An Kama Masoyin El Rufai Bayan Ba'a kan Ƙarancin Mutane a Kamfen Tinubu

An Kama Masoyin El Rufai Bayan Ba'a kan Ƙarancin Mutane a Kamfen Tinubu

  • Amnesty International ta bukaci gwamnatin Najeriya ta saki Imran Usman Wakili ba tare da wani sharadi ba bayan tsare shi kan sukar APC
  • Kungiyar ta ce an kama Wakili ne saboda goyon bayansa ga tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da kalaman da ya wallafa a kafafen sada zumunta
  • Amnesty ta yi zargin cewa an hana wanda ake tsare da shi ganawa da iyalansa da lauyansa, lamarin da ta ce ya saba wa dokokin kare hakkin dan Adam

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna – Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bukaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta sakin Imran Usman Wakili, wani magoyin bayan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, da ake tsare da shi.

Kungiyar ta ce an kama Wakili ne saboda wasu sakonnin da ya wallafa a kafafen sada zumunta, inda ya soki karancin mutanen da suka halarci kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam'iyyar APC a Kaduna.

Kara karanta wannan

Mutane 17 da ƴan bindiga suka sace a wurin ibada sun rasa rayukansu

An kama matashi da ya soki Tinubu
Imran Usman Wakili da jami'an DSS suka cafke a Kaduna. Hoto: Imran Usman Wakili, DSS Unofficial.
Source: Facebook

Amnesty International ta bayyana hakan ne a wani sako da ta wallafa a shafinta na X ranar Talata, 3 ga watan Nuwamban 2026.

Amnesty ta bayyana dalilin kama Wakili

Kungiyar ta yi zargin cewa hukumomin tsaro sun kama Wakili ne saboda ra'ayoyinsa kan harkokin siyasa da kuma goyon bayan da yake bai wa El-Rufai.

A cewar Amnesty, jami'an tsaro sun gano inda Wakili yake zaune a wani katafaren gidaje da ke Karu, a wajen birnin Abuja, inda suka kai samame ranar 29 ga watan Oktoba.

Ta ce tawagar 'yan sanda dauke da makamai sosai ta isa wurin da misalin karfe 4:30 na yamma, inda suka bukaci jami'an tsaron gidan su nuna musu dakinsa.

Kungiyar ta kara da cewa bayan jami'an sun gano cewa Wakili ba ya gida, sai suka kama kaninsa wanda suke zaune tare da shi, da kuma manajan gidan.

Ana zargin cafke matashi da ya soki Tinubu
Shugaba Bola Tinubu na Najeriya. Hoto: Dada Olusegun.
Source: Facebook

An hana shi ganawa da iyalansa da lauya

Kara karanta wannan

Da gaske an ɗaure mace kirista saboda ta sa musulmi ya yi ridda? An samu bayani

Amnesty International ta bayyana cewa akwai barazanar yi wa Wakili mummunan cin zarafi, musamman saboda zargin hana shi ganawa da iyalansa da kuma lauyansa.

Ta ce tsare shi ba tare da bin ka'idojin shari'a ba ya saba wa hakkinsa na fadin albarkacin baki da sauran dokokin kare hakkin dan Adam.

Kungiyar ta ce wallafa ra'ayi a kafafen sada zumunta kan batutuwan da suka shafi jama'a hakki ne na kowane dan kasa, kuma bai kamata a hukunta mutum saboda hakan ba.

"Tsare Imran Wakili kawai saboda amfani da hakkinsa na fadin albarkacin baki abu ne da ba za a amince da shi ba, kuma yana nuna rashin mutunta bin doka da oda."

in ji kungiyar.

Amnesty ta yi magana kan tsare El-Rufai

Kungiyar ta kuma yi ikirarin cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, ya shafe sama da kwanaki 260 a tsare ba bisa ka'ida ba.

Ta bayyana cewa dokokin kasa da kasa kan kare hakkin dan Adam ba su amince da tsare mutum ba bisa hujjar cewa jami'an gwamnati ko wasu masu fada a ji ba su ji dadin sakonnin da ya wallafa a kafafen sada zumunta ba.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ba da mamaki, ya dauki alkawari shiga dazuka da afafunsa

Amnesty International ta bukaci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta kawo karshen abin da ta kira hare-hare kan 'yancin dan Adam tare da tabbatar da sakin Wakili nan take ba tare da wani sharadi ba.

Maulidi: Amnesty ta soki yan sanda

A baya, an ruwaito cewa kungiyar kare haƙƙin bil’adama ta Amnesty International ta buƙaci hukumomin Najeriya su gudanar da bincike kan kisan wani matashi.

An kashe matashin mai suna Umar Muhammad, wanda aka fi sani da Gajiye, a wani taron Maulidi da aka gudanar a Banki, ƙaramar hukumar Bama ta jihar Borno.

Amnesty ta ce ya kamata a gudanar da bincike cikin gaggawa tare da tabbatar da cewa duk jami’an ’yan sandan da ke da hannu a kisan sun fuskanci shari’a ta gaskiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.