 453 da ake yaɗawa ba, ko kuma ya bayyana jihohin da aka ƙirƙiro su ɗaya bayan ɗaya.

Kara karanta wannan

INEC ta yi magana kan 'shirin' ɗaga ranar zaɓen shugaban ƙasa a 2027

Karin bayani daga INEC

Ifogah ya bayyana cewa aikin da ake yi yanzu ya bambanta da faɗaɗa rumfunan zaɓe da INEC ta gudanar a shekarar 2020.

A wancan lokacin, hukumar ta mayar da wasu wuraren kaɗa ƙuri'a zuwa rumfunan zaɓe na kansu domin rage cunkoso da sauƙaƙa wa masu zaɓe samun wuraren kaɗa ƙuri'a.

Ya ce an gudanar da aikin ne saboda yawan masu zaɓe da ke wasu rumfunan zaɓe, wanda ya haddasa cunkoso a lokacin zaɓe.

Wajen Zaben Abuja
Wani utum na kada kuri'a a Abuja. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Sai dai wasu masu zaɓe sun koka bayan an sauya musu wuraren kaɗa ƙuri'a, amma hukumar ta tabbatar da cewa sababbin wuraren ba su yi nisa sosai da wuraren da suke amfani da su a baya ba.

INEC ba ta da dan takara a 2027

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana cewa ba ta da ɗan takarar da take so ko wata jam'iyyar siyasa da ta fi so a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

'Ba mu goyon bayan kowace jam'iyya a 2027,' shugaban INEC

Shugaban hukumar, Farfesa Joash Amupitan, ya ce INEC za ta gudanar da aikinta bisa doka da kuma muradin masu zaɓe a Najeriya.

Amupitan ya kuma bayyana cewa hukumar ta kammala matakai tara cikin 14 na shirye-shiryen zaɓen 2027, yayin da rajistar masu zaɓe ke ƙaruwa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng