APC da Shugaba Tinubu Sun Fara Fargabar Haduwa da Atiku a Babban Zaben 2027"
- Tsohon gwamnan Edo, Oserheimen Osunbor ya ce alamu sun nuna APC na tsoron fuskantar ɗan takara mai ƙarfi a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Osunbor ya ce ADC za ta ɗaukaka ƙara kan hukuncin kotu da ya soke takarar tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar
- Ya bayyana kwarin gwiwar cewa Atiku zai shawo kan ƙalubalen shari’ar saboda goyon bayan da yake samu daga jama’a
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Edo, Nigeria - Tsohon gwamnan Jihar Edo kuma Mai Ba da Shawara kan Harkokin Shari’a na ADC, Oserheimen Osunbor, ya zargi jam’iyyar APC da fargabar fuskantar zaɓen shugaban ƙasa na 2027.
Jigon ADC ya ce alamu sun nuna APC tana tsoron dan takararta na shugaban kasa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kara dan takara mai karfi kamar Atiku Abubakar.

Source: Facebook
Ana zargin APC ta shiga fargaba
Da yake magana a shirin Politics Today na Channels Television ranar Alhamis, Osunbor ya ce APC ba ta son wani ɗan takara mai ƙarfi ya kalubalanci Shugaba Bola Tinubu a zaɓen.
“Na sha faɗin hakan, suna tsoron duk wani ɗan takara mai ƙarfi da zai fafata da Shugaba Bola Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na watan Janairu mai zuwa,” in ji Osunbor.
Mai ba da shawarar kan harkokin shari’a na ADC ya ce jam’iyyar da ɗan takararta na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, za su ci gaba da yaƙin neman zaɓensu saboda sun yi imanin cewa hukuncin kotun da ya soke takarar Atiku ba zai tabbata ba.
“Ɗan takararmu na shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, da kuma yaƙin neman zaɓenmu na ci gaba ba tare da wata tangarda ba, saboda mun yi imanin cewa wannan hukunci ba zai tabbata ba, kuma ba zai iya tabbata ba,” in ji shi.
Ya bayyana kwarin gwiwar cewa Atiku zai shawo kan ƙalubalen da yake fuskanta a yanzu, yana mai cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar na samun goyon bayan jama’a.
“Atiku zai tsira saboda jama’a suna tare da shi. Ƙarfin jama’a zai fi ƙarfin waɗanda ke son mayar da ’yan Najeriya bayi,” in ji shi.
Hukuncin da kotu ta yanke
Jawaban Osunbor sun biyo bayan hukuncin da Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke ranar Alhamis, inda ta cire shugabancin ADC ƙarƙashin Sanata David Mark tare da soke matakan da jam’iyyar ta ɗauka a lokacin wannan shugabanci.
Matakan da aka soke sun haɗa da tsarin da ya kai ga zaɓen Atiku a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027.

Source: Facebook
Mai Shari’a Peter Lifu ne ya yanke hukuncin a ƙarar da Nafiu Bala Gombe, tsohon Mataimakin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, ya shigar.
To sai dai Osunbor ya tabbatar da cewa jam’iyyar ADC za ta ɗaukaka ƙara zuwa gaba domin wata babbar kotu ta soke hukuncin.
Atiku ya yi fatali da hukuncin kotu
Kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, Atiku Abubakar, ya yi Allah-wadai da hukuncin kotu wanda ya rusa shugabancin Sanata David Mark.
Wazirin Adamawa kuma tsohon mataimakin shugaban kasa ya bayyana matakin a matsayin wani shiri na musamman domin raunana ADC da kawo cikas ga takararsa.
Asali: Legit.ng

