An Yi Rashi a Arewa: Babban Basarake Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

An Yi Rashi a Arewa: Babban Basarake Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Sarkin gargajiya mai sarautar Balogun Gambari na Masarautar Ilorin, Alhaji Aliyu Adebayo Balogun, ya rasu a ranar Laraba, 25 ga Nuwamba, 2026
  • Sanata Saliu Mustapha ne ya sanar da rasuwar, inda ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai hikima da ya bayar da kumagudummawa
  • Mustapha ya mika sakon ta'aziyya ga Sarkin Ilorin, majalisar sarakunan masarautar, al'ummar Gambari da iyalan marigayin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ilorin, Kwara - Al'ummar Masarautar Ilorin sun shiga alhini sakamakon rasuwar Balogun Gambari na masarautar, Alhaji Aliyu Adebayo Balogun.

Sanata Saliu Mustapha, wanda ke wakiltar mazabar Kwara ta Tsakiya a Majalisar Dattawan Najeriya ya mika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayi.

Basarake ya rasu a Kwara
Taswirar jihar Kwara da wani mai sarauta ya yi bankwana da duniya. Hoto: Legit.
Source: Original

An sanar da mutuwar mai saurata a Kwara

Sanatan ya sanar da rasuwar marigayin a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafin X a ranar Laraba, 25 ga Nuwamba, 2026.

Kara karanta wannan

Bayan hallaka basarake a Niger, gwamnati ta yi magana bayan ɗaukar matakai

Mustapha, wanda ke rike da sarautar Turaki na Masarautar Ilorin, ya bayyana rasuwar Balogun Gambari a matsayin babban rashi ga masarautar da al'ummarta.

Ya ce marigayin ya kasance mutum mai hikima da kwarewa, wanda ya yi wa masarautar hidima tare da bayar da shawarwari masu amfani ga mutane da dama a lokacin rayuwarsa.

Mai sarauta ya rasu a Kwara
Marigayi Balogun Gambari na Masarautar Ilorin, Alhaji Aliyu Adebayo. Hoto: @RealMallamSaliu.
Source: Twitter

Sakon ta'aziyyar Sanata Saliu Mustapha

A cikin sakon ta'aziyyar, Sanata Mustapha ya mika sakon jaje ga Sarkin Ilorin, Mai Martaba Alhaji (Dr.) Ibrahim Sulu-Gambari, da majalisar sarakunan gargajiya ta masarautar.

Haka kuma, ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin, al'ummar Gambari da daukacin al'ummar Masarautar Ilorin bisa wannan babban rashi da suka yi.

Sanatan ya fara sakon nasa da addu'ar Musulunci kamar haka:

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un.
"Na samu labarin rasuwar Balogun Gambari na Masarautar Ilorin, Alhaji Aliyu Adebayo Balogun, cikin alhini da jimami.
"Rasuwarsa babban rashi ne ga Masarautar Ilorin, musamman ma fannin masarautar gargajiya da al’ummar da suka amfana da hikimarsa da hidimominsa.

Kara karanta wannan

Hadimin Atiku ya magantu kan Rarara, ya fadi yadda Tinubu ya zama masa ala ka kai

"Ina miƙa saƙon ta’aziyyata ga Mai Martaba Sarkin Ilorin, Alhaji (Dr.) Ibrahim Sulu-Gambari, CFR, da Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Masarautar Ilorin, iyalansa, al’ummar Gambari da daukacin al'ummar Masarautar Ilorin bisa wannan babban rashi."

Ya roki Allah SWT da ya gafarta wa marigayin kurakuransa, ya sanya shi cikin Aljannatul Firdaus, sannan ya ba iyalansa da sauran al'ummar masarautar hakurin jure wannan rashi.

Mambobinn APC 10 sun mutu a hatsarin mota

A wani labarin makamancin haka, mun ruwaito cewa fiye da mambobin jam'iyyar APC 10 sun mutu a wani mummunan hatsarin mota bayan kaddamar da yakin neman zaben gwamnan jam'iyyar a Talata-Mafara ta jihar Zamfara.

Rahotanni sun bayyana cewa wadanda hatsarin ya rutsa da su na kan hanyarsu ta komawa karamar hukumar Gummi ne lokacin da lamarin ya faru, inda wasu da dama suka samu raunuka.

Kwamishinan yada labarai na jihar Zamfara ya tabbatar da faruwar hatsarin tare da sanar da dakatar da wani gangamin yakin neman zabe domin nuna alhini ga wadanda suka rasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.