INEC Ta Yi Magana kan 'Shirin' Ɗaga Ranar Zaɓen Shugaban Ƙasa a 2027
- Shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa hukumar ba ta da shirin sauya ranar zaɓen shugaban ƙasa da na 'yan majalisun 2027
- Amupitan ya ce Rivers ce kan gaba wajen yawan masu katin zaɓe a yankin Kudu maso Kudu, inda take da mutum 3,736,434
- Hukumar INEC ta ce za ta fitar da cikakken kundin masu zaɓe ranar 15 ga Disamba, tare da tabbatar da tsaro yayin zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Joash Amupitan, ya ce hukumar ba ta da shirin sauya ranar zaɓen 2027.
Ya ce an riga an tsara ranar zaɓen, kuma shirye-shiryen gudanar da shi sun yi nisa, saboda haka ba za a sauya jadawalin ba.

Source: Twitter
INEC ta musanta shirin dage zaɓe
Amupitan ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da ma'aikatan hukumar daga jihohi shida na yankin Kudu maso Kudu, domin tantance shirye-shiryensu, cewar Punch.
An gudanar da taron ne a Fatakwal, babban birnin Rivers, ranar Asabar, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen babban zaɓen 2027.
Wannan na zuwa ne yayin da wasu jam'iyyun siyasa ke zargin cewa INEC na shirin ɗage babban zaɓen ƙasar mai zuwa.
Sai dai yayin jawabi ga ma'aikatan hukumar, ciki har da kwamishinonin zaɓe na jihohin yankin, Amupitan ya jaddada cewa babu sauyin jadawalin.
Ya ce lokacin da doka ta tanada domin gudanar da zaɓen ya kafu, kuma hukumar ba za ta sauya shi saboda kowane dalili ba.
A cewarsa, hukumar INEC ta kuduri aniyar gudanar da zaɓe sahihi bisa tanade-tanaden dokokin ƙasar.
Amupitan ya ce:
“Jadawalin da doka ta tanada ya kafu. Ba za mu sauya komai ba. Dole ne a gudanar da zaɓen a lokacin da aka tsara.”

Source: Facebook
Rivers ce kan gaba wajen yawan masu zaɓe
Amupitan ya bayyana cewa hukumar za ta ba Rivers kulawa ta musamman yayin zaɓen mai zuwa, saboda muhimmancin jihar a yankin Kudu maso Kudu.
Ya ce Rivers ce ke da mafi yawan masu rijistar zaɓe a yankin, abin da ya sa hukumar za ta mayar da hankali kanta.
Ya bayyana cewa Rivers na da masu rijistar zaɓe 3,736,434, sai Delta mai mutum 3,525,988 da Edo mai mutum 2,865,263.
Sauran sun haɗa da Akwa Ibom mai mutum 2,566,198, Cross River mai mutum 1,928,978, da Bayelsa mai mutum 1,200,691, cewar Vanguard.
Ya ce jihohi shida na yankin Kudu maso Kudu suna da jimillar masu rijistar zaɓe 15,823,550.
Sai dai ya jaddada cewa hukumar za ta fi mayar da hankali kan Rivers saboda muhimmancinta wajen gudanar da zaɓe a yankin.
INEC ta daura jam'iyyar NDC a shafinta
Kun ji cewa Hukumar zaben Najeriya watau INEC ta sanya jam'iyyar NDC cikin jam'iyyu 20 da za su fafata a zaɓen gwamnan Kano na 202.
NDC ita ce jam'iyya ta 13 a cikin jerin jam'iyyun da hukumar ta amince su tsayar da 'yan takara babban zabe mai zuwa da za a yi a watan Fabrairun 2027.
Sai dai hukumar ba ta bayyana sunan Aminu Abdussalam Gwarzo a matsayin ɗan takarar NDC ba, tana mai cewa hakan ya biyo bayan umarnin kotu.
Asali: Legit.ng

