Abin Tausayi: Wata Babbar Mota Ta Bi Ta kan Uwa da Ƴarta a Abuja Za Su Tallaka Titi
- Wata mata mai suna Grace Titus da ’yarta, Sarah Titus, sun mutu bayan wata babbar mota ta murƙushe su a hanyar filin jirgin saman Abuja
- Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:47 na safe a Gosa-Toge, lokacin da suke ƙoƙarin tsallaka titi zuwa gonarsu domin girbin kayan noma
- Shugaban AMAC, Christopher Maikalangu, ya jajanta wa iyalan mamatan, inda ya bayyana rasuwarsu a matsayin babban rashi ga al'ummar yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Wata mata mai suna Grace Titus da ’yarta, Sarah Titus, sun rasa rayukansu bayan wata motar dakon kaya ta murƙushe su yayin da suke ƙoƙarin tsallaka babbar hanyar Lugbe zuwa filin jirgin saman Abuja.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 9:47 na safiyar Talata a unguwar Gosa-Toge da ke kan hanyar Airport, lokacin da mamatan ke ƙoƙarin tsallaka titi domin zuwa gonarsu girbin wake.

Kara karanta wannan
Atiku ya sake kifar da Tinubu, ya faɗi yadda zai dawo da tallafi, rage farashin fetur

Source: Original
Yadda lamarin ya faru a Abuja
Wani ganau ya bayyana cewa wata motar tipper da ke gudun wuce ƙima ce ta taka matar da ’yarta, inda suka mutu nan take, cewar Punch.
Wani jami’in hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa (FRSC), wanda ya shiga aikin ceto amma ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar da faruwar lamarin.
Jami’in ya ce an ɗauki gawarwakin mamatan zuwa ɗakin ajiye gawa na asibitin Garki da ke Abuja.
Kwamandan FRSC na babban birnin tarayya, Tijjani Iliyasu, shi ma ya tabbatar da aukuwar haɗarin, inda ya ce jami’an tsaro sun ƙwace motar tare da ajiye ta a ofishin ’yan sanda na Lugbe.

Source: Facebook
Martanin shugaban karamar hukumar AMAC
A nasa ɓangaren, shugaban ƙaramar hukumar Abuja Municipal Area Council (AMAC), Christopher Zakka Maikalangu, ya miƙa saƙon ta'aziyyarsa ga al'ummar Gosa-Toge bisa rasuwar matar da ’yarta.
A cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaransa, Kingsley Madaki, ya fitar ranar Talata, Maikalangu ya bayyana rasuwar a matsayin abin tausayi da ya jefa al'umma cikin jimami.
Shugaban ƙaramar hukumar ya tuna da gudummawar da marigayiya Sarah Titus ta bayar a lokacin yaƙin neman zaɓensa, inda ya bayyana ta a matsayin mai biyayya da jajircewa wajen wayar da kan jama'a kan manufofinsa na inganta AMAC.
Maikalangu ya miƙa ta'aziyyarsa ga mijin marigayiyar, iyalan Titus, abokai da maƙwabta, da kuma daukacin al'ummar Gosa-Toge.
Ya roƙi Allah Ya ba iyalan mamatan haƙurin jure wannan babban rashi, sannan Ya jikansu da rahama, cewar Daily Trust.
Yan APC sun yi hatsari a Zamfara
Mun ba ku labarin cewa mutum 15 da ke goyon bayan jam’iyyar APC a jihar Zamfara sun mutu a wani mummunan hatsarin mota yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa taron yaƙin neman zaɓe.
Masu goyon bayan jam’iyyar na tafiya ne daga Gummi zuwa Talata Mafara domin halartar ƙaddamar da gangamin zaɓe lokacin da hatsarin ya rutsa da su.
Saboda rasuwarsu, kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa da gwamnan APC a Zamfara ya ɗage gangamin da aka shirya gudanarwa a Maru.
Asali: Legit.ng
