Munyi Nadamar Goyon Bayan Buhari, Muna Roƙon Allah Ya Yafe Mana, Tsohon Gwamna

Munyi Nadamar Goyon Bayan Buhari, Muna Roƙon Allah Ya Yafe Mana, Tsohon Gwamna

  • Olagunsoye Oyinlola, tsohon gwamnan jihar Osun ya ce ya yi nadamar marawa Shugaba Buhari baya
  • Tsohon gwamnan ya ce sun yi wa mutane alƙawura da yawa yayin kamfen amma ko guda Buhari bai cika ba
  • Tsohon gwamnan ya ce a halin yanzu Allah suke roko ya yafe musu abin da suka yi don ganin Buhari ya hau mulki

Tsohon gwamnan jihar Osun Olagunsoye Oyinlola, ya soki gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari kan rashin magance matsalar tsaro, Premium Times ta ruwaito.

Mr Oyinlola ya yi gwamna a Osun daga 2003 zuwa 2010 a karkashin jam'iyyar PDP. Ya koma jam'iyyar APC jim kadan kafin zaben gwamna na 2014 a jihar.

Munyi Nadamar Goyon Bayan Buhari, Muna Roƙon Allah Ya Yafe Mana, Tsohon Gwamna
Tsohon Gwamnan Jihar Osun, Olagunsoye Oyinlola. Hoto: Premium Times
Asali: Facebook

KU KARANTA: Da Ɗuminsa: Ƴan Bindiga Sun Harbe Janar Ɗin Sojan Nigeria Har Lahira, Sun Sace Matarsa

Yana ɗaya daga cikin wadanda suka yi wa Shugaba Buhari kamfen gabanin babban zaben 2015.

Kara karanta wannan

Kano Za Ta Iya Gogayya Da Takwarorinta a Faɗin Duniya Saboda Jajircewar Ganduje, Buhari

A hirar da BBC Yoruba ta yi da shi a ranar Alhamis, Mr Oyinlola ya ce wadanda suka marawa Buhari baya tuni sun fara neman gafara daga Allah.

Tsohon gwamnan ya ce:

"Na taka rawar gani don ganin Buhari ya zama shugaban ƙasa. Mun yi wa ƴan Nigeria alƙawura masu yawa kuma har yanzu bamu cika ko ɗaya ba. Ɗaya daga cikinsu shine tsaro. Muna tunanin saboda Buhari tsohon shugaban mulkin soja ne zai kawar da Boko Haram cikin watanni shida amma babu abin da ya canja.
"Obasanjo ya faɗa mana ya san Buhari kuma gamsu zai iya jagorancin Nigeria da kyau ba. Amma muna tunanin saboda shi tsohon shugaban ƙasa na mulkin soja ne, zai iya magance matsalar tsaro. Tun bayan samun ƴanci, da yaƙin basasa, ba a taɓa shiga lokaci mai firgitarwa irin yanzu ba.
"Labarin da muke gani a jaridu kullum shine kisa da sace mutane. Iyaye a yanzu ba su da ra'ayin tura ƴaƴansu makaranta. Tun 1999, ba a taɓa samun tabarbarewar tsaro irin yanzu ba."

Kara karanta wannan

Hukumar Sojoji ta saki yan ta'addan Boko Haram 1009, ta mikasu ga gwamnatin Borno

Mr Oyinlola wanda ya dawo PDP ya kuma bukaci a sake fasalin mulkin ƙasar yana mai cewa Buhari yana abu kamar bai san alƙawurran da ya ɗauka wa mutane a 2015 ba.

KU KARANTA: Hoton Yadda Aka Yi Jana'izar Janar Na Sojan Nigeria Da Ƴan Bindiga Suka Kashe

Premium Times ta yi kokarin tuntubar kakakin Buhari, Femi Adesina, domin jin martaninsa amma bai amsa kira da sakon kar ta kwana ba.

Nigeria tana fama da ƙallubalen tsaro a shekarun baya-bayan nan da suka hada da rikicin makiyaya da manoma, ƴan bindiga, yan ta'adda da sauransu.

Kungiyoyi da dama na kira ga Shugaban Kasa ya sauya tsarin mulkin ƙasar amma kawo yanzu bai ɗauki wani mataki a kai ba.

Rashin daukan matakin ya karfafa masu neman ɓallewa daga Nigeria suka ƙara harzuƙa suna neman kafa Biafra da Kasar Yarbawa.

Sai dai tsohon gwamnan Legas, Bola Tinubu, da kakakin majalisar wakilan tarayya, Femi Gbajabiamila da Bisi Akande da shugabannin APC a Kudu maso Yamma sun soki hakan.

Kara karanta wannan

Ina Jin Irin Raɗaɗin da Kuke Ji, Gwamna Ya Lallashi Mutanen Jiharsa

Sun bukaci a haɗa kai a gina ƙasa a ajiye batun kabilanci da addini a gefe

Kano Za Ta Iya Gogayya Da Takwarorinta a Faɗin Duniya Saboda Jajircewar Ganduje, Buhari

A wani labarin, Shugaba Muhammadu Buhari, a ranar Alhamis ya ce jihar Kano za ta iya gogayya da takwarorinta a duniya saboda jajircewa irin na gwamnan jihar, Dr Abdullahi Umar Ganduje, The Punch ta ruwaito.

Ya umurci gwamnonin jihohi su rika koyi da al'adar cigaba daga inda magabantansu suka tsaya domin ciyar da jihohinsu da kasa gaba.

A cewar The Punch, Buhari ya yi wannan yabon ne a lokacin da ya ziyarci Sarkin Kano, Aminu Ado-Bayero, jim kadan bayan kaddamar da aikin shimfida layin dogo na Kano zuwa Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164