"Nan ba da Dadewa ba Yan Najeriya Za Su Fara Murna da Tsare Tsaren Shugaba Tinubu"
- Gwamnan Kano ya ce nan ba da daɗewa ba ’yan Najeriya za su fara amfana da sauye-sauyen tattalin arzikin gwamnatin Tinubu
- Ya bayyana cewa matakan da gwamnatin ta ɗauka sun taimaka wajen daidaita tattalin arziki da darajar Naira
- Abba ya kuma buƙaci ’yan APC su haɗa kai domin tabbatar da nasarar ’yan takarar jam’iyyar a zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya buƙaci ’yan Najeriya su kara haƙuri da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Gwamna Abba ya yi ikirarin cewa nan ba da daɗewa ba yan ƙasar za su fara farin ciki saboda sun fara cin moriyar sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Tinubu ta aiwatar.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnan ya bayyana haka ne ta bakin tsohon mamban kwamitin gudanarwa na APC Muhammad Jamo Yusuf.
Abba ya kare matakan Tinubu
Abba ya fadi haka ne a wurin ƙaddamar da kwamitin kamfen shugaban ƙasa, gwamna, sanata, wakilan majalisar tarayya da na majalisar dokokin jihar na APC a ƙaramar hukumar Tarauni ta Kano.
Ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakai masu wuya amma sun zama wajibi domin daidaita tattalin arzikin ƙasar da kuma sanya ta a turbar ci gaba.
“Mutane da yawa ba su fahimci kyakkyawar manufar da Tinubu yake da ita ba. Idan aka duba manufofin tattalin arzikin gwamnatinsa, ya yi nasarar ceto tattalin arzikin ƙasar nan tare da daidaita abubuwa,” in ji shi.
A cewarsa, darajar Naira ta samu daidaito, lamarin da ya samar da yanayin da ’yan kasuwa da masu zuba jari za su iya hasashen yadda kasuwa za ta kasance.
Gwamna Abba ya ce za a ji dadi
Gwamna Abba Kabir ya ce a halin yanzu ƙasar na cikin wani yanayi da ake buƙatar ɗaukar matakai masu tsauri domin magance matsalolin tattalin arzikin da suka daɗe suna addabar Najeriya.
“Muna cikin wani lokaci da aka ɗauki matakai masu wuya domin ceto Najeriya. Muna kira ga ’yan Najeriya da su yi haƙuri da shugaban ƙasa da manufofin gwamnatinsa. A ƙarshe, dukkanmu za mu yi murna,” in ji shi.
Ya kuma yi kira ga mambobin jam’iyyar APC da su kasance cikin haɗin kai tare da yin aiki domin ganin ’yan takarar jam’iyyar a dukkan matakai sun yi nasara a zaɓuka masu zuwa, cewar rahoton Vanguard.

Source: Twitter
Gwamnan ya bayyana ’yan takarar APC da ke neman mukamai daban-daban a Kano a matsayin mutane masu ƙwarewa, waɗanda suka himmatu wajen samar wa al’umma ribar dimokuraɗiyya.
Abba ya nada sababbin kwamishinoni
Kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya zaɓi sababbin kwamishinoni biyu ciki har da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa.
Kakakin Majalisar dokokin Kano, Jibril Isma’il Falgore, ne ya sanar da hakan yayin zaman majalisar, bayan karanta wasiƙar da gwamnan ya aika domin neman amincewa da naɗin.
Ya ce majalisar za ta gudanar da aikin bisa tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Tarayyar Najeriya, wanda ya dora mata hakkin tantance waɗanda gwamna ya zaɓa domin muƙaman kwamishinoni.
Asali: Legit.ng

