‘Dan Takaran Gwamna, Abubakar Malami Ya Kai Karar Abin da Aka Yi Masa a Kebbi

‘Dan Takaran Gwamna, Abubakar Malami Ya Kai Karar Abin da Aka Yi Masa a Kebbi

  • Abubakar Malami SAN ya shigar da ƙara ga ’yan sandan Kebbi kan rushe wani ginin ADC a Birnn Kebbi
  • Tsohon ministan ya umarci lauyoyinsa su nemi hakkinsa ta hanyar shari’a tare da neman diyyar barnar da aka yi
  • Gwamnatin Kebbi ta musanta hannu a rushe ginin, tana mai cewa ’yan adawa ne ke yaɗa zargin domin tada rikici

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kebbi - Abubakar Malami SAN ya shigar da ƙara a gaban kwamishinan ’yan sandan jihar Kebbi kan rushe gininsa a Birnin Kebbi.

Tsohon Babban lauyan na Gwamnatin Tarayya kuma Ministan Shari’a a lokacin Muhammadu Buhari ya kai batun gaban hukuma.

Abubakar Malami
Abubakar Malami da tsohon mai gidansa, marigayi Muhammadu Buhari Hoto: Abubakar Malami SAN
Source: Facebook

Ana zargin an rusa ofishinsu Abubakar Malami

Wani rahoto daga Daily Trust ya ce Abubakar Malami wanda shi ne ɗan takarar gwamnan jihar Kebbi a ƙarƙashin ADC ya kai korafi.

Kara karanta wannan

Kebbi: Gwamnati ta yi maganar ‘rusa’ ginin tsohon ministan Buhari, Abubakar Malami

Ginin wanda yake wani yanki da aka ware domin kasuwanci a titin Sani Abacha, yana ɗauke da ofishin Malami Pressure Group.

Malami Pressure Group wata ƙungiya ce da take mara masa baya a siyasa a jihar Kebbi.

Abubakar Malami ya fitar da jawabi

Tsohon ministan ya yi magana ne ta cikin wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai, Bincike da Nazarin Manufofin ADC ya fitar a jiya.

Abubakar Bello Abdullahi, ya ce Abubakar Malami ya yi matuƙar mamakin abin da ya faru kuma ya bayyana shi a matsayin rashin bin doka.

Ya yi zargin cewa wasu abokan hamayyarsa na siyasa ne suka rusa ginin domin su harzuƙa jagoran na ADC da magoya bayansa a Kebbi.

Yake cewa ana so ne su ɗauki matakan da ka iya kawo barazana ga zaman lafiyar jihar.

Wani mataki tsohon ministan ya dauka?

Sanarwar ta ce Malami ya umarci lauyoyinsa su nemi hakkinsa ta hanyar shari’a, tabbatar da mallakar kadarar da neman diyya wajen hukuma.

Kara karanta wannan

Tinubu ya zabi manyan hadiminsa da gwamnoni 5, ya shirya masu liyafa a Makkah

An kuma buƙaci ‘ya ‘ya da magoya bayan ADC su kwantar da hankalinsu tare da bin doka, ana cewa jam’iyyar adawar za ta bi hanyoyin shari’a.

Gwamnatin Kebbi ba ta san an yi ba

Sai dai gwamnatin Kebbi ta musanta hannu a rushe wani gini, inda ta bayyana zargin a matsayin ƙarya kamar yadda The Nation ta fada.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan jihar kan harkokin yaɗa labarai, Malam Yahaya Sarki, ya fitar, ya musanta faruwar lamarin.

Sarki ya ce wasu ’yan adawa ne ke yaɗa zargin domin haifar da rashin fahimta tsakanin Gwamna Nasir Idris da Malami mai takara a ADC.

Ya buƙaci mazauna jihar, musamman ’yan siyasa, da su yi watsi da rahotannin da ke danganta gwamnatin jihar da abin da ake cewa ya faru.

Abubakar Malami
Abubakar Malami mai takaran gwamna a Kebbi Hoto: Abubakar Malami SAN
Source: Facebook

Malami ya tsaida abokin gami a ADC

Tsohon Ministan Shari'a Abubakar Malami ya zaɓi Musa Zagi a matsayin abokin takararsa (mataimakin gwamna) a jam'iyyar ADC a Kebbi.

An ji labari cewa sanarwar da aka fitar na zuwa ne yayin da jam'iyyar ke da kwarin gwiwar zai sauke nauyin da aka ɗaura masa idan sun yi nasara.

Naɗin abokin takarar ya zo ne a daidai lokacin da wata kotun tarayya ta ba da umarnin ƙwace wasu kadarori 48 da ake dangantawa da babban lauyan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng