Kotun Daukaka Kara Ta Jikawa APC Aiki, Ta Soke Tikitin Takarar Sanata a Zaben 2027
- Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar Sanata Sahabi Ya’u Kaura kan hukuncin kotun tarayya da ya shafi zaɓen fitar da gwani na APC a Zamfara
- Kotun ta tabbatar da hukuncin babbar kotun tarayya da ke Gusau, wadda ta umarci APC da gudanar da sabon zaɓe cikin kwanaki 14
- Lauyan Dr Sani Abdullahi Shinkafi, Bello Galadi, ya ce kotun ta yi watsi da dukkan hujjojin da Kaura ya gabatar saboda rashin cancanta
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Zamfara, Nigeria - Kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar da Sanata Sahabi Ya’u Kaura ya shigar domin ƙalubalantar hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau.
Sanata Sahabi ua daukaka kara ne domin kalubalantar hukuncin soke zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa.

Source: Facebook
Kotun ɗaukaka ƙarar ta tabbatar da hukuncin ƙaramar kotun a shari’ar da Dr Sani Abdullahi Shinkafi, mai neman tikitin takarar sanata a APC, ya shigar, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Kotu ta umarci APC ta sake zabe
Bayan tabbatar da hukuncin, kotun wacce ke zamanta a Sakkwato ta kuma tabbatar da umarnin gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani a wannan mazaba.
Lauyan Shinkafi, Bello Galadi, ne ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai bayan yanke hukuncin.
Ya ce kotun ta warware dukkan batutuwan da Sanata Sahabi Kaura ya gabatar, sannan ta yi watsi da ƙarar saboda rashin cancanta.
Bello Galadi ya ce sanatan ya ƙalubalanci hurumin Babbar Kotun Tarayya na sauraron ƙarar, amma Kotun Ɗaukaka Ƙara ta tabbatar da ikon ƙaramar kotun na sauraron shari’ar da yanke hukunci a kanta.
Lauya ya yi bayani kan hukuncin
Ya ƙara da cewa kotun daukaka kara ta kuma yi watsi da hujjar cewa ƙaramar kotun ta yi kuskure wajen ɗora wa wanda ya shigar da ƙarar nauyin tabbatar da hujjoji.

Kara karanta wannan
Yari: Idan Buhari ya gaza magance matsalar tsaron Najeriya, me ku ke tunani daga Tinubu?
A cewarsa, hujjojin da aka gabatar sun tabbatar da rashin bin ƙa’idoji da dokokin APC da suka tsara yadda ya kamata a gudanar da zaɓen fidda gwani.

Source: Getty Images
Lauyan ya bayyana hukuncin a matsayin nasara ga dimokuraɗiyya da bin doka, yana mai cewa ya sake tabbatar da cewa babu wani mutum da ya fi ƙarfin doka.
“Wannan hukunci ya tabbatar da cewa matakin da wanda nake wakilta ya ɗauka na tafiya neman hakkinsa a kotu ya dace, kuma ya aika da saƙo mai ƙarfi ga waɗanda suke ganin sun fi ƙarfin doka,” in ji Bello Galadi.
Kotu ta karbe tikitin dan Majalisar wakilai
A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke zama Gombe ta soke zaben fitar da gwanin APC na takarar Majalisar wakilai a mazabar Balanga/Billiri.
A hukuncin da ta yanke, Mai Shari’a Vera E. Ibrahim ta umarci APC ta gudanar da sabon zabe a wannan mazaba tare da hana Ali J.C. sake tsayawa takara.
Kotun ta ce rashin saka sunan Ali J.C. cikin kundin rajistar mambobin APC da aka miƙa wa INEC ya sa takararsa ta saba da doka.
Asali: Legit.ng
