Matasa Sun Yi Wa Yan Sanda Taron Dangi, Sun Kwace Kudin da Suke Karba daga Masu Motoci

Matasa Sun Yi Wa Yan Sanda Taron Dangi, Sun Kwace Kudin da Suke Karba daga Masu Motoci

  • Wasu matasa sun karɓe kuɗin da ake zargin ’yan sanda sun karɓa daga masu ababen hawa a shingen bincike a jihar Edo
  • Shugaban matasan ya ce jami’an ’yan sanda da jami’an sa-kai sun karɓi N4,200 daga masu babura da sauran matafiya cikin ƙasa da mintuna 30
  • Ya yi kira ga kwamishinan ’yan sanda da ya binciki jami’an da ake zargi da karɓar kuɗin, bayan sun ce suna aiki ne bisa umarnin shugabanninsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Edo, Nigeria - Wasu fusatattun matasa sun ƙwato kuɗin da ake zargin wasu jami’an ’yan sanda sun karɓa daga masu ababen hawa a wani shingen bincike da ke kan hanyar Auchi zuwa Aviele, a jihar Edo.

Lamarin ya faru ne lokacin da matasan suka isa shingen tare da zargin jami’an ’yan sanda da karɓar kuɗi ba bisa ƙa’ida ba daga masu motoci da babura.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi magana kan sace dan takarar shugaban kasa, sun fadi abin da ya faru

Yan sanda.
Wasu jami'an yan sanda suna aikin sintiri a kan titi a Najeriya Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Matasa sun kwace kudi daga yan sanda

Daily Trust ta ce a wani bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta, an ga mutane ƙarƙashin jagorancin wani matashi sanye da gajeren wando da riga mara hannu suna tunkarar jami’an tare da bincikar jikinsu, har da waɗanda ke ɗauke da makamai.

“Ku binciki wannan ma,” shugaban matasan ya umarci wani mutum, yayin da wani ɗan sanda mai ɗauke da makami ya amsa da cewa, “Babu komai a jikina,” yana murmushi.

An ga ɗan sandan ya ɗaga hannayensa biyu yayin da wani mutum ke bincikar jikinsa. Daga bisani, mutumin ya nuna alamar cewa ba a samu komai a tare da jami’in ba.

Yan sanda sun yi kokarin shawo kan matasa

Wani ɗan sanda da ake zargin shi ne shugaban tawagar ya yi ƙoƙarin miƙa wayarsa ga shugaban matasan domin ya yi magana da wani da ba a bayyana ko wanene ba, a ƙoƙarin da ake ganin na kwantar da tarzomar ne.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga suka kafa gwamnatinsu, suke karɓar haraji kala 3 a jihohin Arewa 2

Sai dai matashin ya ƙi, yana ihu da cewa, “Ba na son magana!” yayin da jami’in ya sake ƙoƙarin miƙa masa wayar, amma matashin ya fusata tare da bugun hannunsa.

Daga baya, matashin ya umarci jami’an ’yan sanda da na ƙungiyar sa-kai ta Vigilante Group of Nigeria (VGN) su bar wurin, kafin ya je wani wuri ya yi wa jama’a bayani.

An karɓi N4,200 daga matafiya

A cikin jawabin da ya yi wa jama’a, shugaban matasan ya ce sun samu labarin cewa jami’an tsaro na karɓar kuɗi daga masu ababen hawa a shingen.

Ya ce:

“Barkan ku da yamma, mutanena! Muna kan hanyar Auchi zuwa Aviele ne muka tarar da jami’an sa-kai da ’yan sanda sun kafa shingen bincike a nan.
"Mun samu labarin cewa suna karɓar kuɗi daga mutane, saboda haka muka yanke shawarar korarsu daga wurin. Mun gano cewa tuni sun karɓi N4,200 daga masu babura da wasu matafiya. Zan kai wannan kuɗin ga Kwamandan Yanki,” in ji shi.

Ya kuma yi kira ga kwamishinan ’yan sandan jihar da ya binciki jami’an da ke aiki a yankin.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: 'Yan bindiga sun nuna wa mata kusan 30 da karamin yaro rashin imani

Jihar edo.
Taswirar jihar Edo da ke Kudu maso Kudancin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan sanda sun kama matasa 14

Kun ji cewa ’yan sanda sun kama matasa 14 da ake zargi da kai hari kan ayarin magoya bayan APC a hanyar Yashe zuwa Funtua da ke jihar Katsina.

Rundunar yan sanda ta tura jami’an tsaro zuwa muhimman hanyoyi, ciki har da hanyar Yashe zuwa Funtua, domin tabbatar da tsaron magoya bayan ’yan siyasa da sauran masu amfani da hanyoyin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262