Sarki Sanusi II Ya Yi Gargaɗi ga Tinubu, Ya Faɗi Bala'in da ke Tunkarar Najeriya
- Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya ce yawan bashin Najeriya da almubazzarancin kudaden gwamnati na barazana ga dorewar tattalin arzikin kasar
- Sanusi ya bayyana cewa biyan bashin Najeriya ya cinye kashi 124 cikin 100 na kudaden shigar gwamnatin tarayya a farkon shekarar 2026
- Tsohon gwamnan CBN ya bukaci gwamnati ta fifita wutar lantarki, noma, hanyoyi da fasaha wajen kashe kudaden kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano – Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, ya yi gargadin cewa yawan bashin da Najeriya ke karba da almubazzarancin kudaden gwamnati na barazana ga dorewar tattalin arzikin kasar.
Sanusi ya bukaci gwamnatin tarayya ta rungumi tsarin kula da kashe kudade, tare da mayar da hankali kan muhimman bangarorin da za su taimaka wajen bunkasa tattalin arziki.

Source: UGC
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da jawabi ta yanar gizo a taron shugabancin Oxford Global Think Tank da aka gudanar a Abuja ranar Talata, cewar Punch.
Illar da basuka ke yi wa Najeriya
Ya ce alkaluman Bankin Duniya sun nuna cewa biyan basussukan Najeriya ya cinye kashi 124 cikin 100 na kudaden shigar gwamnatin tarayya a farkon rabin shekarar 2026.
Sanusi ya bayyana cewa Najeriya ba za ta iya rage matsin bashin da ke kanta ba matukar gwamnati na ci gaba da kashe kudade ba tare da kula da muhimmancinsu ba.
Sanusi ya yaba da wasu nasarorin Tinubu
Da yake magana tare da hamshakin dan kasuwa, Atedo Peterside, Sanusi ya amince cewa wasu alkaluman tattalin arzikin Najeriya sun inganta karkashin gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan
Sarki Sanusi II ya kuma magana, ya ba Tinubu shawarar da za ta taimaki gwamnatinsa
Sai dai ya ce har yanzu sauye-sauyen da gwamnati ta kawo ba su wadatar wajen inganta rayuwar talakawan Najeriya ba.
A cewarsa, matsakaicin bunkasar tattalin arzikin kasar ya karu daga kashi 0.9 a gwamnatin da ta gabata zuwa kashi 4.5.

Source: Twitter
Haka kuma, ya ce hauhawar farashin kayayyaki ta ragu daga sama da kashi 30 zuwa kusan kashi 14.5, yayin da ajiyar kudaden kasar waje ta karu zuwa dala biliyan 55.
Sanusi ya ce:
"Ina ganin komawa daga matsakaicin bunkasar tattalin arziki na kashi 0.9 zuwa kashi 4.5 ci gaba ne. Rage hauhawar farashi daga sama da kashi 30 zuwa kashi 14.5 shi ma ci gaba ne."
Sai dai ya jaddada cewa gwamnati na bukatar sake duba yadda take kashe kudaden kasa, musamman wajen samar da wutar lantarki, bunkasa noma, gina hanyoyi da fasaha.

Kara karanta wannan
Atiku ya soki DSS, ya fadi makircin da aka shirya domin hana shi gangamin kamfe a Sokoto
Sarkin ya ce kashe dala biliyan 10 wajen gina hanyoyi na nufin an cire wannan adadin daga kudaden da za a iya amfani da su wajen bunkasa wutar lantarki da noma.
Ya kuma bukaci gwamnati ta rika sauraron masu sukar manufofinta da nufin gyara, maimakon kallon korafe-korafen talakawa kan tsadar rayuwa a matsayin hare-hare ga shugabanni.
Sanusi II ya ja hankalin Tinubu
An ji cewa Muhammadu Sanusi II, ya ce ya kamata a yaba wa Gwamnatin Bola Tinubu saboda inganta tattalin arzikin Najeriya.
Sarkin Kano ya ce hauhawar farashi ya ragu, tattalin arziki ya bunkasa, yayin da ajiyar kudin kasar waje ta karu.
Sai dai ya bukaci gwamnati ta inganta sadarwa da jama’a tare da sauraron koke-koken jama’a kan kuncin rayuwa.
Asali: Legit.ng
