Cakwakiyar da ke Zaben Gwamnan Adamawa duk da Tasirin Fintiri, Atiku da Ribadu

Cakwakiyar da ke Zaben Gwamnan Adamawa duk da Tasirin Fintiri, Atiku da Ribadu

  • Zaben gwamnan Adamawa na 2027 na neman zama mai zafi, yayin da za a gwabza tsakanin manyan jam'iyyu a jihar
  • APC na samun karfin goyon bayan gwamnatin tarayya da ta jihar sannan fitowar Abdulrahman Haske na iya kawo mata cikas
  • Masu takara shida, ciki har da Binani, Ishaku Abbo da Hamman Modibbo, na daga cikin wadanda za a fafata da su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Yola, Adamawa - Yayin da Gwamna Ahmadu Fintiri e karshen wa’adinsa na biyu, zaben gwamnan Adamawa sai sake zafi yake yi.

Karfin Atiku Abubakar, da mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu, sun haifar da yanayin siyasa mai sarkakiya a Adamawa.

Zaben gwamnan Adamawa zai yi zafi a 2027
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da Nuhu Ribadu. Hoto: Governor Ahmadu Umaru Fintiri da Nuhu Ribadu.
Source: Twitter

Cakwakiyar da ke zaben jihar Adamawa

Zaben gwamnan jihar Adamawa na shekarar 2027 na neman zama daya daga cikin zabukan da za su fi daukar hankali a tarihin jihar, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

'Ba a cire sunan Pantami a takara ba': PDP ta kwantar wa masoyanta hankali

Karewar mulkin Gwamna Ahmadu Fintiri da sabanin muradun Atiku Abubakar da Nuhu Ribadu, tare da wasu abubuwan cikin gida, sun sauya yanayin siyasar jihar.

A babban zaben 2023, Fintiri da Atiku sun hada karfi karkashin jam’iyyar PDP, inda suka doke jam’iyyar APC.

Sai dai tun daga lokacin, siyasar jihar ta sauya matuka. Ba wai kawai tsoffin kawayen biyu sun rabu ba, har ma an samu wasu manyan sauye-sauyen kawance a fadin jihar.

Yanayin siyasar yanzu ya sa ‘yan takara shida ke ganin suna da damar lashe zaben gwamnan jihar.

Karfin siyasa da sauyin kawance

Gwamna Fintiri ya sauya sheka zuwa APC a watan Fabrairu. Hada karfinsa da na Ribadu ya karfafa jam’iyyar mai mulki a matakin tarayya a jihar da ta rasa a shekarar 2019.

A wancan zaben, Fintiri ya doke gwamna mai ci a lokacin, Jibrilla Bindow, da bambancin kuri’u sama da 40,000.

A daya bangaren, karfin Atiku a siyasar cikin gida da ta kasa na nuna cewa har yanzu yana da tasiri sosai a jiharsa ta asali. Baya ga haka, burinsa na neman shugabancin kasa na iya zama wani muhimmin dalilin karfafa yakin neman zaben dan takarar jam’iyyar African Democratic Congress (ADC).

Kara karanta wannan

2027: Atiku ya zafafa da ya kwatanta Tinubu da dakikin dalibi

Duk da haka, zabukan baya sun nuna cewa masu zabe a Adamawa ba sa bin umarnin manyan ‘yan siyasa a kowane lokaci. Saboda haka, goyon bayan Fintiri, Atiku ko Ribadu ga dan takara ba ya tabbatar da nasararsa a zaben 2027.

Siyasar Adamawa da aka samu sauye-sauye

Jihar Adamawa na da dogon tarihin sauye-sauyen siyasa, wanda ya samo asali musamman daga kasancewar al’ummomi da kabilu daban-daban a jihar. An ga wannan yanayi tun kafin kafa tsarin jihohin da ake da su yanzu.

A lokacin mika mulki zuwa Jamhuriya ta Biyu, a tsohuwar jihar Gongola da ta kunshi Adamawa da Taraba na yanzu, jam’iyyun siyasa biyar da aka yi wa rajista sun yi zazzafar fafatawa a zaben gwamna na shekarar 1979.

Jam’iyyar ADC

Dan takarar ADC, Hamman Modibbo, kwararre ne a harkokin gudanar da kudaden gwamnati, kuma shi ne darakta kuma babban shugaban farko na Hukumar Leƙen Asirin Kudi ta Najeriya (NFIU).

Yana da digiri na biyu a fannin kasuwanci tsakanin kasa da kasa daga Jami’ar Salford da ke Manchester, da kuma digirin farko na tarihi daga Jami’ar Maiduguri.

A matsayinsa na shugaban farko na NFIU bayan ta zama hukuma mai cin gashin kanta, Modibbo ya jagoranci tawagar da ta sauya karamar sashen zuwa hukuma mai muhimmiyar rawar karba, nazari da raba bayanan sirrin kudi ga hukumomin da abin ya shafa a Najeriya da kasashen waje.

