Baturiyar da Ta Saki Bidiyon Sarkin Daura na Fuskantar Barazanar Kisa
- Amnesty ta yi Allah wadai da barazanar kisa da ake yi wa wata ’yar yawon buɗe ido ’yar Poland bayan zargin cin zarafinta da ta yi wa Sarkin Daura
- Mirka Czee ta wallafa sakonnin barazana da cin mutunci da ta ce take samu tun bayan da ta fito ta yi magana kan lamarin
- Kungiyar ta bukaci rundunar ’yan sandan Najeriya ta kare ta tare da gudanar da bincike na gaskiya da adalci kan zargin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta yi Allah wadai da barazanar kisa da ake yi wa wata ’yar yawon buɗe ido ’yar Poland, Mirka Czee, bayan zargin cin zarafinta da ta yi wa Sarkin Daura, Alhaji Faruk Umar Faruk.
Kungiyar ta bayyana cewa Czee ta fuskanci daruruwan sakonnin barazanar kisa, inda wasu suka yi barazanar bin diddiginta domin kashe ta ko cutar da ita.

Source: Facebook
Amnesty International ta bayyana hakan ne a cikin sanarwar da ta wallafa a X Talata, inda ta ce ana cin zarafin matar ta yanar gizo tun bayan da ta fito ta yi zargin abin da ya faru a fadar Sarkin Daura da ke jihar Katsina ranar 14 ga Nuwamba.
Ana yi wa matar barazanar kisa
Czee ta wallafa hotunan wasu sakonnin barazana da ta samu a shafinta na Instagram ranar Litinin. Sakonnin sun kunshi zagi, barazana da kuma bukatar ta goge bidiyon da ta dauka yayin ganawarta da basaraken.
Wasu daga cikin sakonnin sun zarge ta da kokarin bata sunan sarkin, yayin da wasu suka yi mata barazanar cutar da ita tare da gargadinta kada ta sake dawowa Najeriya.
A wani sako, wani mai amfani da shafin mai suna Handel Benny ya zargi matar da cewa ta nuna amincewa da abin da ake zargin sarkin ya yi mata kafin daga bisani ta fito ta koka a kafafen sada zumunta.
Haka kuma, hotunan sakonnin sun nuna yadda wasu ke zargin matar da rashin mutunta addinin Musulunci da al'adun Hausawa, tare da tambayar dalilin da ya sa ta wallafa bidiyon.
An yi mata Dala 50,000
Daya daga cikin sakonnin sirri da Czee ta wallafa ya nuna cewa wani mutum ya yi tayin ba ta Dala 50,000 idan ta goge bidiyon da ya shafi Sarkin Daura.
A cikin sakon, jaridar Punch ta wallafa cewa mutumin ya ce zai ba ta Dala 50,000 idan ta cire bidiyon da ta wallafa.
Amnesty International ta ce irin wadannan hare-hare na nuna dalilin da ya sa mata da dama ba sa kai rahoton cin zarafi a Najeriya, saboda cin hanci da rashawa, kyama da kuma dora laifi kan wadanda aka ci zarafinsu.

Source: Original
Kungiyar ta bukaci rundunar ’yan sandan Najeriya ta ba Czee dukkan tallafin da ya dace tare da gudanar da bincike mai zaman kansa, adalci da inganci kan zargin.
Ta kuma soki abin da ta kira shirun gwamnatin jihar Katsina, tana mai cewa yadda aka tafiyar da lamarin na kara nuna damuwa kan yawaitar cin zarafin mata da kuma kare lafiyarsu.
Maganar Umar Dangiwa
A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan mulkin soja na jihar Kaduna, Kanal Abubakar Dangiwa Umar (mai ritaya), ya bukaci Gwamna Dikko Radda na Katsina ya dakatar da Sarkin Daura kan zargin cin zarafin baturiya.
Dangiwa Umar ya yi wannan kiran ne a cikin wata budaddiyar wasika da ya aika wa gwamnan, inda ya bukaci gwamnati ta dakatar da basaraken har sai an kammala cikakken bincike mai zaman kansa da adalci kan zargin.
Wannan bukata ta zo ne yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan wani bidiyo da ya yadu, wanda ya nuna ganawar sarkin da matar a fadarsa.
Asali: Legit.ng