Sanata Mai Ci Ya Sha Kaye a Sabon Zaben Fitar da Gwani da Jam'iyyar APC Ta Gudanar
- Sanata Tijjani Yahaya Kaura ya samu nasarar zama ɗan takarar sanatan APC a mazabar Zamfara ta Arewa bayan lashe zaben fitar da gwani
- Gijjani Yahaya Ya samu ƙuri’u 16,758, inda ya doke Sanata Sahabi Alhaji Ya’u da Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi
- Zaɓen ya gudana ne a ƙarƙashin tsauraran matakan tsaro, bayan rahotannin harin ’yan bindiga kan jami’an ’yan sanda da aka tura yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Sanata Tijjani Yahaya Kaura ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC na neman tikitin takarar sanata mai wakiltar mazabar Zamfara ta Arewa.
Jami’in tattara sakamakon zaɓen, Sani Abdullahi, ne ya sanar da sakamakon a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara, a ranar Litinin.

Source: Getty Images
A rahoton Leadership, Abdullahi ya ce mutum uku ne suka fafata a zaɓen, waɗanda suka haɗa da Sanata Tijjani Yahaya Kaura, Sanata mai-ci Sahabi Alhaji Ya’u da Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi.
Ya bayyana cewa adadin waɗanda suka yi rajista domin zaɓen ya kai 23,257, yayin da aka tantance masu kaɗa ƙuri’a 19,608. Ya ce an samu ƙuri’u masu inganci 19,492.
Sakamakon zaɓen fitar da gwanin APC
A yayin sanar da sakamakon, jami’in tattara ƙuri’un ya ce Sanata Tijjani Yahaya Kaura ya samu ƙuri’u 16,758, yayin da Sanata Sahabi Alhaji Ya’u ya samu 1,465.
A nasa ɓangaren, Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi ya samu ƙuri’u 1,447, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Abdullahi ya bayyana cewa bayan duba sakamakon da kuma la’akari da ƙa’idojin kundin tsarin mulkin APC da dokokin zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar, Tijjani Yahaya Kaura ne ya samu mafi yawan ƙuri’u.
Tijjani Yahaya Kaura ya samu nasara
Ya ce:
“Ni, Sani Abdullahi, jami’in tattara sakamakon zaɓen fidda gwani na APC na mazabar sanata ta Zamfara ta Arewa da aka gudanar a ranar Litinin, 2 ga Nuwamba, 2026, na bayyana cewa ’yan takarar sun samu ƙuri’u kamar haka.
“Sanata Tijjani Yahaya Kaura ya samu ƙuri’u 16,758, Sanata Sahabi Alhaji Ya’u ya samu ƙuri’u 1,465, yayin da Alhaji Sani Abdullahi Shinkafi ya samu ƙuri’u 1,447.”

Source: Facebook
Ya ƙara da cewa bisa cika ƙa’idojin kundin tsarin mulkin APC da dokokin zaɓe, tare da samun mafi yawan ƙuri’u, an ayyana Sanata Tijjani Yahaya Kaura a matsayin wanda ya lashe zaɓen kuma ɗan takarar jam’iyyar na mazabar Zamfara ta Arewa.
Yadda aka yi rikici a zaben fitar da gwani
Kun ji cewa zaben fitar da gwanin APC na Sanatan Zamfara ta Arewa a Kaura Namoda ya rikide zuwa rikici bayan wasu yan daba sun kai hari rumfunan zabe.
Shugaban karamar hukumar Kaura Namoda, Hon. Mannir Muhammad Haidara, ya tsallake rijiya da baya bayan yan bangar siyasa ne sun kai hari motarsa a makarantar Namoda Model.
Asali: Legit.ng

