Duk da Zargin Barazana, Atiku Zai Kaddamar da Yakin Neman Zabensa a Sokoto

Duk da Zargin Barazana, Atiku Zai Kaddamar da Yakin Neman Zabensa a Sokoto

  • Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, zai isa filin jirgin saman Sultan Abubakar III da ke Sokoto da ƙarfe 9:00 na safe.
  • Jam’iyyar ADC za ta yi amfani da ziyarar wajen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa a sakatariyarta da ke lamba 1, Ilorin Road, Sokoto
  • Sanata Ibrahim Lamido ya umarci shugabannin ƙananan hukumomi da na mazabu su tattara mambobi da magoya baya domin tarbar Atiku da halartar taron

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Sokoto - Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), zai kai ziyara jihar Sokoto ranar Laraba, 4 ga Nuwamba, 2026.

Ziyarar za ta kasance wani ɓangare na shirye-shiryen jam’iyyar na ƙarfafa goyon bayan jama’a da ƙaddamar da ayyukan yaƙin neman zaɓenta a jihar gabanin babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

ADC na neman darewa saboda takarar Atiku a 2027? An ji yadda zancen yake

Atiku zai yi kamfen a Sokoto
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taron jam'iyyar ADC Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Ana sa ran Atiku zai isa filin jirgin saman Sultan Abubakar III da ke Sokoto da ƙarfe 9:00 na safe, inda magoya bayan jam’iyyar, abokan siyasarsa da sauran al’umma za su tarbe shi, cewar rahoton jaridar Vanguard.

ADC ta bayyana dalilin ziyarar Atiku

Mai kula da kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na ADC a jihar Sokoto, Sanata Ibrahim Lamido, ne ya bayyana shirin ziyarar cikin wata sanarwa da aka rabawa ’yan jarida.

A cewar sanarwar, ziyarar na daga cikin ƙoƙarin jam’iyyar na ƙarfafa tushenta a matakin ƙasa da kuma haɗa kan magoya baya domin samun goyon baya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Sanarwar ta yi kira ga mambobin ADC, magoya bayanta da sauran mazauna jihar da ke son ci gaban siyasa da su fito da yawa domin tarbar ɗan takarar shugaban ƙasar, jaridar The Punch ta kawo labarin.

Za a ƙaddamar da kamfen a sakatariyar ADC

Kara karanta wannan

El Rufai ya aiko sako ga masoya da magoya baya kan 'yan takarar da za su zaba a 2027

Sanarwar ta ce bayan tarbar Atiku, za a gudanar da bikin ƙaddamar da ayyukan yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam’iyyar a jihar Sokoto.

Za a gudanar da taron ne a sakatariyar ADC da ke lamba 1, kan titin Ilorin Road, a cikin birnin Sokoto.

Ana sa ran manyan shugabannin jam’iyyar, zaɓaɓɓun jami’an gwamnati, waɗanda aka naɗa muƙamai, shugabannin ƙananan hukumomi da na mazabu za su halarci taron.

Haka kuma, ana sa ran masu kula da harkokin wayar da kan jama’a, ƙungiyoyin goyon baya da sauran masu ruwa da tsaki za su kasance cikin mahalarta taron.

An ba shugabannin ADC umarni

Sanata Lamido ya ce an umarci shugabannin jam’iyyar na ƙananan hukumomi da mazabu da su farfaɗo da tsarin siyasarsu, tare da tattara mambobi da magoya baya a faɗin jihar.

An kuma buƙaci ƙungiyoyin mata da matasa, da sauran ƙungiyoyin da ke goyon bayan ADC, da su ƙara ƙaimi wajen wayar da kan jama’a da halartar taron.

Kwamitin yaƙin neman zaɓen ya kuma yi kira ga masu kula da tattara magoya baya da su tabbatar da kyakkyawan haɗin gwiwa tsakanin sassan jam’iyyar.

Kara karanta wannan

An fara batun Tinubu ya je Umrah ne don neman kuri'un 'yan Arewa, hadiminsa ya magantu

Ya ce hakan zai taimaka wajen tabbatar da nasarar tarbar Atiku da kuma bikin ƙaddamar da yaƙin neman zaɓen.

Ziyarar Atiku na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyun siyasa ke ƙara shirye-shirye da sauya dabaru domin faɗaɗa sansanoninsu gabanin babban zaɓen 2027.

Sai dai sanarwar ba ta bayyana wasu ƙarin bayanai kan sauran ayyukan da Atiku zai gudanar yayin ziyararsa ta jihar Sokoto ba.

Atiku zai yi yakin neman zabe a Sokoto
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taro Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Atiku ya yi zargi kan DSS

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar shugaban kasa na ADC, Alhaji Atiku Abubakar, ya zargi kan shugabannin Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS)

Atiku Abubakar ya zarge su da daukar nauyin wasu masu zanga-zanga domin kawo cikas ga kaddamar da kamfen da zai yi a Sokoto.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng