Kwankwaso da ke Tare da Peter Obi, Ya Koma ba Atiku Shawara kan Zaben 2027

Kwankwaso da ke Tare da Peter Obi, Ya Koma ba Atiku Shawara kan Zaben 2027

  • Dan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Kwankwaso, ya ce bai kamata Atiku Abubakar ya karya tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu ba
  • Kwankwaso ya buƙaci Atiku ya mara wa Peter Obi baya domin Kudu ta kammala wa’adin mulkin da ya rage mata kafin shugabancin ya koma Arewa
  • Tsohon gwamnan Kano ya ce ya taɓa yin watsi da burinsa na zama shugaban ƙasa domin ba wa Obi damar tsayawa takara, saboda sun yi imani da manufofi iri ɗaya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, ya gargaɗi Atiku Abubakar, kan ƙoƙarin kawo cikas ga tsarin karɓa-karɓar shugabancin Najeriya tsakanin Arewa da Kudu.

Kwankwaso ya jaddada cewa har yanzu lokacin yankin Kudu ne ya samar da shugaban ƙasa na gaba, don haka bai kamata wani ɗan takara daga Arewa ya nemi kujerar a zaɓen 2027 ba.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Jigon APC ya yi wa Atiku tatas, ya bukaci ya yi ritaya daga siyasa

Kwankwaso ya ba Atiku shawara
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso tare da Atiku Abubakar Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Twitter

Ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da manema labarai a gidansa da ke Kano ranar Lahadi, 1 ga watan Oktoban 2026, cewar rahoton tashar Arise tv.

Kwankwaso ya kuma gargaɗi jam’iyyar African Democratic Congress (ADC) kan abin da ya kira ƙoƙarin haifar da ruɗani game da tsarin rabon mulki.

Me yasa Kwankwaso ke adawa da takarar Arewa?

Tsohon gwamnan na Kano ya ce duk da cewa kundin tsarin mulkin Najeriya bai tanadi tsarin karɓa-karɓar mulki tsakanin Arewa da Kudu ba, hankali da adalci sun nuna cewa idan wani yanki ya yi mulki na wa’adi biyu, ya kamata a bai wa ɗayan yankin damar karɓa.

A cewarsa, tsayar da ɗan takara daga Arewa a wannan lokaci ba zai taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin kan ’yan Najeriya ba.

Maimakon haka, ya yi zargin cewa hakan na iya haifar da ruɗani da rashin jituwa tsakanin al’ummar ƙasar.

Kwankwaso ya ce bai kamata Atiku ya kawo cikas ga tsarin ta hanyar sake neman shugabancin ƙasar a wannan lokaci ba.

Kara karanta wannan

Obi ya fadi yadda zai yi aiki tare da Kwankwaso idan suka yi nasara a 2027

Ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasar da ya mara wa Peter Obi baya domin ya jagoranci Najeriya, har sai an kammala wa’adin mulkin da yake ganin ya rage wa yankin Kudu.

Kwankwaso ya ce ya sadaukar da burinsa

Jagoran tafiyar Kwankwasiyya ya tuna cewa ya taɓa tsayawa takarar shugaban ƙasa sau uku a jere, amma daga bisani ya yanke shawarar ajiye burinsa domin bai wa Peter Obi damar wakiltar yankin Kudu.

Ya ce ya ɗauki matakin ne saboda yana ganin Obi mutum ne mai nagarta kuma ɗan yankin Kudu, tare da kasancewarsu masu manufa iri ɗaya.

"Abin da ke faruwa a ADC ba zai taimaka mana ba. Wasu mutane suna son haifar da ruɗani ta hanyar kawo ɗan takara daga Arewa, alhali sun san cewa har yanzu lokacin Kudu ne. Bayan shugabancin Obi, sai mulki ya koma Arewa.” In ji shi.

Kwankwaso ya ƙara da cewa​:

“Na sadaukar da burina domin Peter Obi saboda mutum ne mai nagarta kuma ɗan Kudu. Muna da manufofi da akida iri ɗaya. Muna da ƙarfi kuma za mu iya tafiyar da harkokin wannan ƙasa cikin sauƙi.”

Kara karanta wannan

Atiku v Amaechi: Wike ya lissafo matsaloli da ke tattare da tikitin ADC

Ya ce bai kamata a karya tsarin rabon mulki ba

Kwankwaso ya jaddada cewa domin samun daidaito a tsarin siyasar Najeriya, ya kamata a bai wa Peter Obi, wanda ya fito daga yankin Kudu, damar jagorantar ƙasar.

Ya ce tsarin rabon mulki tsakanin Arewa da Kudu yana da muhimmanci wajen tabbatar da fahimtar juna da zaman tare tsakanin yankunan ƙasar.

A cewarsa, bayan kammala wa’adin mulkin da ya kamata Kudu ta yi, shugabancin ƙasar zai koma Arewa kamar yadda tsarin karɓa-karɓar mulki ya tanada.

Kwankwaso ya ja kunnen Atiku
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso na jawabi a wajen taro Hoto: Hon. Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Kwankwaso ya gargadi INEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa dan takarar mataimakin shugaban kasa na jam'iyyar NDC, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya tura sakon gargadi ga hukumar INEC.

Sanata Kwankwaso ya ce samun kura-kurai a rajistar masu zaɓe ta farko na iya kawo cikas ga sahihancin babban zaɓen 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng