Sanata Yari Ya Yi wa Yankin Tinubu Gori kan Kuri’u, Ya Bugi Kirki kan Arewa
- Daraktan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC, Abdulaziz Yari, ya yi alkawari cewa Arewa za ta ba Tinubu ƙuri’u
- Yari ya buƙaci al’ummar Ekiti su ƙara goyon bayan Tinubu, yana mai cewa APC na neman ƙuri’u 800,000 daga jihar a zaɓen 2027
- Tsohon gwamnan Zamfara ya lissafa ayyukan gwamnatin Tinubu a Ekiti, tare da ƙalubalantar jam’iyyun adawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Abdulaziz Yari, daraktan kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, ya bugi kirji kan tasirin Arewa a zabe.
Ya bayyana cewa Arewa za ta samar wa Shugaba Bola Tinubu ƙuri’u fiye da dukkan yankin Kudu maso Yamma a zaɓen 2027.

Source: Facebook
Yari ya bayyana hakan ne ranar Alhamis, 5 ga Nuwamba, yayin gangamin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC da aka gudanar a Ekiti, cewar TheCable.

Kara karanta wannan
Sanata Yari ya ɗauko da zafi, ya kutsa wata jiha domin ba Tinubu ɗaruruwan ƙuri'u
Ya yi kira ga al’ummar jihar da su mara wa Tinubu baya domin ya samu damar komawa kan mulki a karo na biyu.
Yari ya bayyana shirin Arewa kan zaɓen 2027
Tsohon gwamnan Zamfara ya ce al’ummar Arewa sun shirya tsaf domin tallafa wa Tinubu, yana mai cewa za su yi ƙoƙarin tabbatar da nasararsa a faɗin ƙasar.
A kalamansa, Yari ya ce Bola Tinubu ya taimaka wa mutanen Arewa wajen samun manyan mukamai a Najeriya har sau uku.
Ya bayyana cewa saboda wannan dalili ne yankin Arewa ke ganin ya dace ya mara wa shugaban ƙasar baya a zaɓe mai zuwa, cewar Punch.
Yari ya lissafa ayyukan gwamnatin Tinubu
Tsohon gwamnan ya ce APC na sa ran samun goyon bayan shugabannin siyasa da sauran al’ummar Ekiti bisa ayyukan da ya ce gwamnatin Tinubu ta gudanar tun bayan hawanta mulki.
Ya lissafa makarantu, jami’o’i, hanyoyi, tallafin karatu ga matasa da kuma shirye-shiryen ƙarfafa mata a matsayin wasu daga cikin ayyukan gwamnatin tarayya a jihar.
Yari ya kuma ƙalubalanci jam’iyyun adawa da su bayyana manufofin da za su aiwatar idan aka zaɓe su, tare da nuna yadda za su bambanta da na gwamnatin Tinubu.

Source: UGC
Ya kare manufofin tattalin arzikin Tinubu
Yayin kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin tarayya, Yari ya yi ikirarin cewa hauhawar farashi da tsadar abinci sun ragu.
Ya ce APC za ta yi yaƙin neman zaɓenta ne bisa alkaluman ayyukan da ta ce ta gudanar da kuma abubuwan da ta cimma wa ’yan Najeriya.
Yari ya bayyana cewa jam’iyyar na neman ƙarin dama daga al’ummar ƙasar domin ci gaba da aiwatar da shirinta.
Ya kuma ce APC a shirye take ta kare nasarorin da take ikirarin ta samu, yana mai cewa tana jiran jam’iyyun adawa su gabatar da nasu hanyoyin magance matsalolin ƙasar.
Sanata Yari ya nema wa Tinubu alfarma
An ji cewa Abdulaziz Yari ya bukaci al’ummar Ekiti su bai wa Shugaba Bola Tinubu kuri’u 800,000 a zaben shugaban kasa na 2027.
Tsohon gwamnan Zamfara ya ce Tinubu ya cancanci wa’adi na biyu saboda ayyukan da gwamnatinsa ta gudanar a Ekiti.
Yari ya bayyana cewa al’ummar Arewa za su goyi bayan Tinubu a 2027, yana mai cewa za su tabbatar masa da nasara.
Asali: Legit.ng
