Gwamna Abba Ya Yi Barazanar Korar Mukarraban Gwamnatinsa, an Ji Dalili
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi barazanar sallamar duk wanda aka samu yana karkatar da kayayyakin tallafi ko sayar da su
- Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila ya raba motoci 16, babura 400 da injinan ɗinki ga waɗanda suka ci gajiyar shirin ƙarfafa tattalin arziki a Kano ta Kudu
- Gwamnan ya kuma buƙaci ’yan APC su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a da shirye-shiryen jam’iyyar gabanin zaɓen 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kano - Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gargaɗi waɗanda aka naɗa kan muƙaman siyasa da jami’an jam’iyyar APC kan sayar da kayayyakin ƙarfafa tattalin arziki da aka raba wa al’umma.
Gwamna Abba ya yi barazanar sallamar duk wanda aka samu yana sayar da kayayyakin ko karkatar da su daga hannun waɗanda aka tanadar wa.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne a daren Litinin ta bakin shugaban APC na jihar, Umar Haruna Doguwa, yayin shirin ƙarfafa tattalin arziki karo na 12 da Sanata Abdurrahman Kawu Sumaila, mai wakiltar Kano ta Kudu, ya shirya, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar NDC ta yi barazana ga INEC kan cire sunan Aminu Gwarzo daga takara a Kano
Gwamna Abba ya yi barazanar kora
Abba Kabir Yusuf ya jaddada cewa an samar da kayayyakin ne domin inganta rayuwar al’umma, ba domin a sayar da su don amfanin kai ba.
"Duk wanda ya sayar da wannan tallafi, zai rasa muƙaminsa. Ni da kaina zan sallame shi. An bayar da kayayyakin ne domin jin daɗinku, ba domin sayarwa ba, musamman ga shugabannin jam’iyya.” In ji shi.
Gwamnan ya buƙaci waɗanda suka amfana da shirin su yi amfani da kayayyakin yadda ya kamata, domin bunƙasa ƙananan sana’o’i, samar da ayyukan yi da buɗe sabbin hanyoyin samun kuɗin shiga.
An raba motoci 16 da babura 400
A wajen shirin, an raba motoci 16 ga shugabannin APC na ƙananan hukumomi, yayin da aka bai wa shugabannin jam’iyyar a Kano ta Kudu babura 400.
Haka kuma, mutane 200 da ke sana’ar ɗinki sun amfana da kayan tallafi domin bunƙasa sana’o’insu.
An tanadar wa kowane mai cin gajiyar wannan ɓangare injinan ɗinki biyu na yau da kullum da kuma injin ɗinki guda ɗaya na masana’antu.
Ana sa ran tallafin zai taimaka wajen faɗaɗa sana’o’in waɗanda suka amfana, samar da ƙarin ayyukan yi da ba su damar koyar da wasu sana’ar.
Abba ya bukaci ’yan APC su shirya zaɓen 2027
Gwamnan ya kuma bayyana fatansa cewa APC za ta samu nasara a babban zaɓen shekarar 2027.
Ya buƙaci ’yan jam’iyyar su ci gaba da ƙoƙari wajen wayar da kan jama’a da gudanar da ayyukan haɗa kan mambobi domin cimma manufofinsu na siyasa.
“Muna fatan nasara za ta kasance tamu a babban zaɓen 2027, idan Allah Ya yarda. Mu ci gaba da aiki tuƙuru.” In ji shi

Source: Facebook
An yi wa Gwamna Abba barazana
A wani labarin kuma, kun ji cewa babbar kotun tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin tsare Sanusi Dankaka a gidan gyaran hali, kan zargin barazana ga Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano.
An bayar da umarnin ne bayan an gurfanar da shi kan zargin yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf, barazanar wallafa bidiyo da hotunansa na tsiraici a Facebook.
Asali: Legit.ng
