Tambuwal Ya Fusata da aka Kai wa Dan Takarar ADC Hari da Bindiga a Sokoto

Tambuwal Ya Fusata da aka Kai wa Dan Takarar ADC Hari da Bindiga a Sokoto

  • Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya yi Allah-wadai da harin da aka ruwaito an kai wa dan takarar gwamnan ADC, Manir Muhammad Dan’iya, da tawagarsa
  • Tambuwal ya bukaci rundunar ’yan sanda, DSS da sauran hukumomin tsaro su gudanar da bincike mai zaman kansa tare da hukunta duk wanda aka samu da hannu
  • Ya kuma yi kira ga magoya bayan ADC su kwantar da hankalinsu, yana mai cewa babu barazana da za ta hana jam’iyyar gudanar da gangami da kamfen a jihar Sokoto

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Sokoto - Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Sanata Aminu Waziri Tambuwal, ya yi Allah-wadai da harin da aka ruwaito an kai wa dan takarar gwamnan jam’iyyar a jihar, Hon. Manir Muhammad Dan’iya.

Kara karanta wannan

Yadda aka ceto malaman da aka sace za su tafi yi wa Tinubu addu'a a Zamfara

Rahotanni sun bayyana cewa an kai wa dan takarar hari ne tare da wasu mambobin tawagarsa a hanyar zuwa filin jirgin sama.

Aminu Tambuwal
Sanata Aminu Tambuwal yana addu'a. Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Source: Facebook

Tambuwal ya bayyana hakan ne a ranar Asabar cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce lamarin ya faru ne a kusa da filin jirgin saman Sokoto a ranar Juma’a, 30 ga Oktoba, 2026.

Tambuwal ya bukaci a yi bincike

Tsohon gwamnan ya ce zargin cewa jami’an rundunar Sokoto Marshal da Community Guard ta jihar sun tare ayarin motocin Dan’iya, suka bude wuta tare da lalata motarsa, abin damuwa ne matuka.

Ya kuma yi zargin cewa jami’an sun tsare jami’an hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) guda biyu da ke cikin tawagar tsaron dan takarar.

Tambuwal ya bukaci rundunar ’yan sandan Najeriya, DSS da sauran hukumomin tsaro da su gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa da adalci domin gano gaskiyar abin da ya faru.

Kara karanta wannan

An bude wa tawagar dan takarar gwamnan ADC wuta da bindiga a Sokoto

Ya ce duk wanda aka samu da hannu a lamarin ya kamata ya fuskanci hukunci bisa tanadin doka.

Korafin da Tambuwal ya yi

Tambuwal ya jaddada cewa kowane dan Najeriya na da ’yancin yin zirga-zirga, shiga jam’iyyar siyasa da neman mukamin siyasa bisa doka.

Ya ce babu wani dan kasa da ya kamata ya fuskanci barazana, tashin hankali ko cin zarafi saboda amfani da wadannan hakkoki.

Manir Dan'iya da aka kai wa hari
Dan takarar gwamna na ADC a Sokoto da aka kai wa hari. Hoto: Sokoto ADC
Source: Facebook

Ya kuma yi kira ga duk wanda ke da sabani ko korafi kan siyasa da ya bi hanyoyin lumana da doka wajen bayyana matsayinsa, yana mai cewa kamata ya yi jama’a su bayyana ra’ayinsu ta hanyar kada kuri’a, ba amfani da makamai ba.

A cewarsa, aikin hukumomin tsaro shi ne kare dukkan ’yan kasa ba tare da la’akari da jam’iyyar da suke goyon baya ba, don haka bai kamata a yi amfani da su wajen tsoratar da ’yan siyasa ba.

ADC za ta yi kamfen a Sokoto

Tsohon gwamnan ya kuma bukaci gwamnatin jihar Sokoto ta tabbatar da cewa dukkan hukumomin tsaron da ke karkashinta suna gudanar da ayyukansu bisa doka ba tare da nuna bangaranci ba.

Kara karanta wannan

Lauyan Pantami ya yi magana kan maido da sunan shi cikin 'yan takara

Ya bayyana cewa duk da abin da ya faru, babu wata barazana da za ta hana jam’iyyar ADC gudanar da gangamin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa da ta tsara yi a ranar 4 ga Nuwamba, 2026.

Tambuwal ya bukaci mambobi da magoya bayan jam’iyyar su kwantar da hankalinsu, su yi hakuri tare da ci gaba da jajircewa wajen gudanar da harkokinsu cikin lumana.

INEC ta yi magana kan tsaro

A baya, mun rahoto cewa shugaban hukumar INEC, Farfesa Joash Amupitan, ya bayyana cewa hukumar ta sauya tsarin tura jami’an tsaro a ranar zabe.

Amupitan ya bayyana hakan ne a Gombe yayin bude taron tuntuba da ma’aikatan shiyyar Arewa maso Gabas da kuma tantance shirye-shiryen zaben 2027.

A cikin sanarwar hukumar, an bayyana cewa INEC ta sake fasalin hadin gwiwarta da rundunar ’yan sanda, hukumar NSCDC, DSS, rundunar sojoji da sauran hukumomin tsaro.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng