Kwankwaso Ya Bude Sabon Shafi a TikTok, Ya Bayyana Irin Bidiyoyin da Zai Fara Wallafawa
- Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bude shafi a dandalin TikTok
- Tsohon gwamnana Kano ya yi alƙawarin rika wallafa sahihan bayanai, sabbin labarai da abubuwan da suka shafi harkokinsa na yau da kullum
- Matakin na zuwa ne yayin da NDC ke ƙara shirin tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027 tare da Peter Obi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Rabiu Musa Kwankwaso, ya bude shafi a dandalin sada zumunta na TikTok.
Tsohon gwamnan na Kano ya yi wa mabiyansa alƙawarin rika wallafa sahihan bayanai, sababbin labarai da abubuwan musamman da suka shafi harkokinsa na yau da kullum.

Source: Facebook
Kwankwaso ya bude shafi a TikTok
Kwankwaso ya sanar da shiga TikTok ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba, inda ya buƙaci ’yan Najeriya su bi shi a sabon shafinsa domin ganin bidiyon da zai riƙa wallafawa.
A cikin saƙon, tsohon gwamnan Kano ya ce:
“Na shiga na bude TikTok! Ina ƙarfafa ku duka da ku bi ni a can domin samun sahihan bayanai, sababbin labarai da abubuwa na musamman da suka shafi rayuwata ta yau da kullum kai tsaye.
“Najeriya za ta yi kyau. — RMK.”
A cikin wani bidiyo da ya haɗa da saƙon, Kwankwaso ya yi maraba da masu amfani da TikTok zuwa shafinsa, sannan ya ƙarfafa su da su bi shi tare da yaɗa bidiyonsa.
“Barka masu amfani da TikTok, barkan ku da zuwa shafinmu na TikTok. Ku kunna sanarwar sababbin abubuwa, ku biyo mu, ku yaɗa bidiyonmu. Na gode, Allah ya albarkace ku,” in ji shi.
Kwankwaso na shirin zaɓen 2027
Shigar Kwankwaso TikTok na zuwa ne a daidai lokacin da NDC ke ƙara shirye-shiryen tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na 2027, inda ake sa ran zai tsaya takara tare da Obi a ƙarƙashin tutar jam’iyyar.
Manyan ’yan siyasar biyu sun koma NDC a hukumance a watan Mayu, bayan sun fice daga ADC. Matakin ya biyo bayan shawarwari kan makomarsu ta siyasa da tsarin karba-karba.

Source: Facebook
Daga bisani, an tabbatar da Obi a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na NDC a babban taron jam’iyyar na ƙasa da aka gudanar a ranar 30 ga Mayu, yayin da aka zaɓi Kwankwaso a matsayin mataimakinsa.
Tikitin takarar ya haɗa magoya bayan Obi da kuma tafiyar siyasar Kwankwasiyya ta Kwankwaso, wadda ke da gagarumin tasiri a Kano da wasu sassan Arewacin Najeriya.
Kwankwaso ya yi magana kan kisan Masussuka
Kun ji cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi alhinin rasuwar Sheikh Yahaya Masussuka wanda aka hallaka a Katsina.
Kwankwaso ya yi Allah-wadai da kashe-kashen malaman addini da sauran fararen hula da ’yan bindiga ke yi, yana mai cewa lamarin ya zama babban abin damuwa da ke buƙatar ɗaukar matakan gaggawa.
Asali: Legit.ng

