'Sai Mai Tsoron Ubangiji': Gwamna Ya ba da Satar Amsa ga Magajinsa a Zaɓen 2028

'Sai Mai Tsoron Ubangiji': Gwamna Ya ba da Satar Amsa ga Magajinsa a Zaɓen 2028

  • Gwamna Diri ya shawarci masu sha'awar maye gurbinsa a zaben gwamnan Bayelsa da su nemi yardar Ubangiji ta hanyar addu'a
  • Ya ce duk wanda Ubangiji ya zaba domin jagorantar jihar ba wanda zai iya hana shi samun mulkin
  • Fasto Joseph Opelema ya bukaci Kiristoci su hada ibadarsu da sauke nauyin da ke kansu a matsayin 'yan kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yenagoa, Bayelsa – Gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, ya ba masu neman gadon kujerarsa ta gwamna shawarar abin da ya ke bukata.

Diri ya bukaci duk masu sha'awar maye gurbinsa a kujerar gwamna da su nemi yardar Ubangiji ta hanyar addu'a, yana mai cewa dole ne wanda zai jagoranci jihar ya kasance mai tsoron Allah.

Gwamna ya fara maganar mai gadon kujerarsa
Gwamna Douye Diri na jihar Bayelsa a gidan gwamnati. Hoto: Douye Diri.
Source: Facebook

Diri ya bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin bikin godiya ga Ubangiji karo na 15 na jihar, wanda aka gudanar a cibiyar Ecumenical da ke Igbogene, Yenagoa, cewar Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamna Bala ya yi ta'aziyyar shugaban karamar hukumar da ya rasu a Bauchi

Gwamnan ya bayyana cewa an mika jihar Bayelsa ga Ubangiji, yana mai cewa babu wanda zai iya hana duk wanda Allah ya zaba jagorantar jihar.

Ya kara da cewa Ubangiji Madaukakin Sarki ne kadai ke da ikon karshe kan al'amuran jihar.

Diri ya bukaci zaman lafiya da hadin kai

Gwamnan ya kuma bukaci al'ummar jihar su ci gaba da zama cikin hadin kai, hakuri da zaman lafiya, yana mai bayyana wadannan abubuwa a matsayin muhimman sharuddan samun ci gaba.

Ya tabbatar da cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kokarin inganta rayuwar al'ummar jihar, yana mai cewa tana da karfin siyasar da ake bukata domin kawo sauyi a Bayelsa.

Diri ya bayyana jihar a matsayin daya daga cikin wuraren da suka fi dacewa da bunkasa ci gaba a Najeriya.

Gwamna ya magantu kan magajinsa a 2028
Taswirar jihar Bayelsa da APC ke mulki karkashin jagorancin Douye Diri. Hoto: Legit.
Source: Original

Godiya ta musamman ga al'ummar Bayelsa

Ya gode wa al'ummar jihar bisa goyon bayan da suka ba gwamnatinsa cikin shekaru shida, tare da bukatarsu da su ci gaba da ba shi hadin kai, cewar Punch.

Kara karanta wannan

Abubuwan da Tinubu ya fada kan zabe bayan shiga dakin Ka'aba a Saudi

A kalamansa:

"Ku da kuke son zama gwamna, ku je ku nemi yardar Ubangiji. Duk wanda yake son zama gwamna dole ne ya kasance mai tsoron Ubangiji. Idan Ubangiji ya ce eh, babu wanda zai iya cewa a'a, har da ni.
"Mu ci gaba da bautar Ubangiji. Mu kasance masu hakuri da juriya, domin a karshe za mu yi nasara."

Gwamnan ya ce mutanen da aka haifa a Yenagoa ko kuma suka san yadda Bayelsa take a baya za su iya ganin irin sauye-sauyen da aka samu a jihar.

Ya ce hakan kadai ya isa su gode wa Ubangiji, yana mai jaddada cewa da kyakkyawar niyya da karfin siyasa za a iya kawo ci gaba ga al'umma.

Gwamna ya fadi dalilin barin PDP

A wani labarin, mun ba labarin cewa gwamnan Bayelsa, Douye Diri ya ce ya dauki matakin barin PDP ne saboda maslahar al'ummar jiharsa amma ba kowa zai fahimta ba.

Kara karanta wannan

"Ba sabon alkawari ba"; Gwamna Radda ya fadi abin da yake kamfen da shi

Ana sa ran Gwamna Diri zai shiga jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya a ranar Litinin, 3 ga watan Nuwamba, 2025.

ai girma gwamnan ya shawarci yan siyasa su gujewa gaba a tsakaninsu, su maida hankali wajen inganta rayuwar al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.