Dan Najeriya Ya Ladakawa Matarsa Duka a Ketare, Za a Fatattake Shi zuwa Gida
- Wani ɗan Najeriya mai shekaru 44 zai fuskanci korar sa daga Birtaniya bayan kammala zaman gidan yari saboda lakadawa matarsa duka
- An yanke masa hukuncin ɗaurin shekara ɗaya da watanni 11 bayan ya amsa laifin cin zarafin matarsa a lokacin rikicin aure
- Kotun ta kuma hana shi kusantar matar tasa na tsawon shekaru takwas, yayin da hukumomin Birtaniya ke shirin mayar da shi Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Birtaniya - Wani ɗan Najeriya mai suna John Onyejiaka, mai shekaru 44, ya shiga hannu bayan kotu ta same shi da laifin cin zarafin matarsa.
Onyejiaka ya samu hukuncin ɗaurin shekara ɗaya da watanni 11 bayan amsa laifin shake matarsa yayin wani rikicin aure a gidansu da ke Norton, Staffordshire.

Source: Facebook
Hukuncin da kotu ta yanke wa John
Kotun Crown da ke Stoke-on-Trent ce ta yanke masa hukuncin a ranar Talatar makon da ya gabata, tare da sanya masa takunkumin hana kusantar matar tasa, kamar rahoton Punch ya ce.
Jaridar The Sentinel ta ruwaito cewa za a mayar da mutumin Najeriya bayan ya kammala zaman gidan yarinsa, saboda takardar izinin zama a Birtaniya ta kare a watan Nuwambar bara.
Ma'auratan sun ƙaura zuwa Birtaniya ne a shekarar 2024, amma sun dade suna fuskantar matsaloli a zamantakewar aurensu.
Yawan sabani da ma'auratan ke samu tsakaninsu
A ranar 9 ga Janairu, 2026, sun samu saɓani, lamarin da ya sa matar ta bar gidan ta je wurin wata ƙawarta.
Bayan kwana biyu da dawowarta, Onyejiaka ya nemi ta shiga ɗakinta, sannan ya sanar da ita cewa ya gaji da auren kuma ba ya son ci gaba da zamantakewar.
Lauyar gwamnati, Emily Andrew, ta shaida wa kotu cewa matar ta amince da shawarar kawo ƙarshen auren a wannan karon saboda irin azaba da take sha, cewar Vanguard.
Ta ce hakan ya haifar da gardama, inda Onyejiaka ya fara dukan matar a fuska da kai, yana yi mata barazanar cewa:
"Zan kashe ki.”
Lauyar ta ƙara da cewa mutumin ya sa hannunsa a wuyan matar tare da matse shi, lamarin da ya hana ta numfashi kuma ta fara jin tashin zuciya.
Yadda matar ta tsira daga sharrinsa
Sai dai matar ta samu damar tserewa daga hannunsa, inda ta kira motar ɗaukar marasa lafiya domin samun agajin gaggawa.
Rahoton ya bayyana cewa abin da Onyejiaka ya aikata ya jefa matar cikin matsanancin tashin hankali da damuwa a zuciya.
An tura tsohon gwamna a Kenya gidan yari
Mun ba ku labarin cewa tsohon gwamnan jihar Migori a Kenya, Zacharia Okoth Obado, ya shiga gidan yari na tsawon shekaru 25 bisa zargin kisan kai.
An yanke wa Obado hukuncin ne tare da wasu tsofaffin hadimansa biyu, Michael Oyamo da Caspal Ojwang' Obiero da aka ce suna da hannu dumu-dumu a kisan.
Kotun ta tabbatar da cewa Obado ne ya sanar da dalilin aikata kisan tare da kudaden gudanar da shi wanda ya daga wa al'ummar yankin hankali.
Asali: Legit.ng