Kara karanta wannan

Kano: Abba ya yi wa Barau da Bichi sulhu kan rikicin da suke da juna

Modibbo ya gina yakin neman zabensa kan gaskiya da rikon amana, kula da kudade, gyaran hukumomi da tsaron al’umma da kan iyakoki.

Sai dai takararsa na fuskantar rikicin cikin gida a ADC. Umar Suleiman, tsohon manajan darakta na Hukumar Tashoshin Jiragen Ruwa ta Najeriya kuma tsohon jami’in diflomasiyya, ya lashe zaben fitar da gwani na ADC a watan Mayu, inda ya doke Modibbo.

Suleiman ya dage cewa har yanzu shi ne sahihin dan takarar jam’iyyar, kuma ya samu umarnin kotu da ke hana jam’iyyar sauya shi da wani.

Duk da wadannan matsalolin shari’a, shugabannin ADC na kasa tare da Atiku sun goyi bayan Modibbo a watan Agusta, lamarin da ya haddasa rikici mai tsanani tsakanin bangarorin jam’iyyar kan tikitin.

Saboda haka, yayin da Suleiman ke kalubalantar sauya shi a kotu, shugabancin ADC na kasa na ci gaba da goyon bayan Modibbo.

Baya ga haka, Muhammad Shuwa shi ne dan takarar da bangaren ADC karkashin Nafiu Bala ke marawa baya, lamarin da ya sa mutane uku ke ikirarin rike tikitin jam’iyyar a jihar.

Kara karanta wannan

Buba Galadima ya yi wa APC tonon asiri, ya ce ta kawo sabuwar dabara a 2027

Jam'iyyun NDC, LP da PDP

Dan takarar Nigeria Democratic Congress (NDC), Aishatu Ahmed, wadda aka fi sani da Binani, fitacciyar ‘yar siyasa ce a Adamawa.

Tsohuwar sanatar ta shahara wajen gina goyon baya a matakin kasa da kasa da kuma shirye-shiryen tallafa wa kananan ‘yan kasuwa da sauran jama’a.

Tana mai da hankali kan walwalar al’umma, samun kiwon lafiya da kuma bai wa mata da kananan ‘yan kasuwa damar shiga harkokin tattalin arziki.

Binani injiniya ce a fannin gine-gine, kuma ta taba zama ‘yar majalisar wakilai mai wakiltar Yola ta Arewa, Yola ta Kudu da Girei.

Wani dan takara, Ishaku Abbo, ya wakilci mazabar sanatan Adamawa ta Arewa daga 2019 zuwa 2023, sannan ya koma kujerar a 2023 kafin kotu ta soke nasarar tasa.

Abbo fitaccen dan siyasa ne mai bayyana ra’ayoyinsa, kuma yana da goyon bayan matasa sosai a yankin arewacin Adamawa.

Yana takara karkashin jam’iyyar Labour Party (LP), inda yake amfani da salon siyasar da ke jan hankalin jama’a kai tsaye.

Kara karanta wannan

'Illar da rikicin Zamfara zai yi ga Tinubu, Yari, Matawalle da Dauda Lawal'

Dabarunsa sun hada da tuntubar matasa masu kada kuri’a, inganta adalci a zamantakewa, bunkasa hanyoyin karkara da karfafa hada kan jama’a a yankin sanatan arewacin jihar.

Maurice Vunobolki, dan takarar PDP da ke samun goyon bayan Nyesom Wike, akawu ne mai lasisi, masani kan kula da harkokin kudi kuma mai ba da shawara kan ayyukan ci gaban kasa da kasa.

A baya, ya yi aiki a ayyukan ci gaba da kasashen waje ke tallafawa, tsarin sayen kayayyakin gwamnati da ayyukan more rayuwa na kananan hukumomi a Arewacin Najeriya.

Sai dai Vunobolki na fuskantar hamayya daga Caleb Myebangara, dan takarar bangaren PDP karkashin jagorancin Tanimu Turaki.

Myebangara kwararren ma’aikacin banki ne, kuma ya fara yakin neman zabensa yayin da ake jiran hukuncin Kotun Daukaka Kara da ke Abuja kan shari’ar bangaren PDP na Tanimu Turaki.

Babachir ya yi tone-tone bayan shiga NDC

An ji cewa Babachir David Lawal ya yi zargin cewa wasu ‘yan takarar gwamna a NDC na aiki ne domin karya Peter Obi da Rabiu Kwankwaso.

Ya bukaci magoya bayan NDC su yi watsi da abin da ya kira dabarun ‘yan jam’iyyar masu neman kawo cikas a Arewa maso gabas.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.