Wata Sabuwa: Shugaba Bola Tinubu Ya Rage Kasafin Kudin Shekarar 2026

Wata Sabuwa: Shugaba Bola Tinubu Ya Rage Kasafin Kudin Shekarar 2026

  • Shugaba Bola Tinubu ya aika da sabon ƙudirin kasafin kuɗin 2026 ga Majalisar Wakilai, inda ya rage kasafin da kaso mai dan tsoka
  • Duk da rage kasafin, Tinubu ya bar gibin kasafin kuɗin a kan Naira tiriliyan 31.46, wanda ya kai kashi 5.64 cikin 100 na GDP
  • Sabon kasafin ya tanadi kuɗin shiga na Naira tiriliyan 33.72 da kuma kashe Naira tiriliyan 26.23 kan ayyukan raya ƙasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya aika da ƙudirin doka ga Majalisar Wakilai domin soke tare da sake kafa dokar kasafin kuɗin 2026, inda ya nemi rage adadin kuɗin da aka amince da shi daga Naira tiriliyan 68.32 zuwa tiriliyan 65.18.

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wasiƙar da ya aikewa shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, mai ɗauke da kwanan watan 20 ga Nuwamba, 2026, wadda aka karanta yayin zaman majalisar ranar Talata.

Kara karanta wannan

Kotu ta rike wa Gwamnonin Najeriya $100m a banki saboda bashin Paris Club

Shugaba Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a majalisar wakilai. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa shugaban ya kuma aika da sabon tsarin kuɗin shiga da kashe-kashen gwamnatin tarayya, inda ya ce an yi sauye-sauyen ne domin daidaita kasafin da basussuka da sauran nauyin da ke kan gwamnati da kuma kuɗin da take da su.

Dalilin rage kasafi da Tinubu ya yi

A cewar wasiƙar, sabon tsarin na da nufin daidaita wasu kuɗin da Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) ya kashe a madadin tarayya.

Haka kuma, an yi tanadin biyan wasu basussukan gwamnati da ba a ware musu isassun kuɗi ba, tare da amincewa da wasu kuɗin ayyukan gine-gine da kuma alƙawuran ƙarin kudi.

Tinubu ya ce an kuma tanadi kuɗin mayarwa ga ma’aikatun gwamnati da hukumomi daban-daban da kuma wasu asusun musamman.

Ya bayyana cewa yawancin kuɗin ayyukan raya ƙasa da aka ware wa ma’aikatu sun riga sun samu izinin kashewa, yayin da aka ƙara wasu sababbin tanade-tanade domin muhimman ayyukan ƙasa.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Ana zargin wasu mutane sun shirya sace kwamishina da iyalinsa

N31.46tn za ta zama gibin kasafi

Sabon tsarin ya nuna cewa jimillar kuɗin da gwamnatin tarayya za ta kashe zai zama Naira tiriliyan 65.176, sabanin tiriliyan 68.323 da aka amince da su a baya.

Shugaba bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a wajen kamfen a Jigawa. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Gwamnati na sa ran samun kuɗin shiga har Naira tiriliyan 33.720, ciki har da kuɗin da kamfanonin gwamnati za su samar.

An ware Naira tiriliyan 26.232 domin ayyukan raya ƙasa, amma gibin kasafin kuɗin ya ci gaba da kasancewa a Naira tiriliyan 31.457, wanda ya yi daidai da kashi 5.64 cikin 100 na GDP.

Tinubu ya kuma bar shirin sabon rancen kuɗi a kan Naira tiriliyan 29.22, wanda ya ƙunshi rancen cikin gida na Naira tiriliyan 18.43 da kuma na ƙasashen waje na tiriliyan 10.79.

Ayyukan da gwamnati za ta yi

Shugaban ya bayyana cewa daga cikin abubuwan da aka ba fifiko akwai kammala muhimman ayyukan tituna, kare noman abinci da rage kuɗin da ake kashewa wajen samar da kayayyaki.

Kara karanta wannan

Ana shirin 2027, Tinubu zai raba tallafin Naira biliyan 45

Vanguard ta rahoto cewa sauran abubuwan sun haɗa da inganta amfanin gona, sauƙaƙa samun kasuwanni ga manoma da kuma ɗaukar matakan magance matsalolin ƙarancin ruwa.

Ya nemi haɗin kan ’yan majalisar domin su gaggauta nazari da amincewa da ƙudirin, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen aiwatar da kasafin cikin tsari da biyan basussukan da ake bin gwamnati.

ADC ta caccaki Bola Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar ADC ta buƙaci Shugaba Bola Tinubu ya yi murabus ko kuma Majalisar Tarayya ta tsige shi kan zargin katsalandan a hukuncin Kotun Ƙoli kan zaɓen gwamnan Kano na 2023.

Jam’iyyar ta yi zargin cewa Tinubu ya yi amfani da matsayinsa wajen samun hukuncin da ya amfanar da Gwamna Abba Kabir Yusuf domin ya sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

ADC ta ce hirar da Gwamna Yusuf ya yi da BBC Hausa ta tayar da tambayoyi kan ’yancin bangaren shari’a da kuma yiwuwar amfani da hukuncin kotu wajen cinikin siyasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng