Ciyaman Ya Sha da Kyar da Miyagun Yan Daba Suka Farmaki Wurin Zaben Fitar da Gwanin APC

Ciyaman Ya Sha da Kyar da Miyagun Yan Daba Suka Farmaki Wurin Zaben Fitar da Gwanin APC

  • Zaben fitar da gwanin APC na Sanatan Zanfara ta Arewa a Kaura Namoda ya rikide zuwa rikici bayan wasu yan daba sun kai hari rumfunan zabe
  • Shugaban karamar hukumar Kaura Namoda, Mannir Muhammad Haidara, ya tsallake rijiya da baya bayan maharan sun far wa motarsa
  • Rikicin ya tilasta wa masu kada kuri’a tserewa domin tsira, yayin da jami’an INEC ba su isa wasu rumfunan zabe ba har zuwa lokacin hada rahoton

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Zamfara, Nigeria - Wasu yan daba da ake zargin yan bangar siyasa ne sun tarwatsa mutane a rumfunan zaben fitar da gwanin jam'iyyar APC da aka shirya domin fitar da dan takarar Sanatan Zamfara ta Arewa.

Rahotanni sun nuna cewa zaben fitar da gwani a Kaura Namoda, jihar Zamfara, ya rikide zuwa rikici a yau Litinin, inda aka ce yan daba sun kai hari kusa da Fadar Sarkin yankin.

Kara karanta wannan

An kama mutum 3 kan zargin ƙona motar yan tawagar yakin neman zaben jam'iyyar APC

Tutar APC.
Tutar jam'iyya mai mulkin Najeriya watau APC Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Twitter

DailyTrust ta ruwaito cewa maharan sun kai hari makarantar firamare ta Namoda Model da kuma rumfar zaben unguwar Galadima Dangaladima da ke gaban fadar Sarkin.

Wannan lamarin da ya kawo cikas ga gudanar da zaben tare da tilasta wa masu kada kuri’a da sauran mazauna yankin tserewa domin tsira.

Wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne sun kuma yi fada a tsakaninsu, wanda ya yi sanadin jikkatar mutum daya sosai.

An yi gargadi kafin harin yan daba

Kafin isowar maharan, daya daga cikin masu kada kuri’a, mai suna Malam Sanusi Kaura, ya sanar da dan jarida cewa akwai yiwuwar ’yan bangar su zo su kawo cikas ga zaben.

Ya ce:

“Na zo ne domin sanar da kai, a matsayinka na dan jarida kuma muryar marasa galihu, cewa mun samu labarin ’yan banga na kan hanyarsu ta zuwa domin kawo cikas ga zaben.”

Harin ya kawo cikas ga harkokin rumfunan zaben yayin da masu kada kuri’a ke jiran isowar jami’an Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), wadanda ba su isa wuraren ba har zuwa karfe 11.30 na safe.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda na ganin ƙiyayya, an ƙona motoci a tawagar kamfen dinsa

Rikici tsakanin magoya bayan ’yan takara

’Yan takara biyu da ke neman kujerar sanatan sun hada da Sanata mai ci, Sahabi Ya’u Kaura, wanda ke bangaren Ministan Tsaron Kasa, Bello Matawalle, da Sanata Tijjani Yahaya Kaura, wanda ke bangaren Sanata Abdul’aziz Yari.

Dukkan ’yan takarar sun fito ne daga unguwa daya, wato Galadima Dangaladima, da ke cikin garin Kaura Namoda.

A wani bangare kuma, Shugaban karamar hukumar Kaura Namoda, Hon. Mannir Muhammad Haidara, ya tsallake rijiya da baya bayan yan bangar siyasa ne sun kai hari motarsa a makarantar Namoda Model, tare da lalata wasu sassanta.

Zamfara.
Taswirar jihar Zamfara da ke Arewa maso Yammacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Daga bisani, maharan sun nufi rumfar zaben Galadima Dangaladima da ke kusa da fadar Sarkin, inda suka kawo cikas ga harkokin zabe da kuma rera taken siyasa da magoya bayan ’yan takara ke yi.

Magoya bayan Sanata Sahabi Ya’u Kaura na rera taken neman ya koma majalisar dattawa domin yin wa’adi na biyar a lokacin da rikicin ya barke.

Kara karanta wannan

Jerin labaran karya da suke yawo a yanar gizo da za a iya dauka gaskiya ne

Kotu ta soke zaben fitar da gwanin APC

Kun ji cewa kotun ɗaukaka ƙara ta yi watsi da ƙarar da Sanata Sahabi Ya’u Kaura ya shigar domin ƙalubalantar hukuncin Babbar Kotun Tarayya da ke Gusau.

Sanata Sahabi ya daukaka kara ne domin kalubalantar hukuncin soke zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC na kujerar Sanatan Zamfara ta Arewa.

kotun wacce ke zamanta a Sakkwato ta kuma tabbatar da umarnin karamar kotun na sake gudanar da sabon zaɓen fitar da gwani a wannan mazaba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262