Kebbi: Malami Ya Kafa Kwamitin Kamfen Mai Mutum 600 domin Kifar da APC
- Tsohon Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Tarayya, Abubakar Malami, SAN, ya kaddamar da kwamitin yaƙin neman zaɓen ADC a Jihar Kebbi
- Malami ya buƙaci mambobin kwamitin su tabbatar da haɗin kai, zaman lafiya da kuma ladabi, tare da gudanar da kamfen bisa manufofi ba tare da ƙabilanci ba
- Ya bayyana haka ne yayin bikin kaddamar da kwamitin, inda ya ce aikin mambobin shi ne kai saƙon ADC zuwa kowace ƙaramar hukuma da al’umma a jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Birnin Kebbi – Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, SAN, ya kaddamar da Darakta-Janar da sama da mambobi 600 na kwamitin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar ADC a Jihar Kebbi.
Malami ya buƙaci mambobin kwamitin su gina haɗaɗɗiyar jam’iyyar siyasa mai ƙarfi wadda za ta isa ga al’ummomi daban-daban a faɗin jihar.

Source: Facebook
A cewar sanarwar da hadimin Malami, Mohammed Bello Doka ya wallafa a Facebook, tsohon ministan ya bayyana kafa kwamitin a matsayin mataki na samar da tsari mai ƙarfi na tunkarar zaɓuka.
Malami ya nemi ADC ta hada kai
Malami ya jaddada cewa kwamitin bai kamata ya zama tarin ƙungiyoyin da ke fafatawa da juna domin cimma muradun ‘yan takara daban-daban ba.
Ya ce ya kamata a dauki nasarar kowane ɗan takarar ADC a matsayin nasarar jam’iyyar baki ɗaya.
Ya ce:
“Wannan kwamitin yaƙin neman zaɓe na ADC ne baki ɗaya. Ba batun ɗan takara ɗaya ko kujera ɗaya ba ne. Daga kujerar gwamna zuwa Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai da Majalisar Dokokin Jiha, dole ne mu yi aiki a matsayin tsintsiya madaurinki ɗaya.”
Malami ya kuma buƙaci mambobin su guji ƙabilanci, bangaranci da rikicin cikin gida, yana mai cewa irin waɗannan abubuwa na iya raunana duk wata jam’iyyar da ke son samun nasara.
Kira ga sulhu da haɗin kai
Tsohon ministan ya ce babu wata ƙabila, mazaba, ƙaramar hukuma, gunduma ko al’umma da ya kamata ta ji an ware ta daga kamfen ɗin ADC.
Ya kuma buƙaci shugabannin jam’iyyar su mayar da sulhu da sasanta rikice-rikice cikin gida cikin muhimman ayyukan kamfen.
Malami ya bayyana manufar jam’iyyar da kalmar “ADC ɗaya, kamfen ɗaya”, yana mai cewa mambobin ba za su iya nuna haɗin kai a bainar jama’a sannan su riƙa yi wa junansu zagon ƙasa a ɓoye ba.

Source: Facebook
Ya ce:
“’Yan takara daban-daban, ADC ɗaya. Al’ummomi daban-daban, Jihar Kebbi ɗaya.”
Batun kamfen cikin lumana
Malami ya umarci kwamitin da ya gudanar da ayyukansa cikin mutunci, ladabi da girmama abokan hamayyar siyasa, al’umma da masu kaɗa ƙuri’a.
Ya ce kamfen ɗin ADC a Kebbi dole ne ya kasance cikin lumana, bisa doka, kuma ba tare da cin mutuncin ƙabila, kalaman ƙiyayya ko kai wa mutane hari saboda asalinsu ko zaɓin siyasarsu ba.
Punch ta ce ya tunatar da mambobin cewa zaɓe na wucin gadi ne, yayin da alaƙar da ke tsakanin al’ummomi za ta ci gaba bayan an kammala zaɓe.
Gwamnan Kebbi ya sauya mataimaki
A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, ya zaɓi Alhaji Ibrahim Augie a matsayin abokin takararsa a zaɓen gwamna na 2027.
Matakin ya maye gurbin mataimakin gwamnan jihar na yanzu, Sanata Umar Tafida, wanda ya kasance abokin takarar Idris a baya.
Rahotanni sun ce an bayyana matakin ne a Birnin Kebbi, inda Sakataren Shirya Ayyukan Jam’iyyar APC na Ƙasa, Alhaji Suleiman Argungu, ya magantu.
Asali: Legit.ng


