An Fara Ƙarancin Samun Jiragen Sama saboda Kamfen Tinubu a Najeriya
- Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce ’yan siyasar da ke shirin yakin neman zaben 2027 na fuskantar karancin jiragen haya
- Akpabio ya bayyana cewa kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu ba sa iya biyan bukatar zirga-zirgar fasinjoji
- Ya bukaci gwamnatin tarayya ta dauki matakan farfado da harkokin sufurin jiragen sama tare da samar da kamfanin jirgin sama na kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa shi da sauran ’yan siyasar kasar na fuskantar matsala wajen samun jiragen haya da za su rika amfani da su yayin yakin neman zaben 2027.
Akpabio ya danganta matsalar da karancin jiragen sama da kuma gazawar kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu wajen biyan bukatar fasinjoji a Najeriya.

Kara karanta wannan
Atiku ya soki DSS, ya fadi makircin da aka shirya domin hana shi gangamin kamfe a Sokoto

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisar dattawa ranar Talata, lokacin da sanatoci ke tattauna kudirin tabbatar da yarjejeniyar zirga-zirgar jiragen sama tsakanin Najeriya da China, cewar Vanguard.
Sanata Tahir Monguno mai wakiltar Borno ta Arewa ne ya gabatar da kudirin, inda ya bukaci gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta sake duba yarjejeniyar domin bai wa kamfanonin jiragen saman Najeriya damar gudanar da zirga-zirgar kai tsaye zuwa China.
Akpabio ya koka kan karancin jiragen haya
Da yake bayyana matsin lambar da bangaren sufurin jiragen sama ke fuskanta, Akpabio ya yi amfani da watan Disamba a matsayin misali, inda ya ce bukatar zirga-zirgar jiragen sama kan karu sosai a lokacin bukukuwan karshen shekara.
Ya ce hatta kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu ba sa iya biyan bukatar jama'a, lamarin da ya shafi shirye-shiryen yakin neman zaben ’yan siyasa.
A kalamansa:
“Ku jira watan Disamba ku ga yadda za a samu cunkoso da rudani. Hatta kamfanonin jiragen sama masu zaman kansu ba za su iya biyan bukatar ba. A yakin neman zabe ma, muna kasa samun jiragen haya.

Kara karanta wannan
Ciyaman ya sha da ƙyar da miyagun yan daba suka farmaki wurin zaɓen fitar da gwanin APC
Ya kamata mu bukaci gwamnatin tarayya ta duba wannan matsala domin rage wa kamfanonin jiragen sama wahala.”

Source: Facebook
Akpabio ya tuna da kamfanin Nigerian Airways
Shugaban majalisar dattawan ya kuma tuna lokacin da Najeriya take da kamfanin jirgin sama na kasa, wato Nigerian Airways, wanda ke jigilar alhazai daga Najeriya zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin Hajji.
Ya ce a wancan lokacin kamfanin yana da jirage tsakanin 32 zuwa 40, wadanda ke gudanar da zirga-zirga zuwa wurare daban-daban.
Akpabio ya tambayi yadda harkokin sufurin jiragen saman kasar suka tabarbare har aka kai ga halin da ake ciki yanzu.
Ya jaddada bukatar Najeriya ta samar da kamfanin jirgin sama na kasa wanda zai rika daga tutar kasar a harkokin zirga-zirgar jiragen sama.
Hayar jirage: Yadda ’yan siyasa ke kashe makudan kudi
Amfani da jiragen sama masu zaman kansu ya zama ruwan dare tsakanin ’yan siyasar Najeriya da manyan jami'an gwamnati, musamman a lokutan yakin neman zabe da tafiye-tafiyen aiki.
A lokacin zabuka, musamman na shugaban kasa, ’yan takara da jam'iyyun siyasa kan kashe miliyoyin nairori wajen hayar jirage domin kai ziyara jihohi daban-daban da halartar tarukan yakin neman zabe.
Rahotannin yanar gizo sun kiyasta cewa hayar jirgin sama mai zaman kansa a Najeriya na iya kaiwa dala 5,000 zuwa dala 7,000, kwatankwacin kusan Naira miliyan 6.6 zuwa Naira miliyan 9.3 a kowace sa'a
Osun: APC ta sake cire sunayen kamfen Tinubu
Mun ba ku labarin cewa jam’iyyar APC a Osun ta kafa kwamitin mutum 168 domin yaƙin neman zaɓen sake zaɓen Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Matakin ya biyo bayan kafa kwamitin mutum 344 da Gwamna Ademola Adeleke ya yi ba tare da manyan shugabannin APC ba.
APC ta ce ba za ta amince da goyon bayan Tinubu kaɗai ba, tana son Adeleke ya goyi bayan dukkan ’yan takararta.
Asali: Legit.ng
