Oshiomhole Ya Fallasa Abin da Atiku Ya Gaya Masa kan Tallafin Man Fetur

Oshiomhole Ya Fallasa Abin da Atiku Ya Gaya Masa kan Tallafin Man Fetur

  • Adams Oshiomhole ya ce Atiku Abubakar ya taɓa bayyana masa dalilan da ya sa yake ganin ya kamata a cire tallafin man fetur
  • Oshiomhole ya kuma tuna da matsayar Atiku ta 2023 kan mayar da NNPCL hannun masu zaman kansu, yana tambayar yadda hakan zai yiwu
  • Atiku dai ya ce zai dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a 2027, yana mai cewa hakan zai rage tsadar rayuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon shugaban kungiyar kwadago ta Najeriya (NLC), ya soki shirin Atiku Abubakar na dawo da tallafin man fetur idan aka zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa a 2027.

Oshiomhole ya ce Atiku ya taɓa bayyana masa dalilin da ya sa yake ganin ya kamata a cire tallafin man fetur lokacin da yake riƙe da mukamin mataimakin shugaban ƙasa.

Kara karanta wannan

Pantami na murnar samun tikitin PDP, abokin hamayyarsa ya sha alwashin jawo masa matsala

Oshiomhole ya yi magana kan Atiku
Alhaji Atiku Abubakar da Sanata Adams Oshiomhole Hoto: RAUF AREGBESOLA, Adams Oshiomhole Outreach
Source: Facebook

Tsohon Gwamnan Jihar Edo ya bayyana hakan ne a wata hira da tashar TVC ranar Talata, 29 ga watan Satumban 2026 yayin da yake martani kan alƙawarin Atiku na mayar da tallafin man fetur.

Atiku Abubakar ya taɓa goyon bayan cire tallafin

Oshiomhole ya ce a lokacin da yake shugaban NLC, Atiku ya yi masa bayani kan abin da yake gani a matsayin almubazzarancin kuɗin tallafin man fetur da kuma dalilin da ya sa ya kamata a cire shi.

“Atiku Abubakar da kansa idan ya samu lokacin tunani cikin nutsuwa, zai yi wa kansa dariya. Kar ka manta, ni ne shugaban NLC, kuma a lokacin da yake mataimakin shugaban ƙasa, Atiku ya yi mini bayani kan ɓarnar da tallafin man fetur ke haifarwa da kuma dalilin da ya sa ya zama dole a cire shi, sai dai ban yarda da su ba,” in ji Oshiomhole.

Kara karanta wannan

Akwai kura: Shugaban APC ya hango matsalar da Arewa za ta shiga idan Tinubu bai zarce ba

Ya tambayi matsayar Atiku kan NNPCL

Sanatan ya kuma yi tambaya kan daidaituwar matsayar Atiku a kan batun, yana tunawa da wata shawara da tsohon mataimakin shugaban ƙasar ya gabatar a 2023 ta mayar da Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL) hannun masu zaman kansu.

“Ka tuna, Atiku yana da tarihin cewa a shekarar 2023 ya ce zai mayar da NNPCL hannun masu zaman kansu. Ba ka da wannan faifan? Har ya ƙara da cewa ko da za a kashe shi, zai yi hakan. Ban san dalilin da ya sa zai mutu saboda yana son mayar da NNPCL hannun masu zaman kansu ba,” in ji shi.

Oshiomhole ya yi tambaya kan farashi

Oshiomhole ya ƙara tambayar yadda gwamnati za ta mayar da kamfanin mai na ƙasa hannun masu zaman kansu, amma a lokaci guda ta ci gaba da kayyade farashin da sabbin masu kamfanin za su sayar da man da suke samarwa.

“Shin za ka iya mayar da wani abu hannun masu zaman kansu, sannan har yanzu ka riƙa gaya wa sabon mai shi farashin da zai sayar da abin da yake samarwa?” ya tambaya.

Kara karanta wannan

Yadda farashin litar fetur za ta kasance idan Atiku ya dawo da tallafi

Atiku ya yi alkawarin dawo da tallafi

Atiku Abubakar, wanda shi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na ADC, ya ce zai dawo da tallafin man fetur a matsayin wani ɓangare na manufofinsa na tattalin arziki idan aka zaɓe shi a 2027.

Atiku ya ce manufar za ta taimaka wajen rage tsadar rayuwa tare da sanya farashin man fetur ya zama mai sauƙin biya ga ’yan Najeriya.

Sai dai Oshiomhole ya ci gaba da cewa matsayar da Atiku ya taɓa nunawa a baya kan cire tallafin man fetur na haifar da tambayoyi game da sabon alƙawarin da ya yi na dawo da shi.

Atiku ya ce zai dawo da tallafi
Atiku Abubakar na jawabi a wajen taro Hoto: @atiku
Source: Twitter

Akpabio ya yi shagube ga Oshiomhole

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi barkwanci kan bidiyon Sanata Adams Oshiomhole.

Akpabio ya yi barkwancin ne kan wani bidiyo da ya nuna Sanata Oshiomhole yana yi wa wata budurwa tausa a cikin jirgin sama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng