An Fara Maganar Tsige Trump bayan Democrat Ta Karbi Majalisar Amurka

An Fara Maganar Tsige Trump bayan Democrat Ta Karbi Majalisar Amurka

  • Shugaban Amurka, Donald Trump, ya yi gargaɗin cewa yunƙurin da jam'iyyar Democrat za ta yi na tsige shi daga mulki zai jawo mata babbar asara a siyasa
  • Trump ya bayyana hakan ne bayan jam'iyyar Republican ta sha kaye a zaɓen tsakiyar wa'adin mulki, inda Democrat suka samu rinjaye a majalisa
  • Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya bayyana fatan cewa nasarar Democrat za ta ƙara wa ƙasarsa damar samun tallafin Amurka a yaƙin da take yi da Rasha

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Amurka – Shugaba Donald Trump ya yi martani kan yiwuwar jam'iyyar Democrat ta fara shirin tsige shi daga mulki bayan ta karɓe rinjaye a majalisun dokokin Amurka a zaɓen tsakiyar wa'adin mulki.

Trump ya bayyana cewa idan Democrat suka ɗauki matakin tsige shi bayan fara sabon zaman majalisa a watan Janairu, hakan zai iya jawo wa jam'iyyar babbar matsala a siyasa.

Kara karanta wannan

Iran ta yi magana kan zaben Amurka bayan Trump ya sha kaye

Shugaba Donald Trump
Donald Trump na magana da 'yan Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tashar Anadolu Agency ta ruwaito cewa Trump ya bayyana hakan ne ranar Laraba, kwana guda bayan jam'iyyar Republican ta sha kaye a zaɓen.

Trump ya yi gargaɗi kan tsige shi

Da aka tambaye shi game da yiwuwar Democrat za su nemi tsige shi bayan samun rinjaye a majalisa, Trump ya ce:

“Ina ganin hakan zai halaka jam'iyyar Democrat idan suka yi hakan.”

Shugaban Amurkan ya kuma jaddada cewa babu wani dalili da zai sa a tsige shi daga muƙaminsa.

Martanin nasa ya zo ne a daidai lokacin da Democrat ke shirin karɓar ikon majalisar dattawa da ta wakilai, lamarin da zai ba su damar gudanar da bincike kan gwamnatin Trump da kuma ƙalubalantar wasu daga cikin manufofinta.

Maganar Zelenskyy kan zaben Amurka

A wani rahoto na daban, Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy, ya bayyana fatan cewa nasarar jam'iyyar Democrat a zaɓen Amurka za ta taimaka wajen ƙara tallafin da ƙasarsa ke samu a yaƙin da take yi da Rasha.

Kara karanta wannan

Democrat ta jero abubuwan da za ta bincika kan Trump bayan cin zabe

TRT ta wallafa cewa Zelenskyy ya bayyana hakan ne a wata hira a ranar Laraba, inda ya ce sauyin iko a majalisun dokokin Amurka na iya amfani ga Ukraine.

Volodymyr Zelenskyy
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelenskyy. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ya ce yana godiya ga 'yan jam'iyyar Republican, amma Democrat sun fi bayyana matsayarsu karara kan goyon bayan Ukraine da samar mata da tallafi.

Zelenskyy ya ce Democrat sun kuma yi magana kan buƙatar farfaɗo da dangantakar Amurka da ƙasashen Turai.

Ya bayyana cewa hakan ya ba Ukraine fatan samun daidaito a tsarin siyasar Amurka da kuma ƙarin tallafin da take buƙata a yaƙin da take yi da Rasha.

Obama ya yi martani

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon Shugaban Amurka, Barack Obama, ya yi magana bayan jam'iyyar Democrat ta sake samun rinjaye a Majalisar Dattawan ƙasar.

Obama, mai shekaru 65, ya wallafa saƙo a kafar sada zumunta ranar Talata, 3 ga Nuwamba, inda ya yi tsokaci kan sakamakon zaɓen tsakiyar wa'adin na 2026.

Ya ce sakamakon zaɓen ya nuna cewa Amurkawa na son siyasar da za ta haɗa kan jama'a maimakon rarrabasu, da shugabannin da za su samar da mafita kan matsalolin da suke fuskanta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng