Jigon PDP Ya Watsawa APC, Tinubu Ƙasa a Ido bayan Saka Shi a Kwamitin Kamfe

Jigon PDP Ya Watsawa APC, Tinubu Ƙasa a Ido bayan Saka Shi a Kwamitin Kamfe

  • Jigon PDP a Plateau, Aminu Zang, ya yi watsi da nadin da APC ta yi masa cikin kwamitin yakin neman zaben Tinubu da gwamnan jihar na 2027
  • Zang ya ce ba a tuntube shi ba kafin saka sunansa cikin jerin mambobin kwamitin, inda ya jaddada cewa shi cikakken dan PDP ne
  • Duk da goyon bayansa ga sake zaben Tinubu, Zang ya ce ba zai goyi bayan gwamnan APC ba, yana mai cewa PDP na da dan takararta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Jos, Plateau –Wani jigon jam’iyyar PDP a jihar Plateau, Hon. Aminu Zang, ya yi fatali da saka sunansa a kwamitin kamfen APC.

Dan siyasar ya yi watsi da nadin da aka yi masa cikin kwamitin yakin neman zaben APC na shekarar 2027 wanda ya ce ya saba da siyasarsa.

Kara karanta wannan

Atiku ya soki DSS, ya fadi makircin da aka shirya domin hana shi gangamin kamfe a Sokoto

Jigon PDP ya ki karbar mukami a kwamitin kamfen APC
Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Caleb Mutfwang. Hoto: Bayo Onanuga, Caleb Mutfwang.
Source: Twitter

Zang ya bayyana cewa har yanzu yana nan daram a jam’iyyar PDP, duk da cewa sunansa ya bayyana a matsayin na 254 cikin jerin mambobin kwamitin tsara ayyukan yakin neman zaben shugaban kasa da na gwamnan jihar, cewar Punch.

Zang ya ce ba a tuntube shi ba

A cikin wata sanarwa mai taken karin haske kan saka sunansa cikin kwamitin yakin neman zaben APC na 2027 a Plateau, Zang ya ce ba a tuntube shi ko sanar da shi kafin saka sunansa ba.

Ya ce duk da godiyarsa ga wadanda suka ga ya cancanci kasancewa cikin kwamitin, ba zai sauya matsayinsa na kasancewa cikakken dan PDP ba.

A kalamansa:

"Yayin da nake godiya ga wadanda suka ga na cancanci kasancewa cikin wannan muhimmin aiki, ina so in bayyana karara cewa har yanzu ni cikakken dan jam’iyyar PDP ne mai biyayya, kuma daga tafiyar Rainbow Coalition."

Da yake zantawa da wakilin Vanguard ta wayar tarho, Zang ya ce bai fusata da matakin ba, amma bai san dalilin saka sunansa cikin kwamitin ba.

Kara karanta wannan

'Sai mai tsoron Ubangiji': Gwamna ya ba da satar amsa ga magajinsa a zaɓen 2028

Ya kara da cewa ba zai yiwu ya kasance dan PDP sannan ya shiga kwamitin yakin neman zaben APC ba.

An saka dan PDP a kwamitin kamfen Tinubu, APC
Gwamna Caleb Mutfwang na jihar Plateau. Hoto: Caleb Mutfwang.
Source: Twitter

Zang ya bayyana matsayarsa kan Tinubu, Mutfwang

Da aka tambaye shi matsayarsa kan zaben 2027, Zang ya bayyana cewa yana goyon bayan ra’ayin Nyesom Wike na ganin Shugaba Bola Tinubu ya sake lashe zabe.

Sai dai ya ce ba zai goyi bayan dan takarar gwamnan APC ba, Caleb Mutfwang saboda kasancewarsa dan PDP.

Ya kuma bayyana cewa jam’iyyar PDP tana da dan takararta na gwamna, wato Cif Kefas Wungak Ropshik.

Zang ya ce har yanzu PDP ba ta kafa nata kwamitin yakin neman zabe ba, amma ana kan shirye-shiryen kafa shi.

Ya yi kira da a tabbatar da zaman lafiya

A cikin sanarwar tasa, Zang ya bukaci masu ruwa da tsaki a harkokin siyasa, mambobin jam’iyyu da magoya baya da su rungumi zaman lafiya da hakuri yayin tunkarar babban zaben 2027.

Ya ce ya kamata a gudanar da harkokin zabe cikin dattako, mutunta juna da kuma nuna kishin kasa.

Kara karanta wannan

Gwamnan APC ya fallasa danyen aikin da Buhari ya yi da ya bar Tinubu da wahala

Haka kuma, ya bukaci daukacin masu ruwa da tsaki da su nemi taimako da shiriyar Allah domin tabbatar da gudanar da zabe cikin lumana.

Kamfen Tinubu: An samu karancin jiragen sama

An ji cewa shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce ’yan siyasar da ke shirin yakin neman zaben 2027 na fuskantar karancin jiragen haya.

Akpabio ya bayyana cewa kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu ba sa iya biyan bukatar zirga-zirgar fasinjoji.

Ya bukaci gwamnatin tarayya ta dauki matakan farfado da harkokin sufurin jiragen sama tare da samar da kamfanin jirgin sama na kasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.