Za a Buga Siyasa a Kebbi, Abubakar Malami Ya Sayi Fom din Takara na ADC

Za a Buga Siyasa a Kebbi, Abubakar Malami Ya Sayi Fom din Takara na ADC

  • Tsohon Ministan shari'a, Abubakar Malami, ya shiga cikin sahun masu neman takarar gwamnan jihar Kebbi a zaben 2027
  • Abubakar Malami ya sayi fom din neman tsayawa takarar gwamnan jihar Kebbi a karkashin inuwar jam'iyyar ADC mai adawa
  • Tsohon Ministan ya koka kan halin da jihar take ciki, inda ya zayyano matsalolin da ke ci mata tuwo a kwarya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kebbi - Tsohon babban lauyan gwamnatin tarayya kuma tsohon Ministan shari’a, Abubakar Malami, ya shiga takarar gwamnan jihar Kebbi.

Abubakar Malami karɓi fom ɗin tsayawa takarar gwamna na ADC gabanin zaɓen gwamnan jihar Kebbi na shekarar 2027.

Malami ya shiga takarar gwamnan Kebbi
Abubakar Malami tare da fom din neman takarar gwamna na ADC Hoto: Abubakar Malami, SAN
Source: Facebook

Abubakar Malami ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, 9 ga watan Mayun 2026 a shafinsa na Facebook.

Meyasa Malami ya shiga takarar gwamna?

Kara karanta wannan

"Mu kece raini": Gwamnan Gombe ya yi martani bayan kafiyar Pantami da Goje

Malami ya ce ya yanke shawarar shiga takarar ne saboda ba zai iya ci gaba da yin shiru ba kan abin da ya siffanta da taɓarɓarewar tsaro, talauci, rashin ingancin kiwon lafiya, lalacewar ilimi, da kuma matsin tattalin arziki a jihar Kebbi.

Ya yi zargin cewa a halin yanzu jihar Kebbi tana fuskantar ɗaya daga cikin mafi munanan matsalolin jin ƙai da na shugabanci a Najeriya, inda ya buga misali da alkaluma masu tada hankali na yaran da ba sa zuwa makaranta, talauci, mace-macen mata masu juna biyu, rashin abinci mai gina jiki, da kuma rashin tsaro.

A cewarsa, fiye da kashi 67 cikin 100 na yara masu shekaru tsakanin shida zuwa 15 ba sa zuwa makaranta, yayin da aka bayar da rahoton cewa fiye da kashi 88 cikin 100 na yara a jihar suna rayuwa cikin talauci.

Malami ya nuna damuwa kan matsalolin Kebbi

Tsohon ministan ya kuma nuna damuwa kan yanayin fannin kiwon lafiya, inda ya bayyana cewa mace-macen mata masu juna biyu ya ci gaba da kasancewa babba, yayin da al’ummomin karkara da dama ba su da damar samun ingantacciyar kulawar awon ciki da sauran muhimman ayyukan kiwon lafiya.

Kara karanta wannan

ADC: Tsohon minista, Amaechi ya zama na 2 da ya sayi fam na takarar shugaban kasa a 2027

Game da rashin tsaro, Malami ya ce al’ummomi da dama a faɗin jihar suna ci gaba da shan wahala sakamakon hare-haren ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane, lamarin da ya tilasta wa manoma da dama barin gonakansu, yayin da sana’o’i ke fuskantar matsin lamba sakamakon tsoro da rashin tabbas.

Malami ya sayi fom din takara
Abubakar Malami tare da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar Hoto: @atiku
Source: Twitter

Ya nuna yatsa ga gwamnati

Ya zargi gwamnati mai ci yanzu da rashin sanin abubuwan da suka kamata a ba wa muhimmanci a daidai lokacin da ’yan ƙasa ke fama da matsin tattalin arziki da rashin tsaro.

Daga nan ya yi kira ga al’ummar jihar Kebbi da su goyi bayan manufarsa ta sake gina jihar ta yadda za ta zama mafi aminci da wadata.

Kotu ta tanadi hukunci kan bukatar Malami

A wani labarin kuma, kun ji cewa wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta jingine hukunci kan wata bukata da Abubakar Malami ya gabatar mata.

Abubakar Malami ya shigar da kara domin neman izinin ɗaukaka ƙara kan hukuncin da babbar kotun tarayya ta yanke game da ƙwace wasu kadarori da ake alaƙanta shi da su.

Kwamitin alkalai uku na kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai shari’a Abba Mohammed, bai bayyana ranar yanke hukuncin ba, sai dai ya ce za a sanar da ɓangarorin da zarar hukuncin ya kammala.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng