Kebbi: Gwamnati Ta Yi Maganar ‘Rusa’ Ginin Tsohon Ministan Buhari, Abubakar Malami

Kebbi: Gwamnati Ta Yi Maganar ‘Rusa’ Ginin Tsohon Ministan Buhari, Abubakar Malami

  • Gwamnatin Kebbi ta musanta zargin cewa ta umarci rusa ginin ɗan takarar ADC a zaben gwamna na 2027
  • Ta ce wasu ’yan adawa ne suka ƙirƙiri zargin domin haddasa rikici tsakanin gwamna da Abubakar Malami
  • Bincike ya nuna an yi ta takaddama tsakanin Malami da wani ɗan kasuwa, Umaru Gulumbe kan kadarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Kebbi - Gwamnatin Jihar Kebbi ta musanta zargin cewa ta umarci wasu da ake tunanin ’yan daban siyasa ne da yin rusau.

An rusa wani gini da ake cewa ɗan takarar gwamnan jihar Kebbi a ƙarƙashin jam’iyyar ADC, Abubakar Malami ya mallaka.

Malami
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris da Abubakar Malami SAN Hoto: Engr Mustapha Umar Faruk/Hassada mai rabo taki
Source: Facebook

Jawabin hadimin gwamnan jihar Kebbi

A wani jawabi da aka fitar a karshen mako, Leadership ta rahoto cewa Gwamnatin jihar ta bayyana zargin a matsayin ƙarya.

Gwamnatin Kebbi ta ce wasu ’yan adawa ne ke yaɗa labarin domin haddasa rashin jituwa tsakanin Nasir Idris da Abubakar Malami.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya zargi Abba da hannu a yunkurin hana Aminu Abdussalam takarar gwamna

A wata sanarwa da mai taimaka wa gwamnan kan harkokin yaɗa labarai ya fitar, an yi watsi da zargin taba wa Malami dukiya.

Sanarwar ta yi kira ga al’umma, musamman ’yan siyasa, da su yi watsi da duk labarin da ke danganta ta da rushe wannan gini.

Ta ce manufar yaɗa zargin ita ce haddasa rashin fahimta tsakanin Idris da Malami wanda yake neman gwamna a inuwar ADC.

Mai taimaka wa gwamnan ya ce gwamnatin Nasir Idris ba ta da hannu ko kaɗan a lamarin.

Ginin da aka ce an rusa a Kebbi

A baya wasu bayanai sun yaɗu a Facebook da sauran kafofin sada zumunta cewa wasu ’yan daba sun yi wa ‘dan adawan barna.

An zargi ’yan jam'iyyar APC da rusa ofishin kamfen Malami bisa umarnin gwamnatin jihar.

Sai dai kakakin gwamnan ya musanta zargin a cikin sanarwar da ya fitar ga manema labarai a Birnin Kebbi ranar Lahadin nan.

Rikicin da ake yi da Malami a kan fili

Malami wanda ya yi shekaru takwas a matsayin ministan shari’a a zamanin Muhammadu Buhari zai kara da APC a Kebbi a 2027.

Kara karanta wannan

Atiku ya gano kuskuren Tinubu a mulki, ya ɗauki alƙawarin gyara bangaren

Binciken jaridar ya nuna cewa ginin da aka ce an rusa ba ofishin yakin zaben wata jam’iyyar siyasa ba ne, illa wani fili ne kurum.

Filin yana daura da Otal ɗin Azbir, a kan titin Sani Abacha Bypass da ke Birnin Kebbi.

Ana zargin cewa Umaru Gulumbe, wani ɗan siyasa kuma ɗan kasuwa a jihar, ne ya mallaki filin bayan shekaru ana shari’a.

An ce shi ma tsohon babban lauyan gwamnatin kasar ya yi iƙirarin mallakar kadarar kafin ya rasa shi a kotu.

Sai dai ƙoƙarin jin ta bakin ɓangarorin biyu domin samun ƙarin bayani bai yi nasara ba.

An ce Gulumbe ya tafi Abuja, yayin da aka ce Malami yana cikin shirye-shiryen ƙaddamar da yaƙin neman zaɓensa a jihar.

Malami
Tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami a gidan shi Hoto: Ethnic African Stories
Source: Facebook

Bola Tinubu ya tafi Umrah

Ana da labari jirgin Bola Tinubu ya wuce Makkah a ranar ranar Alhamis 29 ga watan Oktoba 2026 da nufin yin ibadah.

Shugaban Najeriyan zai Umrah kuma ya yi wa kasarsa addu’a a Saudi Arabiya yayin da yake fuskantar babban zabe.

Hadimin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya ce ana sa ran Tinubu zai dawo Najeriya cikin makon nan da aka shiga yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng