Oshiomhole Ya Kwance wa Atiku da Peter Obi Zani a Kasuwa kan Zaben 2027
- Sanata Adams Oshiomhole ya yi zargin cewa Peter Obi bai magance matsalolin jihar Anambra ba a tsawon shekaru takwas da ya yi yana gwamna
- Oshiomhole ya yi hasashen cewa Atiku Abubakar zai koma Dubai bayan ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
- Tsohon gwamnan Edo ya yaba wa gwamnatin Tinubu, musamman kan amincewa da matsayin Cross River a matsayin jihar da ke samar da man fetur
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Cross River - Sanata Adams Oshiomhole ya soki tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi, da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, inda ya nuna shakku kan ƙwarewarsu wajen jagorantar Najeriya gabanin zaɓen 2027.
Oshiomhole ya ce Obi bai magance matsalolin jihar Anambra ba a tsawon shekaru takwas da ya yi yana gwamna. Haka kuma, ya yi hasashen cewa Atiku zai koma Dubai bayan ya sha kaye a zaɓen shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan
An fara batun Tinubu ya je Umrah ne don neman kuri'un 'yan Arewa, hadiminsa ya magantu

Source: Facebook
Tsohon gwamnan jihar Edo ya bayyana hakan ne yayin wani gangamin yaƙin neman zaɓen jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Cross River, cewar rahoton jaridar Vanguard.
A wajen taron, ya buƙaci al’ummar jihar da su mara wa Shugaba Bola Tinubu baya domin samun damar komawa kan karagar mulki a wa’adi na biyu.
Oshiomhole ya tambayi ƙwarewar Peter Obi
Da yake magana kan alƙawarin Obi na mulkin Najeriya na tsawon shekaru huɗu kacal, Oshiomhole ya ce tsohon gwamnan bai nuna ƙwarewar da za ta tabbatar zai iya cimma nasarori a wannan ɗan lokaci ba.
Obi, wanda ke takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDCa), ya sha alwashin gudanar da mulki na wa’adi ɗaya idan aka zaɓe shi.
Oshiomhole ya tambayi yadda Obi zai iya gyara Najeriya cikin shekaru huɗu alhali bai iya magance matsalolin Anambra ba a tsawon shekaru takwas da ya yi yana gwamna.
"Idan Peter Obi bai iya gyara jihar Anambra cikin shekaru takwas ba, ta yaya zai iya kallonku ido-da-ido ya ce zai yi hakan cikin shekaru huɗu?” In ji shi.
Tsohon gwamnan Edo ya yi magana kan Atiku
Oshiomhole ya kuma yi wa Atiku Abubakar ba’a, inda ya zarge shi da zama a wajen Najeriya na tsawon lokaci, tare da dawowa ƙasar ne kawai lokacin da ake gab da gudanar da zaɓe.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasar, wanda ke takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar African Democratic Congress (ADC), ya sha fafatawa a zaɓukan shugaban ƙasa a baya.
"Atiku, wanda ke zaune a Dubai, yana dawowa gida ne kawai idan zaɓe ya kusa. Idan ya sha kaye a wannan zaɓen, kamar yadda zai sha kaye, a watan Janairu ko Fabrairu, zai koma Dubai.”
Oshiomhole ya yaba wa gwamnatin Tinubu
Sai dai a yayin gangamin, Oshiomhole ya kuma mayar da hankali kan abubuwan da ya bayyana a matsayin nasarorin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu, musamman a jihar Cross River.
Ya ce amincewa da matsayin Cross River a matsayin jihar da ke samar da man fetur, bayan warware matsalar kasancewarta jiha marar iyakar teku, zai ƙara yawan kuɗaɗen shigar da jihar ke samu.
A cewarsa, wannan mataki zai inganta tattalin arzikin jihar tare da buɗe mata ƙarin damar samun kuɗaɗen shiga.
Oshiomhole ya yi amfani da damar wajen kira ga mazauna Cross River da su goyi bayan Tinubu, yana mai nuna cewa ci gaba da mulkin APC zai ba da damar ƙarfafa nasarorin da ya ce gwamnatin ke samu.

Source: Facebook
Kwankwaso ya gargadi Atiku
A wani labarin kuma, kun ji cewa Rabiu Musa Kwankwaso, ya gargaɗi Atiku Abubakar, kan ƙoƙarin kawo cikas ga tsarin karɓa-karɓar shugabancin Najeriya tsakanin Arewa da Kudu.
Kwankwaso ya jaddada cewa har yanzu lokacin yankin Kudu ne ya samar da shugaban ƙasa na gaba, don haka bai kamata wani ɗan takara daga Arewa ya nemi kujerar a zaɓen 2027 ba.
Asali: Legit.ng

