2027: Ana So a Kwarfe Tinubu kamar Yadda aka Yi wa Jam'iyyar Trump

2027: Ana So a Kwarfe Tinubu kamar Yadda aka Yi wa Jam'iyyar Trump

  • Jam'iyyar ADC ta buƙaci 'yan Najeriya su yi koyi da Amurkawa da suka ƙi sake zaɓar jam'iyyar Republican a zaɓen tsakiyar wa'adi
  • ADC ta ce ya kamata masu zaɓe su yi amfani da katin zaɓensu wajen ƙin amincewa da APC saboda salon shugabancinta da manufofin tattalin arzikinta
  • Jam'iyyar ta bayyana cewa zaɓen 2027 dama ce ga 'yan Najeriya su zaɓi shugabancin da zai inganta rayuwarsu, samar da tsaro da ayyukan yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Jam'iyyar ADC ta buƙaci 'yan Najeriya su koyi darasi daga zaɓen tsakiyar wa'adi da aka gudanar a Amurka, inda masu zaɓe suka ƙi jam'iyyar Republican mai mulki.

Jam'iyyar ta yi kira ga 'yan Najeriya da su yi amfani da katin zaɓensu wajen ƙin zaɓar jam'iyyar APC a zaɓen 2027 saboda abin da ta kira gazawar shugabanci da manufofin tattalin arziki da ba su farin jini ba.

Kara karanta wannan

An fara maganar tsige Trump bayan Democrat ta karbi Majalisar Amurka

Bolaji Abdullahi da Bola Tinubu
Shugaba Bola Tinubu a hagu da Bolaji Abdullahi a dama. Hoto: Bayo Onanuga|ADC Vanguard
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da kakakin ADC, Bolaji Abdullahi, ya fitar a X, jam'iyyar ta ce sakamakon zaɓen Amurka ya nuna cewa babban iko a dimokuraɗiyya yana hannun talakawa masu zaɓe, ba shugaban ƙasa ko jam'iyyar da ke mulki ba.

ADC ta yabi Amurkawa

Jam'iyyar ta bayyana cewa zaɓen Amurka ya nuna cewa idan 'yan siyasa suka yi girman kai, manufofinsu suka ƙara wa talakawa wahala, kuma suka ɗauka cewa shahararsu za ta dawwama, katin zaɓe ne ke ba al'umma damar hukunta su.

Sanarwar ta ce:

"Masu zaɓe a Amurka sun fahimci abin da ya kamata 'yan Najeriya su ma su koya: Zaɓe ya shafi jin daɗin al'umma ne, ba son zuciya, biyayya ga jam'iyya ko bautar mutum ba. Babu wani shugaba da ya fi ƙarfin al'umma, kuma babu jam'iyyar da aka ba ikon mulki har abada."

ADC ta ƙara da cewa babu wani ɗan siyasa da ya isa ya ɗauka cewa yana da ikon mulki na dindindin, domin al'umma ce ke da ikon yanke hukunci ta hanyar zaɓe.

Kara karanta wannan

Iran ta yi magana kan zaben Amurka bayan Trump ya sha kaye

Jam'iyyar ta soki gwamnatin Tinubu

ADC ta bayyana cewa 'yan Najeriya sun shafe shekaru suna fuskantar matsin tattalin arziki, tabarbarewar tsaro da ƙarancin damar samun ayyukan yi a ƙarƙashin gwamnatin APC ta Shugaba Bola Tinubu.

Jam'iyyar ta ce duk da halin da jama'a ke ciki, ana son su sake ba APC damar ci gaba da mulki.

A cewar jam'iyyar:

"Ba za mu ci gaba da korafi kan tsadar rayuwa ba, sannan mu sake zaɓar shugaban da ya sa rayuwa ta yi tsada. Ba za mu nemi tsaro ba, amma mu saka wa gazawa. Ba za mu yi burin sauyi da gaske ba, sannan mu ci gaba da tallafa wa tsarin siyasar da ke haddasa talaucinmu."
Shugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump da aka kayar da jam'iyyarsa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Manufofin ADC a 2027

Sakataren yaɗa labaran jam'iyyar, Bolaji Abdullahi, ya ce shekarar 2027 na zuwa da babbar dama ga 'yan Najeriya su kawo sauyi ta hanyar zaɓe.

Daily Trust ta wallafa cewa ya buƙaci masu zaɓe su fito ƙwarai domin zaɓar abin da zai amfani rayuwarsu, maimakon su ɗauki katin zaɓe a matsayin abin tunawa da kasancewarsu 'yan ƙasa.

Kara karanta wannan

Democrat ta jero abubuwan da za ta bincika kan Trump bayan cin zabe

Abdul El-Sayed ya zama Sanata

A wani labarin, mun ruwaito cewa Abdul El-Sayed, ɗan jam'iyyar Democrat, ya lashe zaɓen sanatan Amurka a jihar Michigan bayan doke ɗan takarar jam'iyyar Republican, Mike Rogers.

Rahotanni sun nuna cewa nasarar Abdul El-Sayed ta sanya shi zama Musulmi na farko da aka zaɓa a matsayin sanata a tarihin Amurka.

Zaɓen nasa na daga cikin waɗanda suka fi ɗaukar hankali a zaɓen tsakiyar wa'adi na 2026, inda jam'iyyar Democrat ta samu rinjaye a majalisun dokokin Amurka biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng