Iran Ta Yi Magana kan Zaben Amurka bayan Trump Ya Sha Kaye

Iran Ta Yi Magana kan Zaben Amurka bayan Trump Ya Sha Kaye

  • Kakakin majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Qalibaf, ya ce Amurkawa sun nuna rashin amincewarsu da yaƙi ta hanyar zaɓen da aka gudanar a ƙasar
  • Qalibaf ya bayyana cewa Iran na goyon bayan saƙon da jama'ar Amurka suka aika, bayan jam'iyyar Republican ta fuskanci koma baya a zaɓen tsakiyar wa'adi
  • Rahotanni sun nuna cewa wasu manyan jami'an Iran sun danganta rashin nasarar Republican da goyon bayan Amurka ga Isra'ila da yaƙin da take yi da Iran

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran – Gwamnatin Iran ta yi martani bayan jam'iyyar Republican ta Shugaba Donald Trump ta fuskanci koma baya a zaɓen tsakiyar wa'adin mulkin Amurka, inda ta bayyana cewa sakamakon ya nuna yadda jama'ar ƙasar suka ƙi yaƙi.

Kakakin majalisar dokokin Iran, Mohammad Bagher Qalibaf, ne ya bayyana hakan ranar Laraba a wani saƙo da ya fitar.

Kara karanta wannan

Democrat ta jero abubuwan da za ta bincika kan Trump bayan cin zabe

Mojtaba Khamenei da Donald Trump
Mojtaba Khamenei a hgu da Donald Trump a dama. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

A bayanin da ya yi a X, ya ce ko dai saboda lamirinsu ko kuma tsadar rayuwa, Amurkawa sun bayyana cewa ba sa son yaƙi, yana mai cewa Iran na goyon bayan wannan matsaya.

Ƙasar Iran ta yabi Amurkawa

Qalibaf ya ce idan gwamnatin Amurka ta yi watsi da muradin jama'arta domin biyan bukatun wasu ƙasashen waje da masu yi mata barazana, za ta fuskanci abin da ya kira mummunan sakamako.

A nasa ɓangaren, mataimakin kakakin majalisar dokokin Iran, Ali Nikzad, ya bayyana koma bayan Trump a zaɓen a matsayin sakamakon shan kaye da ya yi a fafatawar da yake yi da al'ummar Iran.

Da yake jawabi a gaban majalisa, Nikzad ya ce sakamakon zaɓen ya nuna gazawar ƙoƙarin Amurka na raunana Iran ta hanyar takunkumin tattalin arziki da matsin lamba.

Ya ƙara da cewa Trump, wanda ke ikirarin samun nasara ta hanyar saƙonnin da yake wallafawa a kafafen sada zumunta, ya kuma fuskanci koma baya a siyasar cikin gida.

Kara karanta wannan

An jika wa Netanyahu aiki a Isra'ila bayan kayar da Trump a zaben Amurka

Maganar Iran kan mashigar Hormuz

Nikzad ya kuma gargaɗi Amurka da kada ta ɗauki duk wani matakin soji a mashigar ruwan Hormuz, yana mai cewa Iran za ta mayar da martani mai tsanani idan aka yi hakan.

A wani martani na daban, mataimakin shugaban sashen sadarwa da yaɗa labarai na ofishin shugaban Iran, Seyed Mehdi Tabatabaei, ya ce sakamakon zaɓen Amurka ya ƙunshi saƙo mai ƙarfi daga masu zaɓen ƙasar.

Anadolu ta wallafa cewa ya danganta rashin nasarar jam'iyyar Republican da goyon bayan Amurka ga matakan Isra'ila a Gaza, da kuma yaƙin da take yi da Iran.

Hanyar Hormuz a Iran
Mashigar Hormuz da ke Iran. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tabatabaei ya ce abin da ya kira laifukan da ake aikatawa a Gaza, bin muradun Isra'ila da kuma yaƙin da ba ya ƙarewa da Iran sun janyo wa Republican babbar rashin nasara a tarihin zaɓen Amurka.

El-Sayed ya ci zabe a Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa ɗan jam'iyyar Democrat, Abdul El-Sayed, ya lashe muhimmiyar kujerar Sanata a jihar Michigan bayan doke ɗan takarar Republican, Mike Rogers.

Kara karanta wannan

Abdul El Sayed: Musulmi na farko ya lashe zaben sanata a Amurka

El-Sayed ya samu nasarar ne duk da hare-haren siyasa da aka kai masa, ciki har da zargin danganta shi da ta'addanci ba tare da hujja ba da kuma saɓanin da ya samu da wata 'yar jam'iyyarsa.

Nasarar da ya samu a zaben ta sanya shi zama Musulmi na farko a tarihin kasar Amurka da ya samu zaɓen kujerar Sanata a majalisar Amurka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng